← Book details Baccin So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 87

Sashe 71

Baccin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yamata wani kwarjini yakuma kara kyau, farin T-shirt ne ajikinsa dawata 3quater na common flag green kaman na sojoji, fuskansa yayi ja, idanunsa sanye dawani glass farare dasuka kara masa kyau sosai, gashin kansa yayi coils sosai kaman bai taje ba dayayi wanka hakama sajensa da dan karamin gemunsa, yakai kusan 1min a motan sai kawai ya yunkura yabude kofan motan yafito yawuce wajen kofa saiya tsaya tareda juyowa yama motan wani mugun kallo dayasa Amirah taji kaman zatai fitsari ajiki, hannunta na rawa takai ta bude kofa tafito ahankali kanta akasa tana wasa da yatsun hannunta batare data kallesa ba, tamaida kofan tafito tafara tafiya ahankali tana zuwa wajen, dudda yanda Marwan baiso yama daura idanunsa akanta amman kasa daurewa yayi, daura manyan jajayen idanunsa yayi akanta wani abu na fizgansa yana fada da abin dan he s trying his best ya danne any feelings na so dayake dashi akanta dan he s so damn angry with her, ya tsareta da idanu yana kallon kafafuwanta daga hijabin da ake gani abu yakara zuwa wuyansa sabida wani mugun fitinannen kishi, abun ya tsaya yamai katutu awuya, harta karaso wajen, sumsum tabi ta gefensa tashiga falon danya bude mata kofan daman ahankali, shima shigowa yayi kawai saiya maida kofan ya kulle kofan da key hakan yasa Amirah tajuyo ta kallesa, juyowa yayi yazare key yasa a aljihun wandonsa yawuceta kaman baisan tana wajenba yayi staircase yafara hawa Amirah tabisa da kallo yanda bai kulata ba, bai kalleta ba, yana abu kaman baisan wacece itaba ya tsayamata arai kaman ya tsaneta. Abu taji ya tsaya mata a wuya ganin ko kallo bata ishesaba kawai saita fashe da kuka ahankali tazauna akan kujera awajen tana matsa hawaye, first of all batasan metayi ba exactly, Miemie ta taba cemata Ya Umar nada kishi to shima Ya Marwan nada kishin ne? Sabida tarike hannun yayansa? Ai mistake ne tadauka shine kayansa yasaka, mesa yake fushi haka? Kuma ita bazata iya mai magana ba tsoro takeji karya mata duka itama. Tana zaune awajen gashi batai salla ba amman tsoron zuwa sama ma takeyi tashi tayi ahankali saita shiga bayin dake nan falon ta dauro alwala tafito tana kallon falonta dayayi kyau tana kokarin tuna gabas nan da nan tagane dan tayi salla agidan ai rannan saita fara salla cikinta namata ciwo na yunwa, sai kallon kitchen take ahaka tana zaune har la asar tasake zuwa tai salla abinta, jin yunwa kaman zai halakata yasa tamike tsaye ahankali tawuce kitchen data gani a wajajen dinning a falon. Gab da za ayi bikinsu daga rannan da Ammi tace an mata aure suka fara koyamata girki da yanda ake amfani dasu gas, shiga kitchen din tayi saita tsaya jimmm, ganin gas din dake nan ba irin gas din dasu Ammi suka koya mata yanda ake amfani dashi bane, kusan burners 6 ne akan gas din ga buttons dayawa na kunnawa chunkushe waje daya wanda batasan wannene na wannan, wannene na wanchan ba, cire hijab na jikinta tayi ta ijiye kan daya daga cikin kujerun dayake zagaye a island na tsakiyan kitchen din, saita tsaya saikuma tajuya tawuce tashiga store na kitchen din, the first abu da idanunta suka gani is kwalin indomie dasauri tadauka tabude dan bama abude ba saita ciro indomie guda daya ta maida kwalin ta ijiye ta dauki egg guda biyu tafito tazo gaban gas