Sashe 2
Baccin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
M SHAKUR EPISODE 1 DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI! BEFORE ANYTHING JOIN ANY OF MY COMMENTS SECTION! https://chat.whatsapp.com/Lexo516Rbc1J318UVT7a6q https://chat.whatsapp.com/Iqo6H7ScyCu85pKADXlnsA https://chat.whatsapp.com/K3p0bPIZP4M2RbqsDlpVzV https://chat.whatsapp.com/FD5l1XPlv0zJjShiIL1Vyx Cike gidan yake makil da jama a, kana ganin yanayin tsarin ginin gidan kasan irin gidan masu dan rufin asiri ne daidai gwargwado, babban compound ne mai dan madaidacin girma dakeda wata yar kodaddiyan milk gate dayake a bude sabida jama a dake shiga da fita. Yammata ansha makeup ansha anko, sun zagaye wata yar budurwa dakana ganinta kasan itace Amaryan sabida yanayin tufafin jikinta da gwargwaro dakuma lalle datasha a hannaye da kafafu, rawa suke sosai a tsakar gidan gaban DJ dayake buga kida yana chanza wakoki anama Amarya liki yan 50, da yan 100naira Duk wannan kidan da hayaniyan da ake bugawa bacci take acikin dakin dakeda dan duhu dan an sauke labulen window, kaman an tsikareta firgigita tabude idanunta tana kallon saman silin na dakin dawani irin sauri ta tashi zaune gashinta nawani irin zubowa bayanta mai tsawo baki kirin dayake a tsefe, sanye take da atampa wanda kana gani kasan sabuwa ce anko kuma dan tayi kama da na mutanen tsakar gidan yan biki, an manta dinkin doguwan riga dayamata wani irin bala in kyau a jiki, very simple style mara nauyi kwata kwata, waige waige tashigayi kaman mai neman abu sai kawai tamike tsaye zumbur tana yarfe hannu karamin lips nata ya furta Ammi wanda muryanta baya fitowa, saita shiga tafiya ahankali ahankali still kalle kalle take tana shafa fuskanta da kanta tana sosa gashin data shiga hargitsawa yafara komawa wani iri kawai tabude kofan dakin, jama a ne birjik afalon ana hayaniya, tana bude kofan kowa yadago kai yakalleta jikake falon tsit sai kuskus da aka fara, kanta tasauke kasa ahankali, saita cigaba da tafiya ahankali batare data hada ido da ko mutum daya na falon ba bakinta na furta. Ammi, Ammi, Ammi ba lallai ma kaji metake cewaba idan bakazo kusa da ita ba, sai gyaramata ake kowa na cire roban abincinsa daga kasa, kawai tawuce tayi kofa tafita jama an dakin na kuskus. Yarinya kyau iya kyau amman kan ba dadi sam, sam Wai ahaka aka haifeta koko jinnu ne cus kyawawan yara haka daman ance yaran jinnu ne a wannan fa haka aka haifota da tabin hankalin ba jinnu bane, yoh yarinyar da asibitin mahaukata ma ake kaita Jama a ne cike a compound din ga rawa anayi tana fitowa kawai tafiya tashigayi har lokacin kuma kanta akasa tana magana ita kadai Ammi, Ammi tana tafiya tafiya irin wacce ba direction dinnan nan da nan jama a suka fara kallonta. Amaryan dake filin rawane ta hangota taja tsaki takalli daya daga cikin yammatan wajen tace je dan Allah ki kirawa mahaukaciyan chan mamanta kafin ta hargitsamin biki, dan wlh tabatamin biki sainaci ubanta kafin akaini gidan mijina dasauri kawarta tace toh bari naje fita daga cikin filin rawan tayi tai bayan gida ta nufa inda mata ke girki dagudu tayi wajen mata mata tadan manyanta akalla zatai 46yrs haka tana sanye da same atampa da kowa yasaka tace Ammi ga Amirah chan tsakar gida zata fara haukan anatse Ammi tajuyo takalleta kafin tai magana matan dake kusa da Ammi tace wai ku yaran yanzu maisa baku da tarbiya