← Book details Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 99 OF 137

Sashe 99

Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lokacin data shiga cikin gidan d'akin gwaggo ta nufa ta taras ta gama salla tana zaune kan darduma tana lazimi, cike da zumud'i ta nufeta ko sallama bata yi ba ta zauna agabanta bayan ta ajiye kayan a gefe, hannu ta kai ta cire gyalen kanta ta juya ma gwaggo k'eya yadda zata ga gashin sosae, shafa Addu'a ta fara yi kafin ta kai hannu ta shafi gashin da fara'a tace "inyee, Fatuuta ce ta zama yar India haka" juyowa tayi tana ta dariyar farinciki ta hau bata labarin yadda aka gyara gashin tiryan tirya,
"Yar kauye kawae" gwaggon ta fad'a bayan ta gama fad'i mata, ita dae sai faman tik'ar dariya take, hannu ta kai ta janyo ledar kayan ta fara curo wanda ya bata daga baya ta mik'a ma gwaggon tata "gashi nan yace in baki" jinjina kai tay ta ciro atamfar mai kyaun gaske tana ta Murmushi don al'amarin Haisam ya daina bata mamaki sai dae in yayi abu tayi godiya tasa mashi Albarka, fiddo na cikin d'ayar ledar Fatuu tayi wanda guda biyu ne daya mai Golden daya Normal Chiganvy irin ta cotonou mai laushin gaske itama ta gwaggon irin tace amman design ba daya ba, Fatuu na gani tace "lahh gwaggo wannan shigen irin tawa ce da aka kai dinki wllh, kinsan na waye?" girgiza mata kai tayi alamar a'a,
"Haulat yace in kai mawa ita da innarta fa" bud'a ido gwaggo tayi sai kuma ta shiga yin godiya, jawo sauran kayan dake acikin babbar ledar tayi anan kuma tai kacibus da yan bras dinta tana ganinsu tai saurin d'agowa ta kalli gwaggo suka had'a ido don ita take kallo tana jiran ganin abunda zata fiddo a ciki, ganin ta k'ame yasa gwaggon tambayarta "lafiya" shiru tayi tana ta d'age baki hadi da dan sosa kai, ganin taki cewa komae ne kuma ga alamun rashin gaskia atattare da ita yasa gwaggo ta kai hannu ta jawo ledar ta lek'a ciki, da mamaki ta d'ago ta kalleta "wannan kuma na waye?" ta tambaya yayin da ta kai hannu ta fiddo da bras d'in, mar mar ta fara yi da ido kaman zata yi kuka cikin in ina ta fara magana "W..wa..wai mai shagon da akai siyayyar ce tace ina bukatarta...." katseta gwaggo tayi "ita ya akai tasan kina buk'atar tatan?"