din ta tsaya tana kalle kalle saitakai hannunta ta kunna guda daya tadaiji shuuu amman batamasan wani gas ta kunna ba, saita rufe garin rufewa ta kunna another one kadan amma gas din yahau fita amman babu kara sabida kadan ta kunna, all this while bata saniba ta tsaya sai lissafe lissafe take, saitasa hannu tadauki lighter na kunna gas din tarike a hannu takai hannunta ta murza another different gas yafara kara Cikin bacci mai nauyi daya kwashe Marwan yaji warin gas dasauri yabude idanunsa yamika hannu yadauki glass yasaka ya kunna wuta yana tashi zaune, warin gas yaji sosai, kawai Amirah ne tafado aransa yana tuna the first abu dayaji tafadi this morning she s hungry, bugawa kirjinsa yafara baisan sanda yawani yaye bargo ya dirko daga gadon dagudu ba dagashi sai dan short ba singlet ko dogon wando jikinsa, yashiga saukowa daga stairs dawani kalan sauri yayi wajen kitchen daidai Amirah na kokarin kunna lighter, daga wajen yayi wani ihuuuu. Amirahhhhhhhh! Awani kalan firgitce Amirah tajuyo daidai yataho dagudu kaman zaki ya fizgota zuwa jikinsa tawani fado cikin kirjinsa atsorace, ya karbe lighter hannunta ya jefar yakai hannu yana kukkulle gas guda biyu data bude yariketa gam ajikinsa yawuce yashiga bude window na kitchen din dan gas din yafita Amirah tadan sa kallon fuskansa he looks so damn worried and scared she could feel yanda kirjinsa ke bugawa gashi yarike gam protecting her with his entire life kaman yar baby dinsa kawai taji zuciyanta yawani narke yayi melting yabude kofan kitchen din na baya shima sannan ya tsaya awajen sai alokacin ya lura da yanda ya kankameta ajikinsa dasauri yasaketa ahankali Amirah takoma baya kanta akasa, cikin tsananin fushi Marwan yace what are you doing in the kitchen? Kasa kallonsa tayi takuma kasa magana, tsawa yadaka mata. Badake nake magana ba ? Dan dagokai tayi saita kasa kallonsa ahankali tace yunwa nakeji indomie da 2 egg dayagani kan island yabi da kallo kirjinsa na bugawa cikin tsananin fada yace bazaki iya zuwa ki sameni kicemin kinajin yunwa ba? What if something happen to you? Dayaya kikeso nayi da kaina? What if you got hurt? Ina kikeso nasa raina? Are you trying to kill me Ameenatu?? Ahankali Amirah tadago kanta for the first time takalli fuskansa jin maganganun dayayi that were shouting I love you Amirah I can t leave without you, hada idanu sukayi wani kunya Marwan yaji da maganganun daya fada da baimasan tayaya yafadesu ba, juyawa yayi dasauri strictly yace leave this kitchen kafin ranki yabaci ahankali tajuya sumsum tawuce tafita, ya tsaya a kitchen din shi kadai har lokacin bugawan zuciyansa bai dawo daidai ba, kusan 5min sannan ya kunna gas din da Kansa ya ja tsaki yadauki pot yasa akan gas din cikin 5min yadafa mata indomie da boiler eggs, yasa mata a bowl yadauki fork yasaka yakashe komi yafito daga kitchen din dan dagokai Amirah dake falon tayi suka hada idanu dasauri tasauke kanta, ijiye bowl din yayi akan dinning kawai yawuce stairs yayi sama abinsa Amirah tasake binsa da kallo saita taso ahankali tazo dinning din ta kalli indomie daya dafa mata saita kara kallon sama wani sanyi taji aranta saitaja kujera tazauna ahankali tashiga ci maganganun dayayi dazu nadawo mata akai. bazaki iya zuwa ki sameni kicemin kinajin yunwa ba? What if something happen to you? Dayaya kikeso nayi da kaina? What if you got hurt? Ina kikeso nasa raina? Are