← Book details Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 137

Sashe 51

Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"To tashi kiyi sallah sai ki dafan"da sauri ta mike jelar kitson da gwaggo ta fara yi mata nata reto agaban kanta ta saukko har wurin kirjinta.

Bayan sun gama Sallan a gefen kitchen ta fiddo Gas d'in ta fara dahuwar taliyan gwaggo dake zaune kan tabarma tana nuna mata yadda zata sa abubuwan,lokacin da ruwan ya tafaso gwaggo tace ta d'aukko taliyar a kicin,ta dibar mata wadda zata dafa,fatuu tace"ki k'ara Gwaggo zan kaima Hajiya" ba musu tace toh,sai dae acan kasan zuciyarta ba hajiyan zata kaimawa ba Haisam zata kaimawa,Tashin Sense,Mutumin da Hadaddan Abinci ma bai dameshi ba,shine za'a kaima Taliya mai daddawa,Haisam yaga ta kanshi😂,

"Wai nikam ko kin daina rashin ji ne Fatuu? Kwana biyu ba wanda ya kawo man k'ararki inata mamaki wllh", gwaggo dake zaune tayi maganar,
Wata yar Isakar Dariya Fatun tayi"Na daina kakus,ance man indae inason in Zama Doctor to sai ma Natsu,don ko inada Kokari indae banda Natsuwa to bazan zama ba",
"waye ya fad'a maki hakan" Fatuu tace"Yaya Handsome na gidan Hajiya",jinjina kai gwaggo tayi"Har shima yasan halinki kenan,ai ni da ina fad'i maki hakan shashasha kika mayar dani shiyasa kika ki daukar maganata...."katseta Fatuu tayi"ai shi mai ilimi ne yasan yanda Abun yake"hannu gwaggo tasa ta ruke baki"ni kuma Jahila ce ko shiyasa baki yarda da maganata ba kenan",

Fatuu dake Dariya tace"to kice Continent sai in yarda ke mai ilimi ce",Juyawa gwaggo tayi gefenta ta rarumo takalmi ta jefo mata,da gudu Fatuu ta fad'a cikin kicin sauran kad'an ta ham6arar da Tunkuyar Taliyan🤣.

*💖A SANADIN MAKWABTAKA💖*
_*(Love and Destiny)*_

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/D2Y0l2ZoRx8FLdjdi2Te0F

_*BY ZAINAB LALUH📲*_

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

*39⃣*

Ta cikin Kitchen d'in ta lek'o da kanta,kitson da gwaggo tayi mata gefe da gefe nata reto"Gwaggo Don Allah kiyi hakuri,Wllh ni bance ke Jahila ba ce,ai nasan kwanaki kinje Makarantar yaki da jahilci kuma har d'an turanci kina ji",banza gwaggo tayi mata tana cigaba da Sauraron Radion wayarta da ta kunna,

"Pls Sorry Kakus"Fatuu ta fad'a,
d'aga kai gwaggo tayi tana kallon kanta da ta leko dashi,dan ta6e baki tayi,tasan in ba tanka mata tayi ba haka zatai ta mata surutu,
"bazaki fito ki duba girkin ba sai ta dafe"jin haka yasa Fatun fitowa daga cikin kicin d'in don ta fahimci gwaggon batayi Fushi ba.

*** *** *** ***

Hajiya zaune ita da Haisam a parlor kaman yadda suka saba bayan isha,
"Tahir ya turo man sako yace naki ne" kallonshi hajiyar tayi"Waye Tahir kuma?wane sako?"
"Matsalar kin tsufa da yawa baki gane mutane,Tahir na gidan Mota Kaduna", Dariya Hajiya tasa"Allah Sarki wai Wannan Yaron tahir,rabona dashi tunda ya kawo man waccan 406 d'in kuma mun kwana biyu bamu gaisa ba, kasan Mutane yanzu sunfi gane ma tarkacen chatting d'innan ni kuma ido ba wani isasshen lafiya ba,ban iya inta k'ura ma waya ido shiyasa ba son yin shi nike ba,Miya ce ne?",
"Yace sunyi magana da Dad akan Mota da za'a kawo maki shine ya turo pictures ki Za6a" Yamutsa Fuska Hajiya tayi"Ali ho,ni bansan mike damunshi ba wllh",

