← Book details Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 137

Sashe 52

Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dan ta6e baki tayi"saida shi bazai ci ba sannan zaki kawo man,wato ni ga kwad'ayayya ko,to nima bazan ci ba...."fuskarta kaman zatayi kuka ta katse Hajiyan"Don Allah kiyi hakuri ki ci",
"Uhm dama kin daina Wahalar da kanki Fateema bafa zanci ba,har ni zaki ma Wulakanci,wato ke mai Yaya ko,to tunda ba zai ci ba sai ki koma dashi kawae" ba alamun wasa a fuskarta tayi maganar,ganin haka yasa Fatuu d'aga kai ta kalli Saude da har lokacin take tsaye a bakin kicin ta dan d'aga murya"Aunty Saude in kawo maki zaki ci?" kafin Sauden ta bata amsa Hajiya ta amshe"bazata ci ba itama tunda tun farko bamu kika kawo mawa ba,saida aka gwasale ki shine zaki mana neman kai da ita,to ba wanda zai ci"maido kallonta tayi kan hajiya da tayi maganar ganin ba alamun wasa a fuskarta yasa ta fara ta6e baki alamar zata fara yin kuka,ganin haka yasa Hajiyar juyar da kanta gefe alamar ko a jikinta,a hankali ta juya ta nufi hanyar fita idanunta cike tabb da kwalla,sharr kwallan ta fara zubowa,gefen gyalenta tasa tana gogewa yayin da hannunta guda ke rungume da kulan taliyan,

"ZARAH....",Haisam ne ya d'an d'aga Murya ya kirata,a hankali ta waiwaya ta kalleshi,alamar tazo yayi mata da kanshi hakan yasa ta koma cikin parlon tana yi tana goge kwallan dake zubo mata,A gabanshi ta tsaya kanta na kallon k'asa,
"Keep it" yayi Maganar yana nuna Sofa table,a hankali ta d'aura kulan saman table d'in kaman yadda yace,d'agowa tayi bayan ta aje ta saci kallonsa,shima ita yake kallo saidai bazaka iya gane tak'amaimai yanayin fuskarsa ba,
"Go and bring plate with fork" gently yayi maganar,da alamun mamaki ta idasa d'agowa tana kallonsa hakan yasa ya d'an lumshe idanunsa alamar eh,da sauri ta juya don daukko Plate da cokali mai yatsu,suna had'a idanu da Hajiya ta wani sha kunu ta nufi hanyar kicin,hakan ba k'aramin dariya yaba hajiyan ba,tana shiga kicin d'in Saude ta mik'o mata abunda taje d'aukan kallon Sauden tayi fuskarta ba yabo ba fallasa ta kar6a,daga haka ta juya ta fuce,

Ba k'aramin daurewa Haisam yayi ba lokacin da ta bud'e kulan zata fara zuba mashi, don ma ba sosae aka cika daddawan ba sannan ga k'amshin Curry da aka sa hakan ya rage mata kaifi sosae,tana zuba kamar cokali biyar ya dakatar da ita alamar ta isa,maida marfin kulan tayi ta rufe ta d'an ja gefe ta tsaya,Slowly ya kai hannu kan fork din ya d'ebo yar kad'an,lokacin da zai kaita bakinshi har saida ya d'an dauke numfashin shi kafi ya sakata ciki,a hankali ya fara chewing dinta kafin ya had'iye,abunda ya bashi mamaki kwata kwata baiji daddawan ya canja taste d'in abincin ba,kamshinta ne kawae ake ji,k'ara kai fork d'in yayi ya debo har ta dan fi ta farko yawa ya kai bakinsa,bayan ya hadiye ya d'ago fuskarshi ya kalleta a inda take tsaye ta zuba mashi idanu,fuskarshi ad'an sake kaman zai yi Murmushi yace"it tastes good",

