← Book details Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 97 OF 137

Sashe 97

Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yanzu kin gan abunda nike Magana ko, in kina sa bra din baza'a rinka ganinsu ba",
Fuska akwa6e Fatuu tace " to kuma gwaggota fa, kar ta bugeni in ta ganni dashi fa",
da sauri Zee tace "No bazata yi maki komae ba, kice mata mai shagon da aka kawoki ce tace kina bukatarta",
jinjina kai tay "to amman in bata yarda ba zansa Ya Handsome ya kawo ni in maido maki abunki" d'aga mata kai tayi alamar ta yarda daga haka ta shiga nuna mata yadda zata sa bra d'in har ta fahimta sannan tace taje ta gwada, tana shiga d'akin gwadawar Zee ta girgiza kai a fili ta furta "in kana sana'a kaga Mutane kala kala ( haka ma Rabiu Mai kayan marmari ya fada🤣),

" Aunty a wane karfe ne kika ce zan makala ma?" Fatuu ta tambaya da d'aga murya, d'an matsawa tayi yadda zata jita tayi mata bayani yadda zata sa tace in taji ta matseta ko ta mata yawa sai tai adjusting karshe ta tambayi ko ta gane, da sauri tace "Nagane karki shigo" dariya Maganar taba Zee ta girgiza kai kawae ta koma kan stool d'in data taso ta zauna can sai gata ta fito ta maida rigar sai faman kakkare kirjin take, mik'ewa Zee tayi ta nufota tace ta cire hannun don taga intayi mata, da farko k'iyawa tayi saida tace mata to ba kina da riga ba sannan ta cire hannun, dubawa tayi taga tayi mata das ta kuma tambayeta lafiya lau breasts d'in sun zauna aciki batayi mata yawa ba, cike da jin kunya ta d'aga mata kai hakan yasa ta kamo hannunta ta sake kaita gaban mirror ta nuna mata yadda yanzu ba'a ganin nipples d'in nata ita dae dan Murmushi tay don duk jinta take wani iri ta takura, umarnin taje ta cire kayan tayi mata, bayan ta curo harda bra d'in ta saka jallabiyarta ta kawo mata kayan duk aka zuba su acikin k'atuwar leda, wata bra d'in Zee ta k'aro mata tace ta saka ta hannunta aciki don dama tana ahannunta ta dunkuleta, k'in sakawa tayi saima ta d'aukko d'ayar da aka saka tace wai bata so Ya Handsome ya gani, Zee tace to ai inta ruk'e a hannune zai ma fi gani sai kawai ta cusa su can cikin hammata ta mak'alesu, ba yadda Zee bata yi ba akan ta kawo a saka acan k'asan kayan amman tak'i wai ai zai iya duba kayan kuma ya ganta, k'arshe dole ta kyaleta suka fito d'ayan shagon,

"Allah ya yi mun gama" Zee ta fad'a yayin da ta tunkaro Haisam da Murmushi, d'ago kai yay ya kallesu fuskarshi a sake, agabanshi ta aje kayan tana kokarin bud'a mashi ya dakatar da ita ta hanyar mik'o mata card yace ta cire kud'in kawae, saman wani d'an table dake d'auke da littafi da wasu yan takardu ta d'aukko Pos machine tasa card d'in, tana kokarin mik'o mashi don yasa pin kawae sai taji ya fad'i mata
Pin d'in yace ta k'ara 20k sama tasha ruwa har saida ta d'an ware ido kafin tayi mashi godiya, Fatuu kuwa sakin baki tayi tana kallon yadda take fidda kudin ga kuma mamakin ance ta k'ara har dubu ashirin duk uban cinikin da akayi mata, tana sake da baki har bata san lokacin da bra guda ta fad'o ba, jin abu ya sauka kusa da kafarshi ne yasashi kai idonshi kasa ya d'an janye kafar kawae sai ga yar bireziya ta fito daga kasan rigar Fatun, kauda kanshi kawae yay ba tare da yace komae ba ita kam bata ma san abunda ke faruwa ba, kaman ance Zee ta kalli k'asan taga bra d'in yashe k'asan tiles bud'a ido tai ta kalli fatun suka had'a idanu, da kai tai mata alamar ta kalli k'asa hakan yasa tai saurin duk'ar da kai, ai koda tay arba da yar bra dinta sai ta wani zabura ta kwalalo ido ta d'ago tana kallon Zee dake yar dariya ta d'an rufe bakinta, juyawa tay ta kalli Haisam dake still azaune ta k'ura mashi ido duk ta sha jinin jikinta sai zare ido take, a hankali ya d'ago ya kalleta suka had'a idanu aikuwa a rude ta ida sakin d'ayar bra d'in ta nufi hanyar fita da gudu.........