"Ai dayake shagon biyu ne,to da aka gama zabar lace da atamfar nawa sai Ya Handsome d'in yace mu shiga ciki a idasa daukko sauran abubuwa...." nan ta kwashe komae yadda Zee ta bata bras d'in ta fada mata, shiru gwaggo tayi had'i da sunkuyar da kai, tunani ta shiga yi dama can tayi tunanin yakamata ta siya mata bra din don irin breasts din nan masu nipples gareta koya tasa riga mara nauyi sai an gansu sosae, to ganin ba wani girma garesu bane yasa ta kyaleta don sam itama ba irin jikin ainihin yan Matan fulani ne da ita ba, su kansu breasts din nata da gani ba irin masu yin girman nan bane sosae wanda suke zubewa, jin gwaggon tayi shiru kuma ta duk'ar da kai ne yasa gabanta ya fara fad'uwa murya na rawa tace " Gwaggo in baki so dama nace mata zansa Ya Handsome ya kaini a maida mata su",
d'agowa tay ta kalleta, nannauyar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta fara magana " tunda ta baki taga ya dace ki rinka sawa ne, ki yi amfani dasu....,amman don Allah Fateema ki natsu kisan kin girma duk wani sakarci da wauta ki ajesu agefe, kada ki fara amfani dasu kice zaki bi mutane kina yamadidi kina nuna masu ko fadi masu, sam hakan bai dace ba don rashin kunya ne, ina son ki kama kanki mace da kunya aka santa ba kaman ke da kike bafullatana wadanda aka sani da tsananin kunya, idan naga kina rawar kai don kin fara saka su to kuwa tabbas zan hana ki amfani dasu ne, kinji ni da kyau?" da sauri ta d'aga mata kai alamar eh, duba sauran kayan tayi tasa albarka yayin da farinciki ya lullu6eta saidae sam bata bayyana a fuskarta ba dalilin Maganar da suka gama da Fatun, umarnin kai kayan d'aki ta bata bayan ta mik'e tace in an sha ruwa sai taje ta kaima su Haulatun tace ai ba azumi take yi ba bari taje yanzu ta kai masu gwaggon tace to ta fara yin salla ta amsa da to daga haka ta fice gwaggon ta bita da ido, girgiza kanta tayi lokaci guda kuma idonta suka ciko da kwalla don tunawa da yadda tai fama da Mahaifiyar Fatun kan saka bireziya sam bata so saboda tsananin kunya dake gareta sam ba halinsu d'aya da Fatuu ba duk da tasan dalilin dayasa wasu halayen nata take yinsu haka, d'aga hannu tayi ta shiga yi masu Addu'a gaba daya.

Tana gama yin sallar ta nufi gidansu Haulatun, lokacin da ta kai masu kayan Golden d'in tace ta haulatu ce dayar kuma ta innar tasu, Murna sosae sukai dama rannan Hajiyar Sanata ta aiko masu da turmi ukku su dinka harda kannanta kaman yadda ta saba yi duk salla tana rarraba atampopin salla ga marasa k'arfi, har tukuici Innar tasu taba Fatun amman tak'i amsa Haulat tace bayan sallar asham zata rakata tayi mashi godiya, labarin irin kayan da ya siya mata ta shiga ba haulatun amman abun mamaki sam bata yi mata zancen bras din ba da alama taji fad'an gwaggo, sosae haulat ta tayata murna tana ce mata ita yanzu ai tazama yar lelen Ya Handsome, sai la'asar Fatuu ta koma gida, da dare bayan an gama sallar asham tare suka iske shi a part d'inshi don sun duba part d'in Hajiya bai je can ba, karo na farko da Haulat ta shiga part d'inshi sosae ta jinjina had'uwar falon acikin ranta, yana kishingide akan kujera yana lallatsa waya suka iskeshi Haulat d'in na k'okarin duk'awa kan Carpet yace ta zauna kan kujera lokacin ita Fatuu tuni ta haye, sosae tayi mashi godiya yace mata ba wani abu daga haka Haulat ta mik'e tace ma Fatuu tazo su tafi, sanin dama da angama sallar yake rakata gida yasa ta mik'e suka mashi sai da safe tana ta fama yi mashi Murmushi harda yi mashi bye bye shima ya d'an d'aga mata hannu suka fice.

