Sashe 29
Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Waya haisam ya ciro daga cikin aljihun jeans din jikinsa ya shiga kiran hajiyan tana d'agawa yace"U have a guest" yana fadin hakan ya cire wayan ya ajeta a gefensa, dagowa yayi yaci gaba da kallon Abbas yana wani murmushi hadi da dan girgiza kai,dan guntun tsoki abbas yaja yace"irin ka ne in kukayi aure kunfi kowa jaraba wllh zaka rinka man wani kallon iskanci"cike da rainin wayo haisam ya dage gira yace"haba" kafin Abbas yace wani abu hajiya ta shigo falon tana sanye da dogon hijab har kasa hannunta rike da cazbaha nufo inda suke zaune tayi tana fadin"bako daga ina..."bata karasa ba suka hada ido da Abbas dake kallonta yana murmushi,hannu hajiya tasa ta rike ha6arta"Abbas,dama kaine bakon?aikuwa da nasan kaine ma ba zan fito ba,yanzun ma komawa ta zanyi"ta kai maganar tana kokarin juyawa,da sauri Abbas ya mike yaje yasha gabanta yana daria,ruko hannayenta yayi yana fadin"afuwan hajjaju ta,tuba nike" harararsa tayi tace"ni bawani dadin bakin da zakayi man,yaushe rabon da ka tako kafafunka gidan nan da sunan kazo gaidani?sai yanzu da abokinka ya dawo shine zan ganka wato dai dama saboda shi kadae kake zuwa ko?" da sauri Abbas yace"No hajjaju aikin san dae ina zuwa ko da baya nan,kawae kwana biyu wllh abubuwa ne sukai yawa bansamu na leko ba,amman dama yanzu zuwa nayi don in gaidaki in kuma bada hakuri,dawowa ta gari kenan..."hajiya dake d'an harararsa ta katseshi"dawowarka gari kenan kazo ganin abokinka ko",
"a'a ke nazo gaidawa ai shi tun kafin na tafi ma mun hadu,pls tuba nike muje ciki ki zauna sai mu gaisa sosae" uhm tace kafin ta juya suka nufi wurin kujeru,haisam dake ta latsa waya amman yana jin abunda suke cewa ya dago yana kallon Abbas da har lokacin yake rike da hannun hajia guda yace"da girman ka..."da sauri Abbas ya daga masa hannu alamar yayi shiru don Allah,karaf sukaji hajia tace"yake karya ba"gaba daya suka sa dariya,
saman 3 seater suka zauna Abbas ya shiga gaida ta,tace"ya iyali,suma dai ka hanamu zumunci kiri kiri Abbas" da sauri yace"ni na isa hajjaju ai in kullum kika ce kina son ganinsu indai ina gari zan kawo maki su",
"haka dae kace amman yaushe rabon da ka kawo su tun can kwanaki da kuka zo"
"in sha Allahu cikin satin nan zan kawo su hajjaju afuwan nasan nayi laifi",
"Shikenan zan hakura amman in baka kawo mun su anyi zumunci ba banga mai sasanta mu ba" da sauri yace"zanma kawo su ai" juyawa hajiya tayi side din da kitchen yake tana fadin"Saude ko ta gama sallan tazo ta kawo maka lemu" tana niyyar kwala ma sauden kira Abbas yace"bari inje in daukko ai ni ba bako bane dama kishi nike ji" ya mike ya nufi hanyar dining yana fadin"ke kin damu dani hajiata,shi wannan gwauron ko tayin ruwanma baiyi munba balle ma ya daukko man" haisam dake a kishingid'e yace"baka san inda ruwan yake bane,ko ni yaron ka ne da zan daukko ma"
Bayan Abbas ya daukko lemun bai zauna ba suka yi sallama da hajia,tace ya jira zata bada sako akai ma d'anta,Saude ce ta kawo masa ledar biscuits dasu sweets din da ta siyo ma hajiyar dazun da rana da taje siyayya kasuwa,suka nufi wajen gate inda ya parker motarsa,bayan Abbas ya tafi komawa haisam yayi part din hajiya ya ci gaba da kallo har aka kira sallan isha ya fito ya nufi masallaci.
*💖ASANADIN MAKWABTAKA💖*
*BY ZAINAB LALUH📲*
~(Oummu Imam)~
Free page 25
.......Bayan angama sallan komawa haisam yayi part d'insa ya shiga wanka,bai jima sosae ba ya fito daga cikin bedroom dinsa ashirye cikin riga da wando marasa nauyi rigan sleeveless hoodie ce army green,irin rigan nan mara hannuwa mai dauke da hula mak'ale a wuya igiyoyinta sun zubo saman kirjinshi sannan gaban rigan anyi wani design din rubutu baki mai walwali, wandon kuwa baki ne 3 quarter ya wuce gwiwarsa ya d'an matse,ba karamin kyau yayi cikin shigan ba,kirarsa ta kakkarfa ta bayyana,baisa hulan rigan ba tana kwance a bayansa sai da ya yi shut down laptop din dake ajiye a falon kafin ya fice ya koma part din hajia,don gaba d'aya yau he's busy working on his laptop dama kuma bai zuwa Gym ranar lahadi,tunda rana hajiya keta kiranshi tana korafin yana gida amman bazai zo suyi hira ba,ya sanar da ita yana wani aikine,tace to ya dawo falonta yayi aikin mana yace mata yafi samun network a part dinsa tayi hakuri da dare zai zo suyi firan.