Waro idanu tayi"Kenan tayi maka dad'i Yaya Handsome?,
Kai ya d'aga mata da d'an murmushi alamar eh,wata k'arar farinciki Fatuu ta saki lokaci guda ta fara tsalle had'i da juyawa saitin da hajiya take tana fad'in"Yeeee,an gwasale hajiya,an gwasale hajiya....",Sosae take tsalle kitson gaban kanta sai dagawa yake sosae, gaba daya ma gyalen ya zamo k'asa,ita kam hajiya mi zata yi in ba Dariya ba,sosae take tik'ar dariya,hakan ya jawo hankalin Saude ta leko,cike da farinciki fatuu ta tsaya da yin tsallan tace"Aunty Saude Yaya Handsome yaci abincin hajiya taji Kunya",hannu Saude tasa ta rufe baki tana dariya,ita kam Hajiya throw pillow ta d'aukko ta jefo ma Fatun,abunda bata sani ba Hajiyar ita tasa haisam d'in yaci abincin,dama da biyu taki ci lokacin da fatuu ta nufi kopar fita daga falon hajiya ta kalli haisam d'in da kai ta rinka lallashinshi tana magana kasa kasa akan ya daure ya ci abincin,

"To a samman in ci nima tunda wanda aka kawon don shi yaci" hajiya ce tayi maganar tana kallon Fatuu dake zaune a gefen Haisam,mak'e kafad'a tayi"baza ki ci shi ba kuwa,shi zai cinye abunshi"ta k'arasa tana murmura ido,

Dan gyaran murya haisam yayi ta juya ta kalle shi"ki yi hakuri ki bata",
"To ai baka ci da yawa ba fa" a shagwa6e tayi maganar,yace"Owk ki d'an kara man kad'an sai ki bata sauran" mik'ewa tayi taje gabanshi ta k'ara masa kafin ta nufi Hajiya da kulan,a gefenta ta dangwarar da kulan"gashi nan don ba Halin ki ba...."bata k'arasa ba sakamakon damkota da hajiya tayi ta daddage ta d'uma mata dundu tana fad'in"Kin raina ni ko Fateema"Fatuu dake ta dariya tace"to ai ke ba kakata bace ba",Sakinta tayi tace"Je ki d'aukko man fork nima in ci inji in kin iya girkin"cike da Zumudi tace to,har ta nufi kicin ta juyo"banda plate hajiya?"kai ta d'aga mata"eh bani cokalin kawae zanci acikin kulan,

Bayan ta kawo mata cokalin a gefenta ta zauna ta k'ura mata ido tana jiran taji mi zatace game da Abincin,jinjina kai hajiya tayi lokacin da takai lomar farko"Ah Masha Allah, tayi dadi sosae wllh,amman dae nasan dije ce tayi shi....."da sauri fatuu ta katseta"Wllh ni nayi shi na rantse da Allah,ita kawae nuna man yadda zansa abubuwa tayi amman tana zaune nayi har na gama" hajiya tace"lalle kinyi kokari"sosae fatuu ta washe baki alamar taji dadi.

Yana gama cin Abincin ya mik'e don gaba daya jin bakinsa yake yana warin daddawan,Bedroom d'in Hajiya ya nufa fatuu ta bishi da kallo har ya shige corridor kafin ta maido idonta kan hajiya"Wai hajiya da gaske Yaya Handsome baison daddawa?" cinye abincin bakinta ta fara yi tace"Wllh kwata kwata baisonta tun yana yaro,warinta yake ji sosae,wani lokacin har Amai yake yi in yaji kamshinta,shiyasa ma bai shan miyan duk da akasa ma daddawa yanzu haka da kika ga ya nufi dakina na tabbatar Brush zai je yi",
Jinjina kai fatuu tayi a sanyaye tace "ai da bai ci ba tunda bai so,ni fa koda nayi kuka saboda ke kinki kici ne", dariya hajiya tayi" karki damu,yaji zai iya ne shiyasa yaci,nima kuma dama don yaci d'in tunda shi kika kawo mawa yasa nace maki bazan ci ba,yanzu da yaci ba gashi nima ina ci ba"gyad'a kae fatuu tayi sai faman fara'a take ba k'aramin dadi taji ba da suka ci,

