← Book details Baccin So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 87

Sashe 19

Baccin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sai yabata tausayi ahankali tace nagode Ya Umar Allah kara buda maka dasauri yace inhar zaki godemin da gaske godiyan danakeso is kidena kuka sabida dagamin hankali yake share fuskanta tayi tass yace to yima mijinki murmushi kadan murmushi tayi tadanja hijabinta tana boye fuskanta yayi murmushi yace Alhamdulillah baison abinda sai taba Miemie ko kadan, suna zaune awajen Dr yafito dasauri Umar yatashi yace stay here zama tayi yawuce wajen Dr dasauri, Dr yace jikinta yahau sosai that s abinda yayi contributing dayasa takasa farfadowa amman she s out of danger mun mata allurai mun dinka mata kan, tana bukatan full circle na sleep so bazata tashi ba sai zuwa gobe da safe zuwa rana haka amman Alhamdulillah no need to worry again Dasauri Umar yace Alhamdulillah Alhamdulillah thank you Dr thank you Dr yace zaku iya shiga ku ganta yanzu za a maidata ward tahowa wajen Miemie yayi data tsaya tana kallonsa murmushin dataga yanayi yadan kwantar mata da hankali yace Ammi is fine yanzu amman Dr wai yamata alluran bacci sai zuwa gobe zata farfado muje ki ganta zasu maidata ward daga emaergwncy room din Gyadamai kai tayi tabisa sukaje har ward ne inda kusan patient goma suke kowa akan gadonsa suka gaida mutane sannan sukaje gadon Ammi dake bacci ga drip nabin jikinta da gudu Miemie tawani rungumeta ta kankameta Umar yabita da idanu, da yanada kudi dabazai jira 4 months da aka deba musu ba kawai aurenta zaiyi yahuta da wutan sonta dake damunsa sai yanzu hankalinsa ya kwanta ganin tadena kuka dazu world dinsa was crumbling because of yanda take kuka. Ahankali yazo wajen 10k ya dunkule ya ijiye kusa da ita yace ga wannan incase wani abu come up, bari nakoma gareji anjima zan dawo da yan abubuwan da kuke bukata dago kanta tayi takallesa saita gydamai kai akunyace tace thank you Ya Umar Allah kara budi da arziki ahankali yace promise bazaki kara kuka ba sauke kanta kasa tayi tana wasa da yatsunta ahankali tace murmushi yayi yace take care and take care of Ammi bye yawuce yafita yan ware din na kallonsu machine dinsa yahau yabuga sai gareji. Miemie na asibitin har magrib ta ari dadduman wacce ke next to bed nasu tai salla har akai isha i ma haka 8 daidai Umar yayi sallama yashigo Miemie tadan dagokai ta kallesa yana gaida marasa lafiyan yan dakin yana sanye da shadda blue mai kyau yasa hula sai kanshi yake hannunsa duka biyun rike da abubuwa sannan yazo wajen gadon ya ijiye basket din yace Umma tace akawo miki Allah kara sauki gobe zasuzo dubiya ya ijiye dayan ledan wanda yan shopping ne yamata, Miemie da kanta ke kasa tace an gode Allah amfana zama yayi akujeran daya bata yakalleta yace bude kula ki debi abinci kici Dan kallonsa kadan tayi ganin ba wasa fuskansa saita sauka saga bakin gadon tabude kulan dafadukan shinkafa aka dafa musu da nama da zobo mai sanyi tadauki spoon da plate ta deba tadan kalli matan dake bata Aron dadduma ta kusa da su tace ga abinci muna kwarya matan tace ahh Alhamdulillah an gode dawowa tayi tazauna tafara ci duk kanta akasa Umar sai kallonta yake, haka take ta gansa taita kunya ko yazo zance awaya ne take bude baki tamai magana, today is the first day datake ganinsa in