← Book details Baccin So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 87

Sashe 3

Baccin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

kallona nace kiyi ba tashi kizo nan nakama suman nan naki ahankali ta tashi ta linke dadduma da hijab ta ijiye inda Ammi ke ijiye saita taho dayake abakin gado Ammi take zaune tana harhada ribons nata dasuke cikin wata yar karaman jaka daban hawa gadon tayi ta kwanta tadaura kanta kan cinyan Ammi, Ammi takalleta tace ai yamiki kyau mage saita dauko comb zata fara kifa kanta yayi a cikin Ammi, Ammi tace zan kwadeki idan baki tsaya ba tunda ke baki kaunar ataba miki kan nan, kinfiso kiyita tsorata mutane dashi, bani kan nace ahankali tafito da kan tasa akan cinyan Ammi, suka fara. Tun tana yar yarinya batason ataba kanta dambe ake sosai, itama Ammi saida tayi da gaske hakan yasa ko yanzu ma ahankali take taje mata gashin, gashinta is so silky and very black kuma bata tabasa relaxer ba, kama gashin tayi agida biyu tsaf tagama hakan yasa tajuyo da kai tana kallon Ammi, Ammi tai murmushi tace iyye Yammata na tayi kyau Masha Allah, yimin murmushi nagani yayyy tsayawa Amirah tayi tsuru tana kallon Ammi sosai dake murmushi kaman zata hadiye Ammi da manya manyan fararen idanunta, ahankali Ammi tajuyo dakatar da murmushin datakeyi tai shiru sai kuma idanunta suka cicciko da hawaye dasauri tadauke kanta tadanja hanci irin maison hadiye kukan nan jikinta yayi sanyi looking very sad, kama hannun Ammi Amirah tayi tashiga wasa dashi tana tattaba hannun tana wasa da fingers din Ammi tana nannade wannan da wannan, sai Ammi tajuyo da kanta ahankali kawai tazuba mata idanu tai nisa a tunani, aka bude dakin dasauri Ammi tajuyo wata yar budurwa ce tana sanye da anko itama kana ganinsu kansu daya kuma kamanninsu kusan daya kawai Amirah zata nuna mata hasken fata ne ita wannan hasken ta kaman na Ammi ne, ta ijiye jakan makaranta tace Wayyoo Allah na Ammi ina wuni nagaji murmushi Ammi tayi tace andawo daga school Miemie, yaya test din dasauri tataho wajen gadon tace Ammi nayi kokari sosai tai maganan duka idanununta na kan Amirah da kanta ke cinyan Ammi tana kirga yatsun Ammi kaman batasan da mutane a dakin ba, Ammi takalli Amirah tace tashi toh ga Miemie tadawo daga school, Miemie zauna min da ita bari nakoma naduba abinci zan kawo miki shinkafa kema Dasauri Miemie tazauna kan gadon tana kallon Amirah tace yau bazaki kulani ba sabida ban kawo miki tsaraba bako Ammi tamusu dariya tace kunfi kusa Ammi tasa hannu tadagota ahankali tace zauna da yaruwanki bari naje nakawo muku abinci Ammi ta karbe hannunta tamike dasauri itama tamike, Ammi cikeda fada tanuna mata gado tace zauna anan nace ita Maryam din bakuwan kice, tun safe banda sukuni sabida ke sai bina kike kuma kinki yarda da kowa, abin naki harda yar uwanki yau, wuce ki zauna nace tunda Ammi tafara fada tasauke kanta kasa takai hannayenta tana sosa cinya duk saita bama Ammi da Maryam tausayi, Maryam da taji duk ba dadi dasauri ta taso takai hannu zata kamata dawani irin sauri ta matsa kusada Ammi, Ammi tace kyaleta kawai Miemie kinsanta hayaniya da jama a duk suna tada mata da hankali, yau rashin yardan hardake kuwuce muje Maryam tace kuma Ammi da bata ganki ba da nine zata mannemawa hakafa Ammi tace ai tunda tamiki halinta yau karki kara kawomata komi daga school Ammi tawuce tai gaba dasauri tabi Ammi kaman bindi Allah tasa kan akwai hula yanzu, Maryam ma tabisu tana kallon yanda simple gown din yama Amirah kyau na wuce misali, backyard Ammi tayi anan taga Maman Baby awajen da ake kwashe abinci a kula tahade giran sama da kasa Ammi ta taho wajen zata wuceta Maman Baby tace ki barshi kawai bana bukatar ki, Allah yasa inada wasu dazasu tsaya kan abinci jekiji da diyarki mara kai dasauri Rakiya tace mekuma yayi zafi Maman Baby kinsan yanda yara suke especially marasa lafiya kuma duk ita tahada abincin ai kafin takaita