Sashe 50
Baccin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ina kwana Baffa yace Amirori yaya an tashi ince anyi kari dai ? Ammi tace wannan tafi karaman Salma neman abinci da sassafiyan Allah komawa jikin Ammi zatayi Ammi tace jeki wajen Miemie tana daki kin tashi tayi Ammi tace maza nace ahankali ta mike rikeda wayan Ammi tajuyo tana kallonta saita wuce tafita tashiga Dakinsu duk Ammi na kallonta kafin Ammi tajuyo takalli Baffa, dayayi murmushi na manya yace Haleematu kinga dai bani kaunar halin Yusufa amman Allah yasani mijin daya aurama Amirah naga yaron kuma Allah ya dauramin kaunar sa da yarda dashi dan haka ni na yarda da auren nan dari bisa dari fatana Allah ya kyautata zamansu Wani kallon Baffa Ammi keyi, Baffa kuma ya gyadamata kai cikeda gamsuwa yace I know duka abinda kike tunani, kina tunanin Amirah batai girma da wayan dazatai rayuwa inda babu ke ba, now the question is yan kwanakin datayi a asibiti ai baki wajen ko? And she was fine, infact kalli improve Ada Amirah bazata taba barinki taje wani daki ke kina wani daki daban ba Lami tace kwarai! Baffa yace ki kwantar da hankalinki kibita da addu a karki rigima da mutumin chan Babansu ki barsa da halinsa, munyi concluding zasu tare rana daya da Miemie dan haka ki kama shirye shirye kinji Baffa yadan sauke murya yasan yanda takeson yarinyar Amirah saidai in baka zauna da itaba wlh saika sota, ahankali yace is time for Amirah to grow up a inda baki haka rayuwa yake, this is her next step na rayuwa, ki daure ki koyar da ita the little you can in this period, kibarma Allah komi, Allah na ganin komi Haleema, and Allah bazai baki kunya for all hakurin dakikay ba, in sha Allah Dr Marwan will take care of Amirahn mu da kyau and zata warke tass tass kinji gyadama Baffa kai tayi ahankali saita lumshe idanu saiga hawaye wlh wlh tana ma Amirah wani so da batason tarabu da ita ko kadan batason tarabu da baby girl dinta, Baffa yace laaaaaa Lami tai yar dariya tace kukan tunanin rabuwa da yar diyarta take Baffa yace tun yanzu, yau naga Maman Amarya mai kuka dan dariya sukayi, sai Ammi ta share fuskanta tass takalli Baffa da Lami tace ragowan kudin dana rage zanja jari bari kawai muyi amfani dashi nama Amirah kayan daki ko Baffa yace nima zan kara miki daga miliyan daya ta wajena dasauri Mami tace ah Baffa kabarshi suka cigaba da hira. Daga Bbaya Baffa yafice yaje kasuwa Ammi tawuce tashiga dakinsu Amirah na tare da Miemie tana kwance jikin Miemie suna kallo da wayan Ammi a YouTube dan Ammi nada data Miemie data dinta yakare amman anjima Umar zai samata, bama suji shigowan Ammi ba, Ammi tace ahh yayi kyau sharan kenan ko Miemie dasauri Miemie ta kalli Ammi Amirah ma haka saita taso daga jikin Miemie ahankali, Ammi tawuce bakin katifa ta zauna dasauri Amirah tazo wajenta Ammi zata mata magana kawai saita zauna ajikin Ammi tana kallon fuskanta sosai muryan nan chan ciki tace Ammi tsareta da idanu Ammi tayi tace menene kika haumin jiki kaman mage ? Yanda Ammi taga tana kallon kwayan idanunta yasa tagane Amirah harta gane tai kuka kafin abin yashiga ranta ya zauna ya tada mata da hankali saitai sauri tace gashi yafadamin ido, idanuna sunyi wani iri ne? Gyadamata kai Amirah tayi itama Miemie na zuwa