← Book details Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 137

Sashe 73

Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yeah,You're right Zarah ni d'iyar kanwar babanshi ce", cike da mamaki Fatuu tace"wllh nama gane ki,Mamanku diyar Hajiya ce wadda ke lagos kuma Babanku Bature ne ko?" Fanan na dariya ta d'aga mata kai alamar eh,
"To ke yaushe zaki zo nan Katsina?" fatuu ta tambaye,
"Currently now am not in Nigeria,ina India ina karatu,sai dae watarana in nazo" zaro ido Fatuu tayi"India!yanzun nan da nike yin magana da ke kina India?"kai Fanan ta d'aga mata alamar eh,

"To mi kike karantawa anan d'in?",
"Medicine"ta bata amsa,
"had'a Magunguna kenan?",
"No,karatun likita kenan",cike da mamaki Fatuu ta ruk'e baki tace"kai ashe wai shine Medicine,shifa nike son in karanta amman bansan sunan karatun ba kenan,ni karatun Doctor kawai nike cewa",sosae Fanan d'in ke dariya jin shirmen Fatuu nan suka shiga yin hira sosae atsakaninsu da alama itama Fanan d'in bakinta asake yake har Fatuu na tambayarta wai tana zuwa wurin yan Film d'in suburbud'a dasu Sharukhan,tace mata a'a ai Karatu ne ya kawota amman dae wani lokacin suna ganin yan Film d'in in sunzo makarantarsu shooting ko akan hanya ko a Mall in sunje Shopping da dae sauran wurare kaman wurin shak'atawa haka,anan Fatuu ke ce mata wai in zata zo tayo mata tsarabar sari amman ba wanda ake nad'awa ba wannan kada ita zai rink'a yi irin masu wando take so irin wanda Roshni d'in Aman na cikin film d'in Shu'umin iko take so,nan Fanan d'in tace mata bata gane irinsu ba don ba kallon film d'in take ba,Fatuu tace mata in anayi a tauraruwa zatasa Ya Handsome ya d'auki hoton irinsu ya turo mata tace to,daga haka Fanan d'in tace mata zata tafi tutorial yanzu sai wani lokacin zasu sake gaisawa Fatuu ta amsa da toh,

"Beb where are u?" Fanan ta fad'a tana d'an kallon gefen Fatuu,Haisam na jin hakan yayi ma Fatuu alamar ta juyo mashi da Laptop d'in,kallonta yayi fuskarshi da Murmushi itama Murmushin take mashi tace"I will be offline now so u can have more time wit ur Funny Mom"lumshe ido yayi still da Murmushi akan fuskarshi slowly ya furta"Ok,Bye Sweethrt",
"Bye Beb"ta d'an ja Maganar daga karshe had'i da yin kiss daga haka ta sauka,waro ido Fatuu tayi tasa tafukan hannayenta duka biyun ta rufe baki alamar mamaki tana kallonshi,kallonta yayi,ganin abunda tayin yasashi cewa" What?"
cire tafukan tayi tana d'an murmushi tace"Nagane Budurwarka ce,amman shine kace man baka da Budurwa ko" ta k'arasa tana tura baki tana yi mashi wani kallo irin ya raina mata wayon nan,

Murmushi yayi yace"Who told u dat?" tana tura baki tace"ba gashi nan kace mata Sweethrt ba kuma tayi maka..." kasa k'arasa Maganar tayi tana guntse dariya,shiru yayi yana kallonta still da Murmushi afuskarshi,ita kuma sai faman guntse dariya take,

Sigh yayi"ai wannan duk wanda ka damu dashi who is important to u zaka iya ce mashi hakan ba sai wanda ake Soyayya dashi ba" daina yin dariyar tayi tace"da gaske?" gira ya d'aga mata"yeah,kaman Grandma d'inki da Uncle d'inki duk zaki iya ce masu hakan is normal",cike da mamaki tace"ashe ba dole sai wanda ake Soyayya ba?"kai ya d'aga mata kafin ya kuma cewa"Mutum mai kirki ma zaki iya ce mashi hakan,kaman wanda yayi maki wani abu kika ji dadi" zaro ido tayi "to kuma in Namiji ne kada yayi tunanin sonshi nike fa",hannu yasa ya shafi forehead dinshi"ai zaki ce ne yadda zai fahimta kaman kice,u're such a Sweethrt"dariya tayi tace"Ya Handsome u are such a Sweethrt" shima dariyar yayi har hakoransa suka bayyana ya furta"thanks,har kin gama fushin dani kenan" turo baki tayi"ai na kyaleka kaci gaba da cin abunda ka saba",