ciki Cikeda fada Maman Baby tace karki gayamin magana Rakiya, bakisan meke faruwa bane acikin gidan nan, bakin ciki take taga sa an diyarta yau tana aure ga tata diyar kai duka yaran nata ma babu manemi, daya ba kan gado kan ba dadi balle ma ayi maganan aure akanta, dayan kuma sai bakin rashin kunya Maryam ta tabe baki tana juya idanu, Maman Baby tace shine takeso mutane su zageni kar kowa yaci abincin tunda ba yarta ke aure ba ahankali Amirah takama bayan rigan Ammi tarike jikinta yadan fara rawa bawai tana kallon mutane bane but she understands everything that is happening around her, bataso taga ana fada da mamanta, dazaran an fara zakaga tarike ko hannu ko rigan Mamanta kanta akasa, Maman Baby tana kallon Ammi cikin idanu tace to bari kiji wlh sama taima yaro nisa saidai yadaga fuska ya kalleta nariga namiki fincinkau Zainabu, diyata na biyu kenan danake aurar wa kekuwa kije kifara ji da mahaukaciyar nan ita kadai tazamema rayuwarki azaba da ukuba tai maganan tana nuna Amirah, tunda ake hayaniyan nan babu abinda yabatama Ammi rai sai kalman karshe data fadi, takalli Maman Baby sosai kaman tabata amsa amman saita fasa sai kawai tasa hannu takama hannu takama Amirah dake jikinta, takalli Maryam dake huci tacika fam tace kuwuce muje ganin Maryam batai motsi ba Ammi tace Maryam nace muje zuciyanta ba dadi tajuya fuuuu, Maman Baby tadaga murya tace dakin barta ai tarama miki yanda tasaba, ahaka zaki kare keda uwarki, Zainabu kekuma nagaya miki aniyanki akanki zai kare gadai daya nan agabanki kina gani, ke kikasan uban me kikayi Allah yabaki ita mai juyayyen kwakwalwa mutanen wajen ne suka dinga bawa Maman Baby hakuri cus zagin yayi yawa sannna tai shiru. Kofan flat nasu Ammi tabude takalli Miemie dake huci strictly tace wuce ciki batai musuba tawuce ciki, Ammi tashigo da Amirah, duk an fita daga dakin, Ammi tawuce ta ita tazaunar da ita akan gado takalli Maryam dake tsaye tace zauna kema Miemie kaman jira take dasauri Maryam tace Ammi wai Matarchan who did she think s kul! Ammi tafadi ahankali hakan yasa Maryam tai shiru, idanunta na ciko da hawaye jikin Ammi yayi sanyi, ahankali tace idan baki fahimceni ba Miemie wanake dashi kuma eh? Ina zan sa raina? Ke koda zanyi fada ba abinda zaki hanani bane Maryama? Kalli yar uwanki ba lafiya, anzo neman aurenki, Babanki yace nan da wata uku, da shirya aurenki zanji koda ciwon yayarki eh Maryam? Do you think tsayawa nayi fada is wise? Ahankali tace Ammi ni bazanyi auren nabarku anan ba wlh wani kallo Ammi tamata tace ke bakida hankali ko kawai saita fashe da kuka sosai, ahankali for the first time tunda tadawo sai Amirah tadago kanta ta kalleta, ahankali Ammi ta taho wajen Amirah na binta abaya, Ammi taduka tana kamota tace Miemie mehaka? Meyayi zafi? Why are you crying like this? Miemie na menene ? Ammi tarungumeta cus Maryam hardly cries, cikin kuka da tsantsan zuciya tace sai ayita kiran yaruwata mahaukaciya, Ya Amirah ba mahaukaciya bace, yar uwata ba mahaukaciya bane, she doesn t hurt me, bata cutar da kowa, Ya Amirah is kind, Ammi she takes care of me, kullum idan zani school she cleans my shoe, da farko ma da rigan jikinta take gogemin saida na nunamata da tsumma akeyi, bantaba fada mata ta gogemin takalmi ba, idan ina assignment tana zama kusadani taita kallona idan nai bacci awajen zata kwashe all books din tasamin ajakan school, she watches me and studied kome nakeyi even though she hardly talks to me, Ammi yar uwana ba mahaukaciya bane kawai Allah ya hallice ta daban ne, Amirah ba bala i akanmu bane, my sister is special, and she s Allah s gift, I love my sister ni wlh da ita zan tafi gidan mijina idan Umar bazai yarda ba nafasa aurenshi ganin yanda take kuka yasa Ammi kawai tadinga lallashinta ta share shirmen datake fadi na zataje gidan mijina da Amirah, da mijin zataji koda Amirah? Hmm yaro yarone!. BACCIN SO
Chapter 3 · 0% Book details