wajen dasaurin ta. EPISODE 4 Cikeda hikima da dabara irin na Uwa Ammi tace huramin idanun Amirah Dasauri Amirah tadaura soft hannayenta akan fuskan Ammi saita hura mata iska a idanun, Ammi tai murmushi tace iyye yammatana ta iya fa kinga gashin yafita Miemie, Miemie tai dariya, sai Ammi tasa hannunta takama na Miemie tazaunar da ita gefenta tace zauna kiji Zama Miemie tayi duk suka kalli Ammi, Ammi tai murmushi tace mesa kika gayamin kinason Dr Marwan Amirah ? Wani kyalli idanun Amirah sukayi sabida Ammi tahanata maganan Dr Marwan tamata fada sosai ganin Ammi yau tamata tambayan akanshi wani sanyi taji saita kankame Ammi sosai Miemie tawani kwashe da dariya tace Ammi wlh da gaske Amirah son Dr nan takeyi jibi yanda take farin ciki sabida kin tambayeta, ohh su Ya Amirah anga fine Dr Ammi takalli Amirah yanda take murna tana wani blushing kyawawan hakoranta na nunawa tace ina jinki fadamin ahankali Ammi tai shiru tana kallon Ammi tana tuna duka abubuwan da Marwan yamata tace Dr Marwan nama Amirah kirki kaman Ammi Miemie tace wooooohhh! Ammi tai shiru harareta hakan yasa tai shiru Ammi ta kalli Miemie tace mesa kikace haka Safan kafanta tanunama Ammi ahankali yace yasama Amirah takalmi da safa, yaba Amirah chocolate, da abinci mai dadi, yahana Amirah kuka, Dr shima Ammi na ne Ammi Tunda Amirah ke maganganun Ammi ke kallonta batajin there sa single soul in this world as innocent as Amirah ba, nobody can understand abinda Amirah tafadi inba a mother ba, in the moment when she was scared tai feeling alone ba Ammi ba Miemie gardawa sun dauketa mutum daya saved her with a kind hearted spirit yabata exact kulawa irin wanda Ammin ta ketaba sai for the first time sai Ammi taji zuciyanta ya natsu da auren it might be a good thing afterall, cike da hikama Ammi tace na aura miki Dr Marwan ahankali Amirah dake wasa da yan flowers na gaban rigan Ammi ta tsaya ta kalli Ammi dasauri, Miemie ma haka, wani tsare Ammi Amirah tai da idanu kaman tasan menene aure, Ammi tace an daura auren ku jiya a masallaci karfe biyu sadakin ki na hannun Babanku, kema yanzu matar aure ce kaman Miemie rana daya za a kaiku gidan mazajen ku wani mamaki ne yakashe Miemie, wani kalan bugawa zuciyan Amirah keyi, ahankali tace Mama Lami matan Baffa ne, Maman Baby Matan Daddy ne, Miemie Matan Ya Umar ne, Amirah Matan Dr Marwan ne? Gyadamata kai Ammi tayi alamun eh, wani washe baki sai tawani kankame Ammi tahau kyalkyala dariya da karfi abinda basu tabaji Amirah tayi ba tawani kankame Ammi, Itama Miemie saitahau dariya tace laaa Ammi wlh Ya Amirah batada kunya, wai dadi fa takeji an mata aure ko Ammi kawai girgixa kai tayi irin na manya tana kallon yaran nata dake dariyan rashin hankali kawai tunani take yanda zata rabu dasu tai rayuwa ita kadai, dakewa tayi tace ku tsaya ban gama magana daku ba zonan Amirah Ammi tadagata daga jikinta wani murmushi takeyi sai Ammi taja kujera ta ijiye gabanta tace zauna anan zama tayi anatse, Ammi tace kinason auren? Dasauri ta gyadama Ammi kai, Ammi tace kinsan me akeyi a aure ? Dasauri tace zanci abinci nima na haifo katoton jariri Miemie tawani kwashe da dariya Amirah ta kalleta sai itama ta kwashe da dariya dan she s extremely happy, Ammi ta kwadama Miemie duka