ALBISHIRUNKU MATAN AFRICA DA KEWAYE SHAHARARRAR MAISAIDA KAYAN MATAN NAN WADDA KUKAFI SANI DA MAMAN HAIDAR TANA YIMAKU ALBISHIR DA CEWA ZAKU IYA SAMUN KAYANTA ADUK INDA KUKE AFADIN NIGERIA DA NIJAR, KARKU MANTA MACE MAI GYARA BATA BORANCI💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃08040448621
Akwai zafafan kayan mata masu matukar kyau da arha cikin sauki zamu aika miki da kayanki cikin aminci da yardar Allah su isa har inda kike ba cuta ba cutarwa karku bari abaku labari.
Muna kawo kalolin ingantattun kaya kamar haka 💥💫💥💫👇👇👇👇
1-Maganin sanyi
2-Maganin gyaran nono
3-Maganin hips
4-Akwai gumba kala kala
5-Maganin matsi masu ciko da gaba ki koma kamar budurwa
6-Kalolin garirrika masu bawa mace ni'ima da jimawa ajiki yana aiki
7-Akwai tsumi sha yanxu magani yanzu
8-Akwai jigidar sirri kala kala
Sannan kuma muna dahuwa kamar haka 💥💫💥💫👇👇👇👇
1-dahuwar kaza
2-yan shila
3-ciccibi
Dadai sauran su.Abubuwa dayawa gaskiya bazasu lissafu bah saboda lokaci maiso ta bini PC don ganin Kalolin kayan da muke dasu 08040448621,
ALLAH YAYI MAKI KIMA DA DARAJA AMATSAYINKI NA MACE👰,KADA KI WOFINTAR DA KANKI A WURIN MIJI SABODA RASHIN GYARA KAI, BURIN MAMAN HAIDAR KO WACE MACE TA ZAMA TAURARUWA⭐YAR LELE AGUN MIJINTA😍 SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI🤝

