Sashe 14
Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
cigaba da magana matashin yayi yana bin bayan Haisam d'in lokacin har ya kama k'ofar motar zai bud'e "Oga in maka kwatancen gidansu ne?" juyowa haisam yayi hannunshi d'aya rike da kofar ya bisa da ido sai da yadau yan seconds yace"Ina jinka" da sauri matashin ya fara magana harda gyara tsayuwa za'ai zuga"Yauwa Oga idan ka mik'e wannan hanyar da zaka bi,ka shiga ciki ina kasan gidan Hajiyar Sanata? Kai Haisam ya d'aga masa alamar "Ehh" ya cigaba"Yauwa to kafin ka kai gidanta ai kasan akwai wata yar kwana da ta raba gidanta da sauran gidajen 6arin tunda ita gidanta kaga tangameme ne yad'an shigo ciki kuma katangar gidanta akwai tsawo....,kowa ya tambaye shi wannan bayanin oho,ya cigaba "to ai gidansu ita waccan Aljanar yarinyar na nan daga shi sai wani sai ita kwanar akwae ma d'an kiyos a gaban gidan,In ma baka gane ba Oga da ka tambayi gidan DIJE ATTENDER,za'a nuna ma da yake awurin kakarta take kuma ita kakar aiki take a asibiti irin masu.....bai k'arasa ba Haisam ya dakatar dashi ta hanyar d'aga masa hannu yace "na gane" yana k'okarin juyawa matashin yace "ko nazo na raka ka ne Oga?"
"No Thanks" Haisam yace lokacin kuma ya shige cikin motar,da sauri matashin ya rufe masa kofar yana fad'in "Allah ya tsare Maigida,Sauka lapia maigida" yana d'aga masa hannu kai da gani kud'i yake son ya bashi,shi kam Haisam jan motar yayi yai gaba abunsa don ya fahimci d'an shaye shaye ne,
Rik'e kugu saurayin yayi a fili yace"Hakanan a banza na wahalar da kaina ma ashe wurin yi masa kwatance,ko yar asi bazai ban ba,mtsww.." yaja tsaki,kafin ya cigaba"ni har nasa ran zan samu na kayan harka,wasu mutanen dai sun cika mak'o wllh" daga haka ya juya saida ya harbi k'asa irin yaji haushin nan kana yai gaba yana ta wuwwurga k'afa shiga niga,Allah ya shirya.
Ko ta kan kwatancan da akai masa bai bi ba,straight gida ya nufa yana karya kwana Officer ya tashi don bud'e masa gate Haisam ya dakatar dashi ta hanyar yi masa horn,juyowa yayi ya nufo wurin motar a hankali ya d'an sauke glass d'in yace ma Officer d'in "I will park it here" daga haka ya maida glass din ya rufe sai daya dan d'auki mintuna kafin ya bud'e kofan ya fito hannunsa d'auke da laptop da charger dinta,Officer yace "You're Welcome Sir" "thanks" Haisam yace kafin ya shige ta k'aramar kofa direct part d'insa ya nufa.
Yana shiga palor ya cire takalmansa a gefe saman desk ya nufa ya aje laptop da charger din,ya wuce saman kujera L-shape ya zauna ya jinginar da bayansa had'i da d'age kansa yana facing sama da gani abunda ya faru yake tunani,don makamancin hakan had never happened to him,hasali shi yara ma tsoron sa suke ba abunda ke hadashi da su,shiyasa da yaga fatuu zata yi masa rashin kunya ya mare ta don tun a jiya ya fahimci bata da kunya,shi da har manya ma shakkarsa suke sai gashi yau Fatuu ta aikata masa wannan d'anyen aiki.
*💖ASANADIN MAKWABTAKA💖*
BY
OUMMU IMAM
*Free Page 12 &13
D'agowa yayi after some minutes yasa hannu gefensa ya d'auki wayarsa wadda ya aje lokacin da zai zauna Contacts ya shiga yayi searching wani suna Iro Mechanic yai dialing kira,bugu biyu aka d'aga speaker ya kunna ya aje wayar a hannun kujeran ya koma ya jingina daga d'ayan bangaren aka fara magana"Assalamu Alaikum" kafin Haisam ya amsa aka cigaba da magana "Allah ya taimaki babban Engineer" amsawa Haisam yayi da fad'in"Malam Iro ya aiki" on the other hand aka amsa "lafia lau wallahi ranka ya dad'e,barka da juma'a" haisam ya amsa"Barka dai,mota ce zaka zo ka d'auka tana nan na parker ta a waje",
Iro yace"toh yalla6ai badai matsala ta samu ba ko? d'an murmushin gefe yayi yace "Malam Iro ku da an nemeku ai kasan matsala ce ko" Iron yace"Hakane yalla6ai,to Allah yasa ba babban matsala bace," hannu haisam yasa ya dan shafi fuskan shi kafin yace"Eh,Widescreen din baya ne yayi damage,so it needs to be changed" Salati Iro ya saka yace"yalla6ai garin yaya,wacce ciki ta samu matsalan? Haisam daya fara k'osawa da maganar amsar k'arshen kawai ya bashi "406,in ka lissafa komae let me know" yana niyyar latse kiran da sauri Iro yace "to yalla6ai sai a sanar ma da Jami'an nan zanzo d'auka tunda kace tana a waje duk da sun san mutum sai....." Haisam ya katse shi da fadin"zan fad'a masu" daga haka ya katse wayan.
