← Book details Baccin So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 87

Sashe 18

Baccin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Allah calm down ba a gyara kuskure da fushi takalli Saleem tace kuwuce kuje ku kwanta Saleem gobe zamuyi magana wucewa azuciye Saleem yayi yace okay Mams Marwan yabi bayansa, sukai sama instead of Saleem yashiga dakinsa dake gaban na Marwan kawai yabude na Marwan ya shiga Marwan yayi dan jimm saiya shigo baice komiba, yamaida kofan tarufe Saleem yashiga cire kayan jikinsa yana jefarwa duk inda yaga dama yarage dagashi sai boxer yafada bayi, dukawa Marwan yayi ya kwashe kayan nasa tass dake wari shaye shaye ya tattara yakai Landry basket yazuba sannan yawuce yafita daga dakin koda yakoma kasa su Mami basanan anma kashe wuta sunje sun kwanta kitchen ya shiga yahada lemon tea yana warware hangover nasu giya da shaye shaye, sai yayi frying egg guda 4 Yayi toasting bread yadauki karamin bottle water duka yahada a tray sannan yakashe komi yafito yataho sama har dakinsa yabude kofa har lokacin wanka yake normally yana dadewa a bayi, ijiyemai abincin yayi kan study desk dinsa inda ka top nasa yake da folders daya kawo daga hospital na patient, ya ijiye wani kati na kwayan magani guda daya shima yana kara flushing toxins daga jiki, yadauki pen yarubuta eat and drink this, yakashe wutan dakin ya kunna mai wutan study desk din dake haska abincin sannan yakunna mai wutan closet kafin yajuya yawuce gado ya bala in gaji ya kwanta yana cire glasses nasa ya ijiye kan side drawer dake gefensa yayi addu a yashafa ajiki ya kwanta ko 2min ba a dauka ba yayi bacci dan yagaji sosai lokaci was already 2 nadare. Wuraren 2:15 Saleem yafito ya tsaya yana kallon abincin daya hadamai a study desk yakallesa yana gado yarufa da bargo sai kawai yawuce closet, pajamas dinsa yadauka yasaka yafito ya shinfida dadduma yayi magrib da isha i yatashi yazauna akan kujera yana kallon rubutun dayamai yakalli kwayar maganin wanda baisan na menene ha amman yabude kawai ya jefa abaki yasha yana daukan tea ya kurba, yadauki spoon yadebi egg yakai baki saiya tsaya yayi wani dan tsuki yana murmushi daya wani irin karamai kyau yace what a terrible cook saikuma ahankali yace is after 2 I m hungry I have to eat it like that shaye shaye nasa kaji yunwa, he knows Marwan yasan da hakan saisa ya ijiyemai abinci tass ya cinye komi dan shi yanada cin abinci, yadauki tea yashiga sha idanunsa suka sauka kan folder ahankali yakai hannunsa yace s see wani case kebama yaron nan headache cus any folder daya kawo g da means one thing the case is intriguing and he needs to study more or dig more yabude file din yanabi da kallo yanashan tea, Aminatu Adamu, born 2004, an kawota akace autism .. saida yabi komi ya karanta down to treatment da Marwan yamata yau zuwa sanin Babanta ne yakawota asibiti she was agrressive ta cije baban dariya yayi yace woww wat a fiesty little girl, inason yara haka, aida kin yayyaga old man dinki da kumba, if I ever see you I will tell you how to handle all this trouble some old niggas, mine too is disturbing my life Yayi maganan yana rufe folder kawai ya ijiye. Yamike tsaye ahankali yayi murmushi yace Aminatu Adamu Daddy s biter yadauki wayansa yawuce zuwa gado yahau gadon ahankali harzai kwanta saiya kunna touch nasa ya haska Marwan dake bacci ya kalli wuyansa dayayi ja sai yadanji wani iri yace bakasan yanzu mun girma ba when will you stop taking beating for me foolish boy, he s just too caring, i thought by now he will realize not everyone deserves it especially me cus gobe still sainaje club ya kwanta yanandago bargo yarufa sai bacci. Wuraren 5 Marwan yabude idanu da kyar shima kawai dan jikinsa yariga yasaba da tashi around that time ne for subhi, ahankali yamika hannu yadauki glasses naaa yasaka sannan ya yaye bargo yatashi zaune yana addu an safiya kafin yamike yawuce yafada bayi saida ya gyara bayin sannan yayi wanka yafito yashiga closet nashi ya shirya yafito cikin wata milk jallabiya yasa faran hula yana kamshi yazo gadon ya bubbuga Salim yace Saleem, Saleem, Saleem da kyar Saleem yayi motsi yace if I have the chance stitches your mouth Marwan ahankali yace tashi muje muyi salla saika dawo ka koma bacci, tashi tashi kafin Abba yazo Sarai yasan yayansa ruwan sanyi zai zuba masa hakan yasa yabude idanu da kyar yaki motsi yace I can t feel my body dagasa Marwan yayi yawuce yashiga bayi yadauro alwala yafito jallabiyan Marwan yadauka daga closet yasaka yafito yana hamma ya ballama Marwan harara dake kallonsa yace mugu murmushi Marwan yayi suka fito suka wuce mosque. JAMA A GA SALEEM GA MARWAN!!! ME KUKE GANI ZAI FARU?? KUN TABA GAN N KANIN DA SHIKE KULA DA YAYA? AGANIN KU WA AMIRAH ZATA AURA?? EPISODE 1 Miemie sosai take buga kofa tana kuka sosai tana kwalama Ammi kira amman shiru kuma babu yanda za ayi ace kap gidan nan ba aji ihunta ba dan harta window taje ta tsaya