*💖A SANADIN MAKWABTAKA💖*

_A heart touching story of Love and Destiny_ 💔

*Mallakin*
⬇️
*🌹ZAINAB LALUH*📲✍
_~(Oummu imam)~_

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

5️⃣9️⃣

.......Bayan ta gama fitar da kud'in har ya mik'e sai kuma yace yana son atampopi guda ukku, Zee ta tambayeshi kaman wane kala yay mata bayani ta d'aukko mashi, sunyi kyau sosae tasaka mashi biyu a leda daban sai d'aya ma a leda daban kaman yadda ya buk'ata, bayan ya k'ara bata card d'in ta fitar da kudinsu atare suka fito daga cikin shagon yana ruk'e da babbar leda guda ita kuma ta ruko mashi guda saida ma tace ya bari Esther ta kai mashi yace ba wani abu, suna fitowa bakin shagon yace ta bashi d'ayar ledar ta koma, duk yadda taso ta kai mashi yace ta barshi kawae, sallama sukai tana tayi mashi godiya har tana cewa ya isar da sak'on sallamarta ga Zarah yace Ok, lokacin da ya iso bakin Motar back door ya bud'e ya saka ledojin kafin ya rufe, d'aga kanshi yay yana d'an kallon wurin da alama Fatuu yake nema, ganin bai ganta bane yasashi tunanin k'ilan ta shige cikin Motar, zagayawa yay da nufin shiga ciki kawae sai ganinta yay a duk'e jikin Motar, tana jin motsinshi ta d'ago suka had'a ido aikuwa da sauri ta sunkuyar da kan tana turo baki, d'an ta6e baki yay ya bud'e Motar zai shiga ganin bata tashi bane yasashi dakatawa yace mata "kina son in take ki ne?" jin hakan yasata mik'ewa sumi sumi ta zagaya d'ayan side d'in maimakon ta bud'e kopar ta shiga sai kawae tai tsaye a bakinta, ganin bata shigo ba bayan ya shigan yasashi sauke glass d'in kopar gefen nashi da d'an d'aga murya kad'an yace "zan fa barki a wurin",
jin hakan yasa takai hannu a hankali ta bud'e kopar ta shiga tana ta sussunar da kai takai hannu ta rufe kopar, tashin Motar yay suka bar cikin Plaza d'in, tunda suka hau hanya batace uffan ba a hankali take satar kallonshi yanata driving idanunshi akan hanya, jin shirun nata yay yawa yasashi d'an juyawa ya kalleta daidai itama ta saci kallonshi suka had'a ido, kasa janye idanun nata tayi tana ta yamutsa fuska kaman zatayi kuka hakan yasashi d'an sakin Murmushi aikuwa kaman tana jira ta fara fad'in "Wllh Allah bani na d'auka ba fa, itace ta bani tace wai ina bukatarta kuma saida nace mata ni bani sawa amman ta matsa in d'auka kuma dama nace mata in gwaggota ta hana zaka kawo ni in maido mata kayanta" d'age gira yay kafin ya juya ya kalleta itama lokacin kallonshin take yadda ta wani kwa6e fuska ne yasashi sakin kayatacciyar dariyar dake Matuk'ar k'ara mashi kyau ba kamar daya kasance hakoranshi na gefe gefe sun d'an yi tsini daga k'asa, tana ganin dariyar da yake kawae sai ta fashe da kuka ta fara rantsuwar Allah ba ita tace tana so ba, ganin da gaske ta tashi hankalinta ne yasashi daina yin dariyar Calmly ya kirata "Zaraah" amsa mashi tai "uhhuym" cikin muryar kuka ba tare data kalleshi,
"Is Okey, ai ba wani abu bane taga kina bukatan ne dat's why ta baki",
Wani kallo tayi mashi baki kumbure kaman zata kai mashi bugu, d'an juyawa yay ya kalleta suna had'a ido sai kawae gani tai yayi mata Murmushi aikuwa sai ta k'ara kware baki tana fad'in " ni wllh ba yar iska bace bani nace ta bani ba ko"

"Who said dat? Kinji na fad'i hakan ne?"
Cikin muryar kuka tace "ba gashi nan kanata min dariya ba"
"Owk, na bari calm ur mind" d'agowa tay don da ta d'age kafafunta sama ta cusa kanta ne,
" isn't something to worry ur self about, kin reaching stage na amfani dashi ne so ba wani abu bane ai"
"To ai na baro su kuma" ta fad'a da disashshiyar murya, juyowa yay ya kalleta fuskarshi sake kaman zaiyi Murmushi aikuwa sai ta fara yayyarfa hannuwa tana fadin "ni ka daina man dariya to" daure fuska yay yace "kinga yanzu na maki wannan ne?" kallonshi tayi ganin fuskar a daure yasata girgiza mashi kai alamar a'a, maida idonshi yay kan hanya yaci gaba da driving,
"Ya Handsome to mu koma a daukko kar muyi nisa" ta fad'a a d'arare, shiru yai kaman bazai ce komae ba sai kuma ya daga ido ya kalleta ta cikin mirror suka hada ido,
"an saka maki a kayanki " taji ya fad'a wai kuma sai ta sunkuyar da kai alamar kunya, d'an Murmushin gefen baki yay ya dan girgiza kanshi yaci gaba da driving dinshi ba tare daya k'ara ko kallonta ba itama bata k'ara cewa komae ba.
Chapter 97 · 0% Book details