ne iyye haka ake magana Zainabu ? Turobaki tayi tace to karya akayi? Danma nazo nafada mata ai danayi shiru abina kwashe nemanta anjima Ammi bata tsaya jinsu ba wucewa tayi da dan sauri tazagayo cikin compound din tanabin ko ina da kallo tana nemanta da idanu gabanta nadan faduwa ta tare wata yar yarinya tace kinga mini Amirah Baby? Baby tace tana waje tana nemanki Ammi dasauri Ammi tasaketa tai hanyar gate tana zuwa taganta awaje tafiya take still ba takalmi akafan dasauri Ammi tasa hannu takama hannunta tace gani nan Amirah Ammi tai maganan tana kai dayan hannunta kan kafadarta tajuyo da ita tanadan maida ijiyan zuciya sabida kalan saurin datayi, ahankali for the first time sai yarinyar tadago kanta Ya Rabbi! Tsarki ya tabbata ga Allah ubangijin daya hallicci kowani bil adama, dan yarinyar nada kyau, wani irin kyau da kafin kaga mace mai kyanta sai an tona, sak Amminta tundaga white skin color din, saidai tafi Maman kyau nesa ba kusa ba, ga gashin idanu dogaye bakake sosai, ga gashin gira baki acike mai yawa kaman buzuwa, tanada dogon pointed nose, ga karamin baki pink yir exactly irin na jarirai, gefen fuskanta da goshinta duk akwai gashi kwance kaman buzuwa, chak ta tsaya tana kallon Ammi kuma babu wani reaction akan idanunta kona damuwa, kona baccin rai, kona farin ciki, Kona tsoro, kona bakin ciki, kawai fuskanta is straight, dan ijiyan zuciya Ammi ta sauke tadan sassauta murya tace jibeki ba kallabi akanki, ba takalmi akafanki, banasha gayamiki duk sanda kika farka baki ganni ba ki zauna awajen zaki ganni zan dawoba amman bakijin maganata, wuce mutafi Ammi takara rikewa gam tashiga tafiya, Ammi na tafiyar da ita ahankali suka shigo cikin gidan daidai wata mata datasha ado sosai tanada dan jiki kana ganinta kasan itane Maman Amarya ta tareta tana wani hura hanci tace idan kinsan ba girkin zakiyi ba maisa kikace zakiyi tunda hankalinki nakan wannan abun tanuna Amirah da kanta ke kasa tana dab da Ammi dake rikeda hannunta, adan natse Ammi tace yanzu zan koma nacigaba Maman Baby Mamababy tana wani huci tace shidai yafi miki, kibar mahaukaciyan nan kiji da abincin jama ko kadan Ammi bataso yau ranta yabaci saisa kawai takara kama hannun Amirah da kyau suka wuce bayan gidan, few matan dake wajen suka bisu da kallo ganin Ammi tadawo da yarinyar, wani plastic chair Ammi tadauka ta ijiye tadaurata akai tace zauna bari nabaki abinci Ammi tajuya dawani irin sauri kaman gudu Amirah ta tashi, Matan dake wajen suka bita da kallo Ammi tajuyo ta kalleta ganin taki zama takara biyota sai kawai ta kyaleta bata cemata komiba tabude katon kulan wajen tadauki plate tazuba mata white rice da stew tasaka spoon tajuya mata sannan tace muje Ammi tai gaba Amirah tabiyo ta abaya, Ammi takamata tasata a kujera ahankali saita debi rice a spoon tadankai bakinta jin ba zafi sosai saita debo takawo wajen bakinta dasauri tabude bakinta hakoranta farare passs, Ammi ta samata shinkafan, karba tayi duk tana kallon idanun Ammi tana taunawa ahankali, sai Ammi takama hannunta tasaka mata plate din tace yauwa to maza cinye, bance ki tashi ba gani nan girki zanyi kinji ? Shiru tayi tana kallon Ammi tana chewing rice din, Ammi tace kice to da dan karamin voice nata da Ammi kadai kejinsa aduniya tace toh Ammi wani heart melting smile Ammi tayi ta tsaya tana kallonta sai kuma ahankali takai hannunta tashafa