Mik'ewa yayi walking slowly ya nufi gaban desk ya dauki telephone yai dialing numbers sannan ya kara a kunne daga can bangaren daya kira aka d'auka"Security" shine abunda aka ce,shi kuma yace"Somebody will come and take the car I parked out there" daga can bangaren akace "His name sir?"
"Iro Mechanic" Haisam ya fad'a daga haka kuma ya kife kan Telephone d'in ya nufi bedroom d'insa,da alama bautar jikin zashi yi inji dai hajia.
Bai dade sosai ba ya fito, sanye da wani lallausan farin Voile ana hangen farar vest d'in ciki sai dai ba sosae ba anyi mashi dinkin Senator style,irin style d'innan wanda rigar ke tsayawa a rabin cinya sai dogon hannu wanda ake matse k'asanshi da link yasa links d'in silver da ratsin bak'i,kafafunsa na sanye da takalma plain half cover bak'ak'e masu kyaun gaske kai da gani kasan zasu yi tsada ga wata Hadaddiyar agogo silver,sai hula da ya sa itama bak'a sai dai bata rufe duka kan ba ana ganin gashin kansa daga gefe gefe haka ma na k'eyarsa ya turo,tana da d'an karamin kulu a tsakiyar ta,irin hular nan ce da ake cema Igbo cap amman da ganin jikin wannan mai tsada ce.
Part d'in hajia ya nufa tana zaune saman kujera one seater jikinta sanye da jalbab fara sol ga glasses mak'ale a idanuwanta ta d'an duk'a tana karatun Qur'ani wanda ke a saman table,da sallama ya shiga a kujerar kusa da ita ya zauna yad'an kwantar da kanshi yana sauraren k'ira'ar ta a cikin suratul kahf,bai jima da shiga ba ta kammala,d'aga hannuwa tayi tana Addu'a lokaci guda suka shafa ita da Haisam wanda ya d'ago yana kallon ta da murmushi a fuskarsa bud'e baki tayi zatayi magana... ya rigata da cewa "Na karanta a Office" gaba d'aya sukai daria tace "wato har kasan abunda zan tambaya kenan" yace "yeah" d'an ta6e baki tayi tace "ai kwadayin falalar nike maka shiyasa nike tambayar ko ka karantan" "I knew" yace, hajiya taci gaba"To ya wurin aikin,Amman kad'an jima baka dawo ba don har nayi tunanin ko acan zakai sallan juma'ar" shiru yayi ya koma ya d'an jingina yana tuna abunda Fatuu tayi mashi,hajiya ta lura da yadda yanayinsa ya canja da sauri tace"lafia dai ko?? d'agowa yayi ya kalleta yace "Yes,kawai motan ce ta samu matsala",
"Wace irin matsala kuma" Hajia ta tambaya da yar damuwa a fuskarta,shiru Haisam yayi baima san mizai ce mata ba,don shi kunya ma yake ji yace wai wata yarinya ta jefar masa mota har ta fasa glass,kuma yasan in har ya fad'i mata abunda ya faru tabbas bazata bari ba sai taje gidan su yarinyar ko ta aika a taho mata da iyayen yarinyar ma don Hajia tana da kirki amman akwae fad'a ba kamar kuma kan abunda ya shafi d'an lelenta Haisam tabbas bazata bari ba,duk da bawai don a biya ba,so bai ma son abun yazama wani big issue,don shi a tunaninsa yarinyar is Abnormal don abubuwan nata sun wuce hankali "Kayi shiru" hajia ta katse shi,d'agowa yayi da d'an murmushi yace"bafa wata babban matsala bace kawai it was faulty lokacin da zan dawo,amman nasamu na k'araso tana waje and I called Iro zai zo ya tafi da ita" sauke numfashi mai karfi hajia tayi don tayi tunanin ko had'ari yayi duk da ta ganshi lafia lau,tace"K'arfen nasara ba tabbas,duka yaushe Iron yazo yayi masu service da ka dawo" d'an ta6e baki Haisam yayi yace "ko kuma ba'a so na ara ba" wani irin kallo hajia tayi masa tace "Eh din,ai kaima kana da taka bama daya ba,karka k'ara daukar man tawa" gaba d'aya sukai daria a daidai lokacin kuma aka fara hud'ubar hausa bayan angama ta larabci a Masallacin gidan,da sauri Hajia ta mik'e tana fad'in kai yau dai mun taushe hannu wallahi,na dawo a gajiye bacci yai awon gaba dani....."ba kince yau ba zaki Aiki ba?" Haisam ya tambaya,"Eh wani abu ne ya taso dole naje, amman ba wani dad'ewa nayi ba don ko tafiya ban bar T.k yayi ba 11:30 muka dawo" ta k'arasa maganar lokacin har yayi gaba ita kuma ta fara kwala ma saude kira"Saude,Saude" fitowa Sauden tayi tana amsawa jikin ta sanye da dogowar hijab brown,hajia tace"Yauwa to mutafi" Saude ta juya tana gaida Haisam wanda ke k'okarin fucewa ya amsa ba tare daya juyo ba suma suka rufa masa baya.