"Kin daina damuwa da Ulcer zai kamani na mutu kenan" d'an yamutsa fuska tayi"to ai tunda su ka saba dasu kilan kana koshi ko,kuma koma na matsa ma ba bari zakai ba" ta k'arasa da sigar shagwa6a,d'an ta6e baki yayi kafin ya kai hannu ya d'aukko sauran cake din da ya aje agefen Laptop,har yakai baki zai gutsira suka had'a ido hakan yasa ya dakata don baida sauranshi da zai bata,mik'a mata yayi ta kalli cake d'in ba tare data amsa ba hakan yasashi cewa"take"maimakon ta amsa d'in sai ta turo mashi baki tace"Nima bancin sauran wani",
waro ido yayi lokaci guda ya gane Magana ta gaya mashi,wato abunda ya fad'i mata rannan data bashi ice cream acikin motane itama ta gaya mashi yanzu,ganin yadda yake kallonta yasata fashewa da dariya tana rufe bakinta da hannunta,aikuwa baisan lokacin da ya dauki throw pillow dake a gefenshi ba ya jefa mata a fuskar,dukar da fuskar tayi tanata dariya kitsonta ya zuba yaraf akan kujeran,still yayi yanata Murmushi shima,can ta d'ago ta mik'a mashi hannu alamar ya bata,shiru yayi yana kallonta kaman bazai bata ba sai kuma ya mik'a mata ta amsa tace"thank u Sweethrt ya Handsome"dariya yayi ya d'an girgiza kai kawae ita kuma ta fara cin cake din,

"Mi yasa kike fitowa haka,where is ur headtie?" yayi mata tambayar had'i da dan kwantar da kanshi jikin kujeran,sai lokacin ta tuna da abunda ya kawo tan,baki cunkushe da cake tace"ba kawu Amadu bane ya biyo ni zai bugeni shiyasa ban koma na daukko kallabin ba",
"Mi kika yi mashi?" idasa cinye cake d'in tayi sannan ta fad'i mashi abunda ya had'a su,idonshi akanta yace"har yanzu kina rashin kunya ko Zarah!"ta6e baki tayi kaman zatayi kuka"to ya kasa yi mun kuma maimakon ya barni inji da abunda ya isheni sai yake ta man maganganu ni kuma naji haushi bansan lokacin dana fad'i mashi hakan ba wllh kaji na rantse,amman bazan k'ara ba" ta k'arasa maganar tana d'age baki had'i da jujjuya kai alamar nadama,still yai yana kallonta ya d'an 6ata fuska,ita kuma sai sussune kai take,

Sauke ajiyar zuciya yayi yace"Let me see d Assignment " aikuwa da sauri ta juya gefenta ta d'aukko littafin,mik'a masa tayi bayan ta bud'o daidai inda tambayar take,hannu yakai ya amshi book din,
"Wai wannan tambayar za'a fidda kuma ga amsar da yake so asamo nan a k'asa wai in batayi irinta ba to ba'ayi daidai ba",shiru yayi yana kallon Assignment d'in can k'asan mak'oshinshi ya furta" CALCULUS" janye littafin yayi ya kalleta da mamaki"Ajin ki nawa kika ce ma?" da sauri ta bashi amsa"Js 3 nike kuma ban dade dana shiga bama" d'an jinjina kai yayi ya k'ara d'aga littafin yana sake kallon question d'in,yasan lissafin sosae tun yana 100lvl yake yinshi,yana da wahala amman awurin wasu don shi lokacin yana degree d'insa na farko yana koya ma mutane shi sosae wadanda basu ganewa in akayi masu,yayi mamakin ganin tana js 3 an bata shi, dama a Senior Secondary take anayinshi a Further math ga wad'anda suke yin Subject d'in shima kuma wanda ake yi masun introduction ne ba'a nitsa masu can ciki don lissafi ne mai rikitarwa sosae gashi yana da yawa,

