Sashe 68
Baccin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
bayan motan kafinma nurses u bude ya tsaya turus yana kallon Saleem da har lokacin yake a sume jikinsa duk jini nurses sukace dan gyara Alhaji waigawa Abba yayi ya kallesu saiya masa gefe agabansa aka ciro Saleem aka sashi akan bed din aka wuce dashi ciki saiya juya yakalli Amirah da itama ake fito da ita aka sata a gadon aka wuce dashi su Ya Ammah da yaran suka bisu ciki da gudu sai Mami ta taho ahankali ta tsaya gaban Abba dake kallonta idanunta yayi jajir tama rasa mezatace saitamaba Abba tausayi hannunsa yamika ahankali yakama nata yace muje ciki cikeda damuwa kuka ya kufcema Mami tace bazaka tambayeni meya faru ba? Tsareta da idanu Abba yayi, sai ahankali yace meya faru daya wuce daga samun lafiyansa ya nemi Matar dan uwansa Marwan na nada masa na jaki haka? Bunsuru ne fa Saleem cikin fushi Mami tace kadena kiransa da sunan nan, bansan meya faru ba amman Saleem bai nemi kowa ba a staircase nafito nagansu dukansu suna parking aka ukun Abba bai sake magana ba yashiga tafiya chan yace meya sami Amirah ? Mami tace sumewa tayi mijinta ya tsallaketa yawuce abinsa Abba bai sake cewa komiba. Bazaka taba iya tantance wani yanayi yake ciki ba, tafiya suka shigayi zuwa cikin asibitin duk suka samu waje suka zauna. Kusan 1hour sukayi wani babban baturen Dr yafito, anatse Abba yatashi Mami tabisa Dr yace Alhamdulillah Alhaji he s fine now he s awake, yasame yanka biyu ne daya akai daya a goshi but munyi stitching he s very much okay, zamu rikesa for one more hour mu tabbatar babu wani concoction saimu sallamesa gyadamai kai Abba yayi yace diyata fa? Dr yace banine Dr dake kanta ba but I will check on her and update you itama gyadamai kai Abba yayi yace thank you Dr yaba Dr hannu suka gaisa sai Dr yawuce yakalli Mami anatse yace wait for me here dan kallonsa Mami tayi saita gyadamai kai yawuce tabisa da kallo, she s feeling so guilty Marwan yama Saleem mugun duka wlh koma Menene yayi bai chanchanci kalan dukan nan ba kodan darajan yayansa wlh, gashi Abba yaki nuna yana fushi kuma tasan babu wanda zaiga kalan dukan nan yaji dadi. Bude kofan dakin Abba yayi Saleem na kwance kan gado idanunsa biyu ga bandage a goshinsa daya akansa an cire masa rigan jikinsa dagashi sai wando idanunsa biyu yana kallon sama dudda yaji an bude dakin amman bai dago kansa ba maida kofan Abba yayi yarufe bazai iya kiran abinda yakeji towards Saleem as tsana ba amman wlh wlh tun bayan sex video Saleem daya kalli yakejin ya tsani Saleem yasan bai tsanesa ba tsabagen bakin cikinsa da taksicin sa ya a yakejin haka amman yanda yakejin haushin halayyan yaron nan kaman yakamasa yayita duka cus an kirasa a office dazu kan precious tazo wai tana neman mijinta Saleem security da yansanda Abba ya a aka koreta ana cikin haka Faruda ta kirasa kan Ya Marwan da Saleem na fada, takaicin yaron yataru yama Saleem yawa da yanzu tausayinsa ma bayaji gani yake kome yasamesa shiya jama kansa, gaban gadon yaje ya tsaya yayi folding hannunsa a kirji cikin kakkausan murya yace mekama Marwan? Kaman badashi Abba ke magana ba ko motsi baiyiba, cikeda fushi Abba yace badakai nake magana ba? Nace mekama mai? Matarsa kayi yunkurin nema yakamaka? Juyo da kansa Saleem yayi for the first time