tana ihu tana kiran su Maman Baby amman shiru, dasauri tai wajen wayanta dake kan gado tadauka jikinta har rawa yake tashiga dialing number Umar, a ringing na farko bai dagaba ana biyune ya daga, cikin kuka sosai tace Ya Umar kana ina? Dadan damuwa yace menene kike kuka meya sameki? Gani a gareji cikin kuka Miemie tace dan Allah kazo gidanmu yanzu ka shigo har side namu dadan tashin hankali yace wait why are you crying like this? Dasauri tace zan fadamaka kazo kashigo ciki ahankali yace ya za ayi na shigo cikin gidanku babu izini tasan gaskiya yafada hakan yasa tace Ammi ta sume ne kuma kanta yabugu ni ina daki a kulle kuma babu kowa dazai budeni nabata taimako you are the only one I could think of, dan Allah kazo Ammi first we will deal with koma menene later ahankali yace okay gani nan zuwa tana tsaye awajen jikinta rawa kawai yake bini bini tana share hawayen dayake saukowa daga idanunta hankalinta atashe batamasan meke mata dadi aduniya ba ina yakai Amirah? Wani matashin saurayine dazaikai shekaru 30 haka aduniya kakkarfa bafulatani yayi parking Wayyo kudina a kofar gidan yana sanye da kayan gajere dan bakaniken mota ne yaciro wayansa yayi dialing number dayasa my wife ajiki ringing daya Miemie tadaga jin tana kuka har lokacin yace waiba nace kidena kuka ba, nothing will happen to Ammi, gani awaje cikin kuka tace to kashigo flat dinmu ne na karshe ai kasan flat din ko rannan dakuka zo ganin Daddy ahankali yace eh nasani katse wayan yayi ya kalli gate din dudda he s feeling uncomfortable amman haka yabude gate din yashiga luckily babu kowa a tsakar gidan yawuce flat nasu sallama yayi yadaga labule yashiga yana hango Ammi akasa flat ga jini agoshinta daya kumbura yace Subhanallahi yayi wajen jin muryansa yasa Miemie ta jijjiga kofan tace Ya Umar ina nan budeni kofan ya kalla sai yayi wajen ya murza key dake jikin kofan yabude Miemie data saka hijab dinta har kasa tayi wajen Ammi da gudu tarushe da kuka tana dagota tana jijjigata. Ammi, Ammi Ammi, Ya Umar Ammi na ta mutu ne ? Dasauri yace t say that yamike cup ja ruwa daya gani akan table yadauka yazo wajen yadan debi kadan ya yayyafa ma Ammi a fuska amman ko gezau batayiba Miemie tarude jijjiga Ammi kawai take kaman mahaukaciya duk takara daburta Ya Umar the only thing dayazo kansa is. Bari nakira keke mukaita asibiti Miemie tace kafadamin gaske ta mutu ko shine bazaka fadamin ba Ya Umar yace waiba nace kid ena magana hakaba cikin tashin hankali tace to maisa bata farfadowa bayan mun watsa mata ruwa inba mutuwa bane, idan Ammi na ta mutu nima saina bita Ya Umar ganin yanda kaman ta haukace saiya duka kusa da ita abinda baitabayi ba yayi yakai hannunsa yakama kuncinta yace Maryam put yourself together babu abinda ya Ammi we will take her to hospital dole ke zaki tsaya mata so kudawo hayyacinki kina jina gyadamai kai tayi yamike dasauri yafita. Ko 3min bai bataba yadawo suka shigo da keke yabudema Keke gate aka shigo Miemie tasama Ammi hijabi yashigo dakin shida Miemie suka kamata suka fito da ita daidai Maman Baby na zuwa wajen tace Au karuwanci kika fara kike kiran saurayin naki har gida dukansu biyu babu wanda yabi ta kanta sukasa Ammi a keke keke yafice Unar ya sauka a waje yahau machine nasa yabisu abaya. Wani karamin primary health care center sukaje suna zuwa aka karbi Ammi dasauri Miemie tazauna tana kuka shiya biya kudin komi da yan kudaden dayake dashi sannan yadawo yazauna gefenta yayi shiru yana kallonta tabasa tausayi wlh yanason Maryam sosai bata taba fadamai anything akan family ta ba but zaman tare yadan lura da yan abubuwa from rannan dayazo tambayan aurenta Babansu baice komi akan Miemie ba amman yanda yadinga kiran Amirah da mahaukaciya dakuma yanda yadinga kaskantar da Ammi agabansu he knew something is going on just like that yasan Ammi bazata fadi hakaba Miemie kuma a kulleta adaki ba sannan baiga Amira ba, he knows something is going on ahankali yace Maryam dago rinannun idanunta tayi tace ahankali yace ina Amirah? Tsare Umar tayi da kallo wani kuka nataso mata kawai saita shiga rerama Umar kuka tama kasa magana but kukanta said a lot tace bamusan inda Daddy yakaita ba Ya Umar yayi shiru saikuma cike da tausayi yace ya isa stop crying kar zazzabi yakamaki, kika fara zazzabi ina zansa kaina eh kinaso nakasa aiki ne? Girgizamai kai tayi yace okay we will do this first thing first, muji da Ammi yanzu dake gabanmu muji ta farfado, tunda Amirah natare da Abba zamu nemeta okay gyadamasa kai tayi ahankali, yazaro handkerchief mai kyau daga aljihu yabata yace wipe your friends mujira Dr I m here for you okay, you are not alone Wifey wani sanyi Miemie taji aranta Umar nada kirki sosai baida wani kudi tasan kwanan nan he s working times 3 sabida yahada kudin aurensu yana hada akwati akwai dan karamin filin dayake dashi daya daha ginin gadan gadan dan awajen yakeso su zauna gashi duk yakashe kudi anan
Chapter 18 · 0% Book details