*** *** ****
Tun bayan da ta shige d'akin bata fito ba saida aka kira magriba ta fito yin alwala anan suka had'e da Amadu yana ganinta yace"ke,yaushe ki ka dawo gidan?ba dazun da ki ka dawo daga islamiyya kince man zaki gidan hajia ba?" fatuu dake ta zare idanu tace"ai..ai hajiyan batanan ne shine na dawo" gyada kai yai ya wuce yayi alwalarsa ya nufi masallaci,itama alwalar tayi ta koma daki tayi salla,gaba daya ranta bai mata dadi sai tufka da warwara take zulluminta kada gobe tayi bataje ta bashi hakuri kaman yadda haulat ta bata shawara ba,gashi ita dae harga Allah tsoron zuwa take don batasan abunda zai biyo baya ba,kuma tana ganin mutumin kaman baida kirki,tana ta zaune har aka kira sallan isha'e,anan ta yanke shawarar komawa bashi hakurin bayan ta gama sallan isha din,
tana gama sallan ta shiga yin addu'a tana rok'on Allah da ya taimaketa mutumin yayi hakuri in taje,ta tuba bazata kara ba,tana cikin shafa addu'an ta jiyo sallamar gwaggo ta dawo,gabanta ne ya fadi rass ta shiga tunanin yadda zata fita daga gidan don tasan sai gwaggon ta tambayi abunda zata je yi gidan hajia yanzu,
d'aga labulen dakinta da gwaggo tayi yasata juyawa da sauri tana kallonta da yake akwae wutan Nepa,shigowa ciki gwaggo tayi jikinta sanye da uniform din aiki fatuu dake kallonta tace"Dja66ama bé wargo gwaggo",
"yauwa,ya gidan? "Lafiya lou" ta bata amsa,
"ashe bakiji dadi ba?yanzun nan Amadu ke gaya man a kopar gida" fatuu tace"eh amman nasamu sauki sosai,ya bani magani nasha har islamiyya ma naje" jinjina kai gwaggo tayi"kin kuwa ci abinci?" Girgiza mata kai fatuu tayi alamar a'a,ganinta sukuku gashi idanunta kaman tayi kuka yasa gwaggo cewa"kodae wani abun ke damunki?ince ba fitina kika jawo mana ba dae,dama inata mamaki kwana biyu da ba'a kawo man k'ararki ba,fada man gaskia minene fatuu? gabanta ne ya fadi rasss da sauri ta sunkuyar da kanta kasa tace"a'a gwaggo ba wani abu fa,kawai har yanzu ban dan jin dadi ne"ta karasa gabanta nata faduwa,
Jinjina kai gwaggo tayi ta nufi hanyar fita tana fad'in"ki tashi ki ci abincin sai ki k'ara shan magani,Allah ya sawaka,ni bari inje in watsa ruwa insamu na kwanta na kwaso gajiya sosai,kizo ki kar6i abincin gama abun biki can cikin jakata da aka ban in zaki ci su cin-cin ne da dublan" daga haka ta fice,sosai gaban fatuu yaci gaba da faduwa jin maganar da gwaggo ta mata,tabbas dole ta tafi taba mutumin nan hakuri tun gobe batayi ba asirinta ya tonu,
*** *** *** ***
Hajiya zaune a falo tana kallon sabon shirin kwana cas'in na tashar arewa 24, haisam ya shigo da yar sallamar da ba lalle ma in taji ba ya nufi kujera ya zauna yana facing din hajiyar,juyowa tayi ta kalle shi da d'an murmushi"sannu,yau kasha aiki,yini guda mutum na latse-latse,basu hakuri gobe kaje office din" hannu yasa ya shafo forehead dinsa kafin yace"ba aikin office bane" gyada kai tayi sai kuma tace"halan turawan ne,suda basu ganin mutum mai hazaka su kyale,in sunyi hakuri ba tattarawa za kai duka ka koma wurinsu ba"
d'an kwantar da kai yayi baice mata komae ba saima wani lumshe ido da yayi,da sauri ta juya tana kallon t.v jin muryar yawale yana magana,ba karamin cin dariyar acting dinsa take ba yana burgeta,tana ta daria tace"in baya ga ma film,ai ni a zahiri bazan iya d'aukan irin wannan matsayin direba ba,sai kata maimaita mashi magana sannan ya fahimta ina dalili" juyowa tayi tace ma haisam"wai nan direba ne fa ahaka" A hankali haisam ya ware idanunsa kan tv d'in yana kallon abunda hajiyan ke magana akai,dan murmushi yayi ya juya ya dauki wayansa dake aje a hannun kujera yana fadin"in driver dinki ne har marinsa zaki one day",
"in naga zai man wasa da rayuwa ba dole na maresa ba,ai wannan kyansa yaron gida ba abu mai mahimmaci kaman tuki ba" shi dai bai ce mata komai ba ya cigaba da latsa wayarsa,ita kuma hajiya taci gaba da kallon su yawale da rayya tana daria,jefi-jefi take waigowa tana ma haisam magana kan shirin don dama haka take bata iya shiru in tana kallo shidai sai dae yayi d'an murmushi ko ya daga mata kai don ba kallon shirin yake ba,so ba abunda yake fahimta.
Hajiya ta sake juyowa tace"akawo maka abinci ko?" Kai ya daga mata alamar eh,ta juya tana kwala ma Saude kira,bayan ta fito ta bata umarnin ta kawo ma haisam abinci tace mata basai ta zubo a warmer ba tunda yanzu zai ci ta amsa da to,ta shige kicin don zubo masa abincin,a tray ta d'auro kayan abincin ta nufo inda haisam d'in yake don ta fahimci indai shi kad'ai zaici abinci baison akai masa saman dining table,saman sofa table ta daura tray din tana gaishe shi ya amsa,tana kokarin zuba masa zo6o cikin cup ya dakatar da ita alamar ta barshi zai zuba da kansa,daga haka tace "aci lpy" sannan ta juya,