yadaura jajayen idanunsa akan na Abba, yana nanata kalman matarsa dazuma da Marwan na dukansa yaji sanda ya furta my wife, Abba yace neman matarsa kayi da alfashan daka saba? Wani abu Saleem yaji azuciyansa sai kawai yafara tunani yana connecting dots mezai kawo Amirah gidansu harta kwana? Marwan ke auren Amirah how? Da kyar yace Amirah ce MATAR MARWAN yaya? Cikin bakar zuciya Abba yace kwarai! Kajini da kyau, na aurama Marwan Amirah tun rannan da aka nemeka aka rasa wajen daurin aure! Wani kalan bugawa kirjin Saleem yafara dayake ba riga jikinsa zaka iya ganin yanda zuciyansa ke bugawa wasu hawaye ne masu masifan zafi suka zubomai yadago jajayen idanunsa yace mesa baka tabamin adalci Yaya? Mena maka ka tsaneni ina matsayin jininka? Menene exactly namaka? Nataba sata? Nataba bata maka suna? Nataba kunyataka na tozarta ka? Amirah is the only girl dana tabaso aduniya kasan haka amman ka dauketa kaba kanin matarka! Abba na kallonsa yace kwarai and I will do that again and again butulu kawai mara mutunci look at abinda kake fadi kanin Matata kake kiran Marwan yaron that has been there for you saving you looking after you, you are a very very useless boy mara hankali Wawa kawai shashasha mai halin dabbobi Yunkurowa Saleem yayi yataso azuciye yasauka daga gadon yayi kan Abba yana huci JAMA A DUKAN ABBA SALEEM ZAIYI??? EPISODE 7 Saleem na huci sosai kaman zai dakesa ko gezau Abba baiyiba Saleem ya tsaya gabansa dudda yanda yakeji kaman yarufe Abba da duka sabida aurama Marwan Amirah dayayi saikuma yakasa Abba yakai hannunsa yakama hannuns yadaura akan jikinsa yace dakeni mana Saleem ka girma ai yanzu, ni yayanka da tun kana dan shekara uku aduniya kake hannuna ka yunkuro zaka daka dakeni Saleem dakeni ran Abba yabaci sosai, saikuma Abba yashiga taba aljihunsa yaciro wayansa yabude watsapp yace bantaba ijiye video na banza awayata ba amman na ijiye wannan sabida rana kaman haka ya kunna video yakama hannun Saleem yasaka wayan yace watch abinda katuramin wayan na hannun Saleem but kasa kallon yayi tanajin yanda yake ihu hakama Precious dasauri yakashe wayan gabaki daya Abba yanuna kansa yace ni kakira wajen daurin aure video call kana shan mama kana gayamini kafasa auren na aurama wani, Saleem kasan kalan manyan mutane business partners dana tara wajen eh? So kake a maidani karamin mutum, Marwan yana gadon asibiti baisan komiba salati kawai nafara tunaninsa yazomin nasan duk duniya babu wanda zai rufamin asiri sai shi haka nasa aka daura aure daga Marwan har mahaifiyarsa basu saniba sai bayan angama naje asibiti na sanar dasu, da kyar na lallabasa yace yarda. Dago kai Saleem yayi idanunsa sunyi jajir saiya kalli Abba dasauri saiya duka yayi kneeling gaban Abba, Abba yabisa da kallo, ahankali yace Yaya nasan namaka laifi dayawa amman kaga some of them ba laifina bane wlh, lokacin dana fasa auren duk ina cikin asirin Precious ne, yanzu I m fine na saketa kuma na rantse da girman Allah daya halicce ne wl h wlh bazan kara zina ba, bazan kara shan wani abuba, amman dan Allah Yaya kasa Marwan yasakan mini Amirah ta na aureta . Wani kallo Abba yamai kallon kana hauka, Saleem yace Yaya ni banmata komiba yau masallaci zanzo kawai naji an rikemin hannu daidai Marwan na shigowa, nida banmasan tana gidan ba, nida