Fitowa yayi yana goge face d'inshi da tafin hannunshi da alama ruwane a fuskar,hanyar fita ya nufa don duk da yayi Brush d'in still jin bakinsa yake ba dai dai ba,Part dinsa zaije Don ya fesa had'addan Mouth spray dinsa ko zaiji daidai,
"in fita zaka yi don Allah ka d'an raka Fateema dare nayi"hajiya ce ta katse mashi hanzari,kai kawae ya d'aga ba tare daya kallesu ba,
"To Fateema tashi ki bi shi sai kuma Allah ya kaimu,Nagode duk da bani aka kawo mawa ba", mikewa tayi ta dauki kulan don tuni hajiyan ta gama ci,
"Sai da safe Hajiya" kai ta d'aga"Allah ya tashe mu lafiya",
har Fatuu ta nufi hanyar fita cike da tsokana hajiya ta dan d'aga Murya"Gobe ki kawo ma Yaya Handsome Tuwo da Miyan kuka",a sukwane fatuu ta juyo ta kalli hajiya dake ta dariya,ganin haka yasa itama tayi dariya tace"ai bazan k'ara kawo masa abu mai daddawa ba",daga haka ta juya tabi bayan haisam wanda tuni ya fice,

Da sauri ta isko shi don a hankali yake tafiyan,jerawa tayi dashi ta d'ago kae ta kalleshi"Yaya handsome don Allah kayi hakuri nasa kaci abunda baka so,wllh ni bansan baka sonta ba"d'an juyawa yayi ya kalleta da dan Murmushi calmly yace"Don't worry ur self,naji dadin abincin ai,thanks",jinjina kai tayi tana ta zabga uban Murmushi daga haka suka fuce daga Gate din gidan,

Fatuu na ganin har sun wuce katangar gidan Hajiya bai tsaya ba tace"Yaya handsome yau har gida zaka rakani ne?"kai ya daga mata alamar eh,taci gaba"ko dae don kar na sake zuwa kangon nan ne,ai bazan k'ara zuwa ba duk da ma an kamasu,oh lemunana ko suna can ko wani ya d'auke su"tayi maganar hannunta ruk'e da ha6arta,

"Ko zaki je ki duba ne" haisam yayi maganar idonshi akan hanya,dariya kawae tayi don ta gane gatse ne yayi mata,gab da kiosk d'in kawu Amadu Haisam ya ja ya tsaya,hakan yasa itama ta tsaya tana kallonshi"kije sai da safe"fatuu tace"to bari inma kawu Amadu magana ku gaisa,bata jira cewarshi ba ta juya tana kwala ma Amadu kira"Kawu Amadu ka lek'o ku gaisa da Yaya handsome",
lek'o da kai ta cikin kiosk d'in Amadu yayi tun kafin yayi magana Fatuu ta nuna masa haisam dayake an maido da wuta akwae haske sosae,,Haisam na ganin Amadun na k'okarin fitowa ya matso ya mik'a masa hannu suka gaisan,fatuu na ganin zai juya bayan sun gaisan tace"Yaya haisam bari abaka biscuit da sweet" yadda tayi maganar sai kace wani k'aramin yaro,wani kallo yayi mata da sauri tace"pls"ta marairaice fuska,jin baijin dad'in bakinsa yasa shi cewa"just a Sweet"da sauri tace to,ta juya ta nufi cikin shagon,can sai gata da ledan sweet ta mik'a masa,d'an bude ido yayi batare daya amsa ba,

"Gashi nan duka yace a baka" girgiza mata kai yayi"yayi yawa inada shi a d'aki,just one ya isa"Wani kallo tayi masa"kai Yaya Handsome ya zaka ce d'aya ya isa,don Allah ka amsa duka" k'in amsa yayi ya bita da ido tace"to in d'ibar maka rabi?"girgiza mata kai yayi alamar a'a,ya d'aga mata dogon yatsansa guda alamar guda daya zata bashi,
Chapter 52 · 0% Book details