you trying to kill me Ameenatu?? Wani shauki taji ya lullubeta, he s angry but he s still very sweet and caring even though he is angry. EPISODE 8 Daki Marwan yawuce yashiga, har lokacin his heart was racing zuciyansa nata gayamai wat if something yasameta dayaya zaiyi? He was so scared, kodayakai sama saida ya tsaya yakara lekota ahankali ta saman bene yaga takai indomie baki tadanyi murmushi kadan ya tsareta da idanu, wani kalan sonta yakeji a zuciyanta kaman zai halakasa, kokarin dago kanta sama Amirah tahauyi hakan yasa yabar wajen da sauri baiso tagansa, soyake yayi wanka yayi salla, baimasan ya akayi bacci mai nauyi yadaukesa ba, wayansa ne yahau ringing hakan yasa yakai hannu yadauka yaga Farida ne, hannu yasa yadauki wayan batare dayayi magana ba dasauri tace Yaya muna kofar gida Mami tabamu abubuwa mu kawoma Ya Amirah dan jim yayi saiyace okay cire wayan yayi daga kunnensa alokacin yaga text message from Saleem he knows Saleem so well da yasan yana bude text message dinnan ransa bac zaiyi kawai saiya ijiye wayan akan gado, yawuce closet dinsa yasa jallabiya saiya fito Amirah na dinning tanacin indomie ta yafito tadan saci kallonsa ko inda take bai kalla ba, yawuce kofa yasa key yabude saiya fita yabude gate, Farida da Faiza yagani da flask har biyu saikuma wayan Amirah, strictly yace get in wucewa ciki sukai da sauri, shiya tsaya yana maida kofan yarufe suka shiga falo Amirah na ganinsu ta mike tana murmushi suma haka suka taho wajenta da sauri da flask din suna ijiyewa kan dinning Faiza tace indomie kikece ga abinci mun kawo, wannan kazanki ne Mami tace ke kadai zakici dasauri Amirah tasa hannu takarvi karamin flask din tana budewa tace Mami ta dafamin, girkin Mami dadi duk suna tsaya suna kallonta yanda take magana saita dago manyan idanunta ta kallesu tace ku zauna muci tare tai maganan daidai Marwan na shigowa falon dan satan kallonta yayi sabida aya da maganan yafito straight daga harshenta was so unlike her, suna kokarin bata amsa Marwan yace Kids dasauri suka juyo suka kallesa yau kowa is minding his business sabida ansan ransa abace yake, wani mugun kallo yamusu yace kuzo kutafi wani iri Amirah taji wlh taso su zauna saiga hawaye yacika idanunta Farida tace ga wayanki don t cry gobe ma zamu dawo gyadamusu kai Amirah tayi hawayen na suakowa takai bayan hannunta ta share suka wuce suka fita Marwan yarufe kofa yajuyo yawuce staircase harya fara hawa saiyadan kalleta yanda take share hawaye kaman zaiyi magana kawai saiya wuce abinsa, dago kai tayi ta ballamai harara tana turo baki saita bude kulan kazanta tadebi Kazan da romo sosai tazauna tafara ci dadinsa baima bari tagane Kazan magani bane tass ta cinye ta shanye romon saita wuce takai pates kitc hen ragowan kazanta tasaka a fridge, shikuma dayan tabarshi a dinning tawuce tadawao falon bayan tasaka hijabinta ta zauna akan kujera tana danna wayanta tanaso takira Ammi da Miemie but bataso takirasu yana gidan, daganan tafarajin kamshinsa saukowa yashiga yi ya chanza kaya zuwa kaftan ash color riga da wando yana baza uban kamshi dan Satan kallonsa tayi kirjinta taji yana bugawa wani abu na fizganta tsabagen yanda yayi kyau looking very classy and expensive dasauri tadauke kanta ta kwanta a kujera tai lamoooo ko kallon inda take baiyiba yawuce kifa yasa key yafice tanaji yana kara kulle kofan da key jin bai
Chapter 71 · 0% Book details