reality tayi magana shima sabida rudewan Ammi ne, cinyewa tayi tasha ruwa sannan ta ijiye plate din, Umar yamike yace bari naje to gud night akwai sock da zanin gado kisa ki rufa da kyau sabida sauro gyadamai kai tayi tace nagode agaida Umma dan kallonta yayi yace muje kirakani akunyace ta sauke kanta kasa wucewa yayi yay gaba sannan tasauka tasa takalmi tafito awaje ta samesa wajen wani bishiya inda akasa kujeran zama haka tawuce wajen tana tafiya ahankali ya tsareta da kallo taje saita zauna amman tabar dan gab between them, sukayi shiru sai chan yace Maryam dago kanta tayi takallesa, ahankali yace how are you? Tambayan ya sosa zuciyanta sosai baki tabude zatai magana kawai saita daura hannayenta akan fuskanta kaman yar yarinya tafashe da kuka, she just feel alone, she feels ayanzu right in this moment batada kowa sai Umar, ba Ammi ba Amirah, mikewa Umar yayi saiyazo ya tsaya agabanta kafin yaduka gabanta ahankali yace Miemie is this the promise dakika min? Yakikeso nayi da raina? Do you want to kill me eh Miemie, bakiso na ko? Girgixamai kai takeyi tana shesheka irin yanda yara sukeyi hancinta harda majina tace Ya Amirah batada lafiya, bataci abinci ba nasan har yanzu dare yayi bazataci ba tunda bataganmu ba, jikinta was hot, bansan wani hali yar uwata ke ciki ba, Ammi gata itama a hospital banda kowaaa tana kuka numfashinta har neman daukewa yake Umar baimasan mezaiyiba sai kawai ahankali yajawota for the first time tunda suka san juna yayi hugging nata. EPISODE 1 Batasan metakeba kawai kankamesa sosai Miemie tayi back, Umar yafara patting bayanta yana mata magana a kunne, Maryam do you also want to loose me too? Cus kukan ki zai iya halakani kinga saiki zama ke kadai aduniya uhn kankamesa Miemie tayi tana girgiza masa kai, ahankali yace komi yayi zafi maganinsa Allah, rayuwan nan babu wanda baya cikin wata jarabawa, I just want you kisan cewa Allah baya bacci, ki karfafa imaninki, kome ke damunki ki fuskancesa kiyi addu a, kima Amirah addu a wherever she s Allah ya tsareta ya kareta yakuma bata lpy, yadawo da ita lpy, sannan Allah yabama Ammi lafiya, everything is going to be okay I promise you, kinji, I m right here fa, I will always support you and be there for you no matter what kinji ?Gyadamai kai tayi tanajin wani natsuwa da karfi a zuciyanta, ahankali Umar yace I love you so much be strong for me okay gyadamai kai tayi, cirota yayi daga jikinsa saita kasa kallonsa kuma ta sauke kanta kasa shima yatashi yakoma gefenta ya zauna saukai shiru sai chan ya kalleta yace bari natafi uhm, saida safe tashi ki koma ciki tashi Miemie tayi da sauri kanta akasa tace saida safe uhm nagode Ya Umar tawuce dasauri yabita da kallo yadanyi murmushi dan hug dasukai sharing nadawomai greasy azuciya yashafa kansa yamike ahankali yawuce yahau machine dinsa yabar asibitin. Wuraren 10 na safiya Ammi tashiga bude idanunta ahankali, dasauri Miemie dake gwfenta tawani zabura tace Ammi kin tashi, gani nan Ammi kina ganina ? Bude idanunta Ammi tayi ahankali tana bin ko ina da kallo kafin tasauke idanunta akan Miemie dake kanta, Miemie tace Ammi murya chan kasa mara karfi Ammi tace ina ne nan Miemie? Meya kawoni nan ? Ahankali Miemie tace kanki ne yadan fashe tun jiya kike nan shiru Ammi tayi nan da nan abinda yafaru jiya yadawo mata dawani irin