Sai lokacin Haisam ya d'ago idanunsa daga kan Wayar dake hannunsa yace"Mi kuma Dad d'in yayi?",
"To wai daga Munyi magana yake tambayana cikin Motoci ba mai Matsala,shine na fad'i masa game da Waccan Vibe d'in da ta lalace yace za'a zo a d'auka,ni ai nayi tunanin gyarota Za'ai kawae Amman shine zai wani ce a turo hotuna in zaba",

Haisam dake d'an kishingid'e ya d'an ta6e baki"Shine har yayi laifi,ke da ba'a maki gwaninta...."da sauri hajiya ta katseshi "To mai Uba kaji nace yayi man Laifi ne,Kawae dai kamata yayi a gyaro Wanccan d'in,ba sai an wani sake ba,Duk ma ga Matoci nan a Gidan,kai kanka akwae biyu naka da kazo dasu ga d'ayar tawa,Sannan acan GRA ma akwae Motoci,to duk miye na sai an Kawo Watan,"

"Ba ruwanki da nawa kowa yayi Amfani da nashi,Kuma na Gra da kike Magana ai Dad yasa Manager d'inshi na nan garin ya kwashe su Saboda anata ajesu ba'a Amfani dasu, in Buk'atar amfani dasu ya tashi zasu yi replacing wanda suka d'aukan,tunda dae so yake a canja maki kawae ki za6a,already i ave selected it for u",

Hajiya dake kallonshi tace"Wacce ka za6ar man?", bai bata amsa ba sai mik'ewa da yayi ya koma kusa da ita ya zauna yana nuna mata pic d'in Motar da ya za6a matan,
"Kai Masha Allah tayi kyau wllh,kuma gata itama yanayin Vibe din gareta inason Mota haka,kamar jeep ce ma ko,Ya sunanta ne,ince dae bata da tsada ko?"

Kwantar da kanshi yayi ajikin kujeran ya d'an zamo"Rav 4,jeep ce,bata da wani kudi sosae just 12 million take..."tun kafin ya k'arasa Hajiya ta waro idanu hannunta d'aya ruke da ha6arta"Million sha biyun ne ba tsada don baka tsoron Allah Haisam,haka kurum jama kai Surutu,aji dadin cewa kudin talakawa yake sata yana kashe man tsofaitsofai dani ko,su Mutane da basa raina abun magana",
"Ina ruwanki da Mutane,let dem say what they want,tunda Allah ya baki iko sai ki denying kanki abunda kike so",
ta6e baki hajiya tayi tace"Uhm surutun Mutane ai abun tsorone haisam,in dae akwae wata wadda bata kai wannan kudi ba in gani",

"Yeah Akwae wasu,ga wata sunanta Venza" yayi maganar yana nuna mata hoton Motar,Hajiya tace"Oh,kaji sunayen Mota iri iri,kuma masha Allah itama ba dae kyau ba,to ita bata kai waccan ba dae ko?"
"Yeah,bata kaita ba,ita 10m take...",
da sauri hajiya ta katseshi tana d'an harararshi "yo miye marabarsu,ni nayi zaton Banzar ce ashe ta kirki ce,kaga nifa banson wadda takai miliyan goma gaskia,in dae akwae na k'asa da hakan to sai in za6a,amman bazan za6i wad'annan ba,ita waccan d'ayan taka d'in nawa take ne?"

"Mercedes kike magana,55m take",Wata Uwar harara Hajiya ta wurga mashi"da Allah ni ba ita nike magana ba,yo ni miya rage man yanzu a Rayuwar da zan rinka hawa Motar Miliyan hamsin harda biyar,d'ayar nike Nufi navy blue dinnan"
Sigh yayi"Corolla S kike nufi,bai da wani tsada 6m yake..."da sauri ta tari numfashinshi"Yauwa to kaga kamar itan ko wadda ma bata kaita ba yar 5 zuwa 4m" Still yayi ya d'an dage gira yana kallonta,
"Kayi man shiru,bakaji mi nace bane?"

Gyara zama ya danyi"Rav 4 da na za6a maki shi za'a kawo period,dama na sanar dake ne don kisan za'a kawo,kina son abu sai ki hana kanki saboda wani Mutane"
A harzuk'e Hajiya tace"To tunda nace banso ba sai akawo man irin wadda nike son ba",banza yayi mata saima latsa wayarshi da ya fara,dama tasan tunda har ta nuna Motar tayi mata to fa sai yasa an kawo ta,
a k'ule tayi kwafa"To wllh da an kawota bada waccan 406 d'in zanyi",d'age gira yayi ba tare da ya kalleta ba yace"as u wish" tana niyyar bud'e baki ta sake yi mashi Magana Muryar Fatuu ta katse mata
hanzari"Assalamu Alaikum,ga bak'uwa daga Makka",