bansan anyi auren ba, Marwan ya tsaneni akan idanunku yake nuna yana sona cewa yayi zai kasheki ba lallai su Mami su gayama ba tunda yana uwansa ne amman halakani yakeso yayi, Yaya kacemai yasaken min Amirah na aura kaji Yaya Wani dan dariya kadan Abba yayi na manya saiya juya yajawo plastic chair dake wajen yazauna yana kallon Saleem dake duke wajen yace Saleem kenan ka dauka yanzu dane Abba ya karkada kafafu saiya kama yatsunsa yace kaga Saleem daka shiryu, da karka shiryu, dakai zina da karkayi uwarsu daya ubansu daya wajena! Kai idan kagama dama kab duka karuwan duniya gadai sakamako Allah yafara nuna maka tun yanzu, kome zakayi da rayuwanka kayi I don t care anymore nayi iyakan bakin kokarina, abu daya zan gayamaka aure tsakanin Amirah da Marwan zama daram! Babu abinda zai raba auren nan har abada ka mutu idan zaka mutu zamu kaika mu binne amakabarta, kasake daga idanu ka kallonmai mata wlh ko halakaka Yayi bazanyi magana ba sabida abinda yadace da kwarto kenan Abba yana maganan yajuya Saleem yabisa da kallo zuciyansa namai suya Abba yasa hannu zai bude kofan cikin kakkausan murya Saleem yace kazabi Marwan akaina dan uwanka Yaya? Juyowa Abba yayi yakallesa yace kwarai! Aure kuma ba fashi ba Amirah ce kadai aduniya ba kaje ka nemo taka Matar ka auro, kuma ka gargadi matan banzan ka da zuwan mini company, idan an sallameka you know you way back home Abba yabude kofa yayi ficewansa abinsa, mamaki yagama kashe Saleem sabida yasan yanda Abba ke sonsa yana nannan dashi yana tarairayansa Abba dahar tashi hawan jininsa yakeyi sabida damuwa akansa amman yanzu kaman anyi asiri an rabasu, Yaya baya kaunar sa baya tausayinsa kaman da Marwan yakeso, wani kalan zafi zuciyansa ke masa, dukan da Marwan yamasa nakara masa ciwo, what happened dazu was yana cikin shock na ganin Amirah da kuma sha awa sabida yanda gabansa yatashi yaji saukan kwalba unexpectedly inba hakaba har wannan cry boy din ya isa yadakesa. Abba na fitowa yahada idanu da Mami dake gefen kofan suna hada idanu tai maza tai kaman bataji komiba tace Alhaji daman zanje wajen Amirah ne nace nazo nagaya maka gyadamata kai yayi yace muje nadubata wucewa sukayi daga ita sai shi zuwa 2nd floor nan ne dakin Amirah, Mami tabude kofa tana zaune kan gadon an saka mata drip tana sanye da kayan hospital idanunta a lumshe bacci take, Abba ya tsare fuskanta da kallo tunda yake baitaba kallon fuskan yarinyar da kyau bama sai yau saiya kalli Mami strictly yace once she s awake I want her agidan mijinta bamu ta aurama mijinta ta aura, zanje gida nayi magana da Marwan and send him here yadauketa su tafi gidansu and leave like a married couple Mami taro ka ta lura akwai fushi adan tattare da Abba so kwata kwata batai musuba tace to Alhaji yin abubu hannu Abba yadaga mata yace allow them to figure everything out mijinta zai kula da ita, kulawansa da taimakonsa yasa taji sauki to this level so let them live together gyadamai kai Mami tayi tace shikenan anatse Abba yace stay with her karku barta ita kadai adaki in this hospital da wanchan yaron gyadamai kai Mami tayi, Abba yajuya bari natafi harya taba kofa Mami tarike masa hannu ahankali tace Alhaji dan juyowa yayi yakalleta instead of Mami tai magana saita rungumesa ahankali tana shafa bayansa without saying a word