sauri tazabura ta mike zaune zata sauka daga gado Miemie tariketa tace Ammi tsaya kinji dan Allah Ammi da zuciyanta yashiga bugawa dumdumdum tace Miemie ina Amirah? Babanki yasa mazan nan sun tafi da ita? Ahankali Miemie ta gyadama Ammi kai, gaban Ammi yayi wani mummunan faduwa sai kawai ta kalleta tace kira Dr a sallameni, bazan iya zaman asibiti bansan wace duniya Amirah take ba, kome zai samen ya samen gyadama Ammi kai Amirah tayi batare datai gardama ba tawuce tafita takira Dr sai gasu, Dr yace Hajiya kibari agama miki treatment BP ki is very high maisa kikeso a sallameki cikin dauriya dan daurewa kawai Ammi take tace nabar diya mara lafiya agida, lafiyanta shine gabana likita banawa ba dan Allah ka sallameni sauri nake, ganin yanda Ammi take magana sai kawai Dr yaji tabasa tausayi yace okay amman ki dinga zuwa duk say sati dan mu dinga managing BP naki sannan you need to sign this discharge against medical advice form gyadamai kai Ammi tayi tai signing komi, Miemie tashiga hada kaya tass Mamie tazira hijabi ance subiya 5k suka biya suka fito Ammi bamatajin karfi jikinta amman tafiya kawai take har titi suka tare keke sai gida. Shiga gidan sukayi bakowa agidan babu motan Daddy bangaren Maman Baby ma a kulle alamun batanan, Ammi kawai tafiya take tana shiga flat nasu koina tabi da kallo kafin tafada ban daki ta dauro alwala tai sallolin da ake binta dan Allah ne fark before anything saita shiga kiran Daddy wayansa na ringing baya dagawa, da kyar tasamu akaro na kusan 20th call aka dauka, muryan Maman Baby taji tadauka tace dan Allah kadauki wayanta kar bakin ciki ya kasheta sweetheart muryan Daddy Ammi taji yace tunda kin rokan mata ai hikenan yasa wayan a kunne yace yi maganan ki da sauri dan tuki nake Zainabu dakewa Ammi tayi tana rike abinda ke zuciyanta saita kalli Miemie dake gwfebta tace bani wuri Miemie ki rufomin kofa ta ashi Miemie tayi jikinta asanyaye tafita daga dakin tarufo kofa amman saita kasa wucewa ta tsaya tareda jingina kanta jikin kofan. Da kyar Ammi tadaure tace Baban Baby ina Amirah? Wani dan dariyan shakiyanci yayi harda shewa yace har abada bazaki san inda Amirah takeba idanma abinda yasa kike kirana kenan gwara ki kashe dan bazan gayamiki ba wani abu Ammi taji yazo mata wuya ahankali tace Baban Baby dan Allah dan darajan sa, kaduba girman Allah kagayamin inaka kai mini Amirah, karaman yarinya ce dabai kamata tana inda maza sukeba, idan suka keta mata haddi fa, ba hijabi ba takalmi ba hula jikinta, Amirah batasan komi akan rayuwa ba batada wayan kara kanta idan suka mata wani abu fa, katuna akwai Allah yarinyar nan marainiya ce, kafadamin ina ka kaita tsaki Daddy yaja yace ai saikuma kiyi keda ganinta har abada dan wlh wlh wlh kinji na rantse miki mahaukaciyan nan bazata kara dawowa cikin gidana ba har abada wlh kuwa ki mutu idan zaki mutu munyi tafiya sai nan da yan kwanaki zamu dawo ya katse wayan Ammi tace Baban Baby Babban Baby tai maza tasake dialing number taji akashe takira Number Maman Baby shima akashe duk dauriya irin na Ammi kawai saitaji kuka yazo mata tafashe da kuka sosai dayasa Miemie tadaura hannunta akan bakinta tana rushewa da kuka itama. Takai morethan 20mins ahaka saita daga wayanta tai dialing wani number ringing daya aka daga wani dattijon namiji ne yace
Chapter 19 · 0% Book details