kumatunta tace yauwa yar albarka na, maza cigaba da ci ingani sauke kai tayi daga kallon Ammi ta debo abincin a spoon takai bakinta tafara ci Ammi tace yauwa Masha Allah, kada ki tashi gani nan anan Ammi tajuya tayi wajen murhu tana tafiya tana waigowa dantaga kota mike taganta azaune amman tanabin Ammi da idanu tanacin abinci ko kyafta idanu batayi, dan ijiyan zuciya Ammi tasauke ta tsaya kusada Rakiya tace kuyakuri Rakiya Rakiya tace haba bakomi, dawainiya da yara haka ai ba karamin aiki bane, kuna nema mata maganin islamic kuwa? Spoon na girki Ammi tadauka tana juyawa tace babu wanda ba mayi, ba matsalan jinnu bane da itaba rashin lafiyane kawai daga Allah dayan matan tace gaskiya yakamata kiyi dagaske, ga sa onninta duk sai aure, to wannan ma ai kanwartata tayi aure abarta tunda har anzo an tambayi aurenta, jibidai yau Ramla ce Amarya, gaskiya dai kuyi da gaske inba hakaba babu wanda zai auri mara lafiya Ammi bata kara magana awajen ba sai aikin gabanta take bini bini tana dagokai ta kalli Amirah da har lokacin idanunta nakan Mamanta duk inda Ammi tayi tana binta da idanu, gama hada komi Ammi tayi tarufe pot tazo tadauki pure water tazo wurin, Ammi ta bude mata ta karbi plate din ta ijiye sannan tasaka ruwan abakinta hannuwanta tasa ahankali tadaura akan na Ammi kullum idan Ammi nabata ruwa haka takeyi tashiga sha tana kallon Ammi, Ammi tamata murmushi tace saura kimini wasa da ruwa anan agwagwa kawai dago kanta tayi alamun ta koshi, murya chan kasa tace Ammi pee Allah yasa tagama hada komi na girkin kawai tsotsewa zaiyi akwashe takalli su Rakiya tace tunda an gama bari nakaita ciki nasa mata kallabi dasauri Rakiya tace karki damu tunda kingama zamu kwashe kiji da abu daya Ammi batace komiba ta karbi plate din ta ijiye takama hannunta tace muje toh kankame hannun Ammi tayi suka wuce Ammi tace duk sanda kika kara fitowa babu kallabi akanki saina saba miki mena gayamiki game da budekai ba kallabi ? Batace komiba ahaka suka shiga falon Ammi ga jama a awajen Ammi ta gaggaisa dasu Amirah na tsaye wajen dab da Mamanta tanama wasa da yatsun Ammi ne ita kadai haka Ammi tawuce da ita bedroom duk aka bisu da kallo, ta maida kofan tarufe sannan tace cikani kije kiyi fitsari dan dago kanta tayi batare data saki Ammi ba sai kawai Ammi tawuce da ita bandakin tabude kofa tace shiga ahankali tasaki hannun Ammi, Ammi tace yi adduan shiga bandaki ahankali bakinta ya shiga motsi saita shiga Ammi tajuya zata wuce dasauri Amirah tace Ammi dan dakatawa Ammi tayi kaman zata mata fada but she knows harda mutanen dasukayi extra yawa yau agidan da hayaniyan biki yasa she s being extra clingy today, other days tana dan bata space even though duk inda zaka gan Ammi zakaga Amirah you must find her awajen, sai kawai Ammi ta tsaya tace jekiyi to gani nan, maza kiyi alwala gyadama Ammi kai tayi tawuce tana daga riganta Ammi na kallonta batako kyafta idanu kana ganin yanda take komi kasan mahaifiyarta tai kokari dan bata wani shirme, tashi tayi bayan tayi tsarki tamaida pant dinta sannan tai flushing zata taho Ammi tace alwala baki salla ba alwala tashigayi shima exactly yanda ake alwala sannan tafito Ammi da kanta ta rufe kofan bayin tadauki hijabi tabata tasaka maroon yamata bala in kyau ta kabbarta salla tayi shima perfectly tana idarwa tajuyo takalli Ammi, Ammi dake daukan ribbon da comb tace ba