Washe gari ya rage saura kwana shidda salla da daddare bayan angama asham taje part d'in hajiya, lokacin da zata tafi ta bata wata babbar leda mai dauke da kaya tace ta kai ma Dije, cike da zumudi ta nufi gida don tasan bai wuce kayan sallar data saba yi masu, lokacin da ta isa gidan gwaggo na kan darduma a tsakar gidan bata dade da gama sallar asham din tata ba tana zaune ga haske ya haske tsakar gidan don tana cikin yin sallar aka maido da wuta, gabanta Fatuu ta nufa da sauri ta aje ledan tana fad'in "gashi Hajiya tace in kawo maki" saida ta shafa Addu'a sannan taja ledan ta bud'e, fiddo kayan ciki tayi gaba daya sannan ta fara daddaga su Fatuu na ganin hakan itama tasa hannu tana tayata d'agawar, d'inkakkun kaya ne d'aya Voile material ne bak'i mai d'auke da manyan fulawowi kala kala ya matukar yin kyau anyi dinkin doguwar riga wadda da gani ta fatuu ce gaban rigar sai sakin kyallin stones da akai ado dasu cikin flowers d'in Material yake, sauran kuma brown shadda ce aka dinka masu gaba daya, gwaggo riga da zani rigar umbrella ce tasha aiki sai ta Fatuu itama shaddar doguwar riga akai mata sai na kawu Amadu dogayen riga da wando ne akai mashi, dama ko sallar data wuce haka tay masu d'inkakkun kaya saidae wanccan karon atamfa tayo masu Amadu kuma yadi ne mai kyau kuma dama ko ba salla ba tana yi ma Fatuu d'inki lokaci zuwa lokaci, wata k'arar murna Fatun ta saki tana fad'in tafi kowa kayan salla wannan sallar gwaggo dai nata faman dariya, lissafi ta shiga yi Ya Handsome yayi mata kala hudu ga bakar doguwar rigar data aje kala biyar kenan sai ga biyu hajiya tayi mata bakwai kenan sai kuma baffanta da yazo ya kawo masu atamfofi ita da gwaggon anyi mata dinki kala biyu Amadu kuma ya kawu masa yadi mai kyau mai matsakaicin kudi dama ita gwaggo bata da niyyar yi mata d'inki wannan sallar tunda baffanta ya kawo mata kuma tasan hajiya dama zata yi mata ga kuma jallabiyar da ta aje, sam bata ma sa ran na Haisam ba iyaka dae ta siya mata gyale da takalma dasu sarka harda sabbin pants da undi da vest sai gashi kuma Haisam din shima ya siya mata, lallae da alama su Fatuu canjin wardrobe za'ai, cike da murna ta ruga waje ta fad'o ma Kawu Amadu suka dawo tare, sosae yay farinciki da ganin kayan, koda lokacin kwanciya yayi Fatuu tasa dukkan kayan tayi gabanta ahaka tai bacci..........

ALBISHIRUNKU MATAN AFRICA DA KEWAYE SHAHARARRAR MAISAIDA KAYAN MATAN NAN WADDA KUKAFI SANI DA MAMAN HAIDAR TANA YIMAKU ALBISHIR DA CEWA ZAKU IYA SAMUN KAYANTA ADUK INDA KUKE AFADIN NIGERIA DA NIJAR, KARKU MANTA MACE MAI GYARA BATA BORANCI💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃08040448621
Akwai zafafan kayan mata masu matukar kyau da arha cikin sauki zamu aika miki da kayanki cikin aminci da yardar Allah su isa har inda kike ba cuta ba cutarwa karku bari abaku labari.
Muna kawo kalolin ingantattun kaya kamar haka 💥💫💥💫👇👇👇👇
1-Maganin sanyi
2-Maganin gyaran nono
3-Maganin hips
4-Akwai gumba kala kala
5-Maganin matsi masu ciko da gaba ki koma kamar budurwa
6-Kalolin garirrika masu bawa mace ni'ima da jimawa ajiki yana aiki
7-Akwai tsumi sha yanxu magani yanzu
8-Akwai jigidar sirri kala kala
Sannan kuma muna dahuwa kamar haka 💥💫💥💫👇👇👇👇
1-dahuwar kaza
2-yan shila
3-ciccibi
Dadai sauran su.Abubuwa dayawa gaskiya bazasu lissafu bah saboda lokaci maiso ta bini PC don ganin Kalolin kayan da muke dasu 08040448621,
ALLAH YAYI MAKI KIMA DA DARAJA AMATSAYINKI NA MACE👰,KADA KI WOFINTAR DA KANKI A WURIN MIJI SABODA RASHIN GYARA KAI, BURIN MAMAN HAIDAR KO WACE MACE TA ZAMA TAURARUWA⭐YAR LELE AGUN MIJINTA😍 SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI🤝

*💖A SANADIN MAKWABTAKA💖*

_A heart touching story of Love and Destiny_ 💔

*Mallakin*
⬇️
*🌹ZAINAB LALUH*📲✍
_~(Oummu imam)~_
Chapter 99 · 0% Book details