"Mi kika yi aka baki wannan Assignment d'in?" ya tambayeta fuska a d'aure,nan ta fara inda inda tana zaro ido ba abun tayi mashi karya ba don ta fahimci ya gane laifi tayi,
"Am asking u Zarah!" ya d'an yi mata tsawa aikuwa a rud'e ta fara kora mashi bayani bata 6oye mashi komai ba,tana gama fad'i mashin kwalla suka zubo mata sharrr,shiru yayi baice mata komae ba,a zahiri ta wani 6angaren tana da gaskiya yadda ya rikesu tsawon lokaci dole su gaji kuma dama lissafi in rana tayi ba kowa ke fahimta ba shiyasa mafi akasari aka fi sa period dinshi da safe,ko kuma ana dawowa break kaman yadda tashi take sai kuma ya had'e masu da double periods d'in malama dole ma su gaji ai,matsalan yadda Fatun tayi Maganar dole zaiga tayi mashi rashin kunya,

"Ke kad'ai ne ajin?" haisam ya tambayeta,girgiza mashi kai tayi idanunta sunyi rau rau,
"Ke kika fi kowa rashin kunya kenan", da sauri ta k'ara girgiza kan tace"a'a wllh nifa bada niyyar rashin kunya nayi Maganar ba,kawae gaskiya na fad'i mashi don ya sani"shiru yayi yana ta kallonta fuskarshi still a d'aure hakan yasa ta sunnar da kanta k'asa tana ajiyar zuciya,
Sigh yayi"as from today,i don't want u to dat again,ba ko ina mutum keda right na ya fad'i abu ba koda yana ganin yana da gaskiya hakan na iya zama ma mutum matsala like it happens to u now,ki koyi yin shiru understand?",
da sauri ta d'aga mashi kai"to ya Handsome wllh bazan k'ara ba",jinjina kai yayi yai shiru yana d'an tunanin yadda zai solving mata don lokacin Sallar la'asar ya riga yayi gashi sai dae ya hakuri da zuwa gym don ko zata fahimta sosae har ta yi bayani a aji sai an d'auki d'an lokaci,ana haka aka fara kiran sallar la'asar mik'ewa yayi tsaye yana gyara rigarshi Fatuu ta d'aga kai tana kallonshi,

"Zanje sallah sai na dawo zan nuna maki yadda yake",jin haka yasa lokaci guda ta saki Murmushi,hanyar Bedroom dinshi ya nufa yana shigewa ta hau yin murna tana bubbuga kujeran kaman sabon kamu, bayan wani lokaci ya fito lokacin ta natsu har ta kwanta ma asaman kujeran,tana ganinshi tayi saurin mik'ewa zaune yana zuwa zai wuce yace"ke bazaki sallan bane?"tana kallonshi tace" to ai banda Hijabi"
"Kije wurin Hajiya sai kisamu kiyi sallan inna gama zanzo nan" amsawa tayi tare da mik'ewa tabi bayanshi,

_________________

Lokacin data shiga parlon hajiyan ba kowa aciki hakan yasa ta nufi dakin Saude don tasan Hajiyan Salla take,da sallama ta shiga cikin dakin lokacin Sauden na niyyar tada salla,juyowa tayi ta kalli bakin kopan shigowan tana ganin fatuu ta saki Murmushi,
"Fateema ce"
"Eh Aunty Saude ina yini"
"Lafiya lou ya Makaranta an dawo ko",
" Eh,Don Allah hijabi zaki ban zanyi salla",amsa mata tayi da to ta nufi wardrobe din bango ta d'aukko mata wata wadda take tunanin bazata yi mata yawa ba sosae ta aje mata agefen Katifarta don fatun ta riga ta shige toilet.
Chapter 73 · 0% Book details