tace tashi ki fita wuce jeki daura sanwa mara kunya tashi Miemie tayi takalli Amirah tace Amaryan Dr Marwan Amirah tasake washe baki. Ammi na kallon ikon Allah saida Miemie tafita Ammi tace ki natsu ko kinaso raina ya bac Dasauri ta girgizama Ammi kai tana wani kalan cute smile dake melting zuciyan mutum, Ammi tace anayin abubuwa da yawa agidan miji, dagayau zan fara koya miki girki, da yanda ake gyara gida kinji gyadama Ammi kai tayi tace Ammi anjima mijina zaizo? Tsayawa Ammi tayi turus tana jin nauyin yanda Amirah tace mijina saita harareta tace ban sani ba Ammi tayi shiru tace kin tuna wankan tsarki dana koyamiki kinayi duk idan kin gama period dinki? Dasauri ta gyadama Ammi kai, magana Ammi zatayi saita kasa maganan yamata nauyi ita zata koyama Amirah bangaren nan? Saita kasa tace kome yafaru tsakaninki da mijinki karki fadama kowa kinji, sirri ne gyadama Ammi kai tayi, Ammi tace muje kiga yanda Miemie ke daura abinci a wuta Tunda suka koma gida yasami all yayyinsa baimason surutun su dan harsun fara ango ango ya hade fuska yawuce dakinsa, bayi ya shiga yayi wanka da kyau yafito pajamas ya saka saiya fito yazo ya kwanta akan gado yayi shiru saiya lumshe idanu 3weeks is so long yafadi murya chan kasa saiya bude idanu dasauri maisa yafadi maganan? Deep down jiyake kaman yabude idanu yaga Amirah, da akace an daura musu aure dudda he s trying to fight d feeling saiyaji sonta yawani karu yakara doubling a zuciyansa. EPISODE 5 2WEEKS! yau duka duka saura kwana 6 tarewa, bangaren Umar yagama gidansa tsaf dan ana maganan satin nan za aje ayi jere Ammi babu abinda batama Miemie ba masu kyau na gata kuma, ta zage gyara yaranta take ba kama hannun yaro, ga mai gyara su yan Maiduguri, kyan da Amirah da Miemie sukayi yabaci, Amirah jikinta kaman glass, cikinta ciwo yake sabida kayan matan da ake bata kaman yasoma ma jikinta yawa da kanta Ammi tafara ragewa cus taga kaman Amirah tamafi Miemie sensitive jiki and abu namata aiki ajiki sosai. Ammi babu abinda bata koya mata ba, gyaran gida, gyaran daki, girki, da yanda ake handling su gas, Ammi tayi iya kokarinta takoya mata intimacy takasa wani nauyi takeji, tagayama Lami tadan koya mata wani abu amman ina daga ita har Lami abu daya suke, sun kasa, gawani kamshi da Amirah keyi an gasa an huda jikinta da turaren shuwa Arab na Maiduguri, Amirah kullum saitayi maganan Dr Yaushe zaiso amman shiru babu wanda yasani, shirye shirye suke ba kama hannun yara, Umar yakawo ma Miemie dubu dari uku na dinkunan ta an kawo akwatinta yau wlh wlh yayi kokari, gobe da safe za aje mata jere zai aiko da mota. Bangaren su Mami suma shirye shirye suke bana wasa ba Abba ya ijiye kudi na ban mamaki hat chanza penti na gidan akeyi suma biki suke shiryawa meanwhile Mami tagama hada akwatin Amirah, Abba da kansa yakira su interior design ana sa komi agidan dayaba Marwan is like 2 houses tsakanin su, shida Mami suka yanke shawaran sAbida condition na Amirah plus Marwan na zuwa aiki gwara suma kusa dasu, kiri kiri Marwan yaki participating in anything, dudda azuciyansa yafi kowa duba calendar da date yawani irin ko a but kagansa he looks so uninterested saisa Abba ya tsaya tsayin daka kan lamarin gidan da interiors din. Yau wuraren 9 manya