Juyawa hajiya tayi ta kalli entry d'in adai dai lokacin Fatuu ta sake maimaita abunda ta fad'a,d'an girgiza kai Hajiya tayi tace shiryayya kafin ta amsa"Wa'alaikumus Salam Maraba da Mutan Makka ku shigo",shigowa tayi tana Dariya hannunta ruke da yar madaidaiciyar warmer ta yafo d'an bakin gyalenta na gado,da Hijabi ta fito ganin gwaggo zaune a tsakan gida,tana zuwa zaure ta cireta ta sagale ajikin windon Amadu kaman yadda ta saba yi daman ta 6oyo gyalen shine ta yafa kafin ta fito,
Tana shiga haisam ya koma inda yake zaune da farko,hakan yasa ta nufi gefen hajiyan ta zauna tana dariya"Hajiyan Sanata ina wuni",
"Lafiya lou fateema,yau Allah yayi kenan an kitse kan nan",

"Ai ba duka akayi ba iya biyun nan ne,tace sai gobe da yamma tunda ba islamiyya zata k'arasa man sauran",
Jinjina kai hajiya tayi kafin tace"wani abun arzikin nasamu da daren nan" tayi maganar idonta akan kulan da fatuu tazo da ita,janye kulan fatuu tayi gefe"Ba naki bane,Yaya handsome na kawo mawa,naje part dinshi naga bai nan shine na kawo masa nan",
Hannu Hajiya tasa ta ruke baki alamar mamaki tace"iyee, yanzu Fatima ni zaki gwasale,duka yaushe kika san haisam d'in da zaki man tawaye,lalle Nagode da wannan babban dizgin da kika man,amman zamu had'u ne",langa6ar da kae tayi tana ma hajiyan dariya kafin ta mik'e tana niyyar nufar inda haisam d'in yake,kwafa hajiyan tayi tana jinjina kai,ganin dae da gaske haisam d'in ta kawo mawa yasa Hajiya juyawa side d'in kitchen ta fara kwalama Saude kira"Saude,Saude lek'o ki tayani Jimami,yau ni Fateema ta wulak'anta",fitowa Sauden tayi ta tsaya bakin kopar kicin d'in hajiya ta shiga fad'i mata abunda fatuu tayi mata,Dariya ta fara yi daga inda take tsaye,

A gabanshi ta tsaya tana ta Murmushi,shima kallonta yake don duk draman da suke da Hajiyan yana sauraransu,hannu tasa tana d'an kange bakinta"kai na kawo mawa Yaya Handsome"ta fad'a da alamun kunya,kai ya d'aga mata,hakan yasa ta d'aura warmer d'in kan hannun kujera ta kinkimo sofa table kafin ta d'auko kulan ta d'aura,Hajiya dae nata bin ta da ido haka Saude ma har lokacin tana a bakin kicin sai faman Murmushi take,

A hankali Fatuu tasa hannu ta fara k'okarin bud'e kulan,k'amshin daddawa ne ya kaima hancin haisam karo bayan
ta bud'e,da Sauri ya juyar da fuskarshi gefe had'i da runtse Idanuwanshi,waro ido Fatuu tayi ganin abunda yayi,

"Miya faru ne naga Wanda aka kawo mawan ya kauda kai hada rufe idanu??" hajiya ce tayi tambayar,a sanyaye fatuu ta juya ta kalleta"nima ban sani ba,dana bud'e ne sai naga yayi haka",
"Miye kika kawo masa ne?"
Fatuu tace"Taliyan hausa ce mai daddawa",bud'e idanu hajiya tayi hannunta ruk'e da ha6arta"ai baya son daddawa Fateema,kamshinta tada mashi Zuciya yake yi shiyasa bai cin duk wani abu da akayi da ita",
Damm gaban fatun ya buga,juyawa tayi ta kalleshi,ya bud'e idanun sai dai kwata kwata bai kalli bangaren da take ba idanunsa na akan TV,jikinta ba k'aramin Sanyi yayi ba,a hankali tasa hannu ta d'auki kulan,juyawa tayi ta kalli hajiya dake kallonta fuskarta d'auke da Murmushi,a hankali ta nufi wurinta,agabanta ta tsaya ta mik'a mata kulan"gashi to Hajiya ki ci" fuskarta a yamutse tayi maganar,
Chapter 51 · 0% Book details