← Book details Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 107 OF 137

Sashe 107

Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Ya handsome " shiru bai amsa ba har saida ta k'ara kira sannan cikin murya mai tattare da bacci ya fara Magana "Zarah hope u'r ok" maimakon ta bashi amsa sai cewa tay "tun d'azun nike kiranka amman kaki ka daga",
"Wayan yana vibrate ne, any problem?"
"A'a dama kwalliyata ta yau zan nuna maka ka maida Vedio call kaga uban gayun dana yi",
ba tare daya k'ara cewa komae ba ya shiga maida kiran Vedio, yana kwance akan wani katafaren gado ya lullube rabin jikinshi da wani lallausan katon bargo blue don yanayin weather d'in can akwae d'an sanyi saboda samun ruwa da suke ba kamar Katsina ba gashi ya saba da Ac indae ba sanyi yayi tsanani sosae ba to bai zama ba tare da ya kunnata ba, Fatuu na ganinshi ta waro ido had'i da washe baki tana mashi dariya shima Murmushi yake mata yana daga kwance kanshi saman farin pillow haka rigar jikinshi kimono robe ce fara sol,
"Ya Handsome wannan gadon kane?" kai kawae ya d'aga mata alamar eh,
"To ina Hajiya da sauran yan gidanku,?" lumshe ido yay kaman bazai bata amsa ba da gani still da sauran bacci a idonshi a hankali kuma ya ware idon slowly yace "suna apartment nasu"
"Kenan anan ma bangarenka dabanne?" kai ya d'aga mata alamar eh,
"da an shigo bangaren naka yake kaman gidan Hajiya?" kai ya girgiza mata kafin cikin muryar bacci ya furta "Upstairs", zaro ido tay da mamaki tace "kai, gidanku na nan Abuja kenan benene tunda kace a Saman bene kake" kai ya sake d'aga mata ya fara kokarin tashi zaune don wani irin bacci ne ke fuzgar shi gashi sam baijin dad'in Vedio call d'in a waya don yafi sabawa da yayi a laptop, jingina bayanshi yay da kan gadon ya ruk'e wayar kan cinyoyinshi dake lullu6e da bargo, yana tashi zaunen da mamaki Fatuu ta kira sunanshi "Ya Handsome" bud'a mata ido yay ba tare daya amsa ba,
"Ashe yadda kake da gashi a hannunka har anan ma kake dashi" cike da al'ajabi tay Maganar tana nuna kirjinta alamar inda take magana akai, a hankali ya d'an duk'ar da kanshi ya kalli kirjin nashi dake abude sakamakon rigar dake jikinshi haka take bata rufe kirji in ba'a sa wata a ciki ba ga gashin nan liya liya a kwance saidae baida yawa sosae don yana rageshi, d'agowa yay ya kalleta ganin ta kafe wurin da ido tanata kallo yasashi kai hannu ya idasa jawo bargon sama, kallon fuskarshi tay suka had'a ido don kar ta sake yin Magana kan gashin yasashi cewa "kince zanga kwalliyanki" da sauri tace eh tare da saukkowa daga kan gado ta mik'e tsaye tun daga kan k'afafunta ta fara nuna mashi har saman fuskarta tana ta dariya,
"Nayi kyau sosae ko?" ta tambaya, fuska a sake ya furta "Yeah" shiru sukae na wani lokaci tana ta kallon fusakarshi tana dariya don dad'in Vedio Call din take ji shi kuma sai faman lumshe ido yake can yace "bazaki je yawo sallan ba?" da sauri tace "zanje, yanzu ai naje wurin Tk d'in don mu tafi kallon salla na iskeshe bai shirya ba amman yace yanzu zai shirya sai mu tafi" kai ya jinjina mata,
"Kai bazaka kallon Sallan ba",
" ba'a yi anan"
"Hawan barikin?" d'aga mata kai yay,
"Ai da yake ance Abujan duk yan gayu ne k'ilan baku zuwa kallo shiyasa ba'ayi, yanzu saidae kaita zama a gida kenan?" d'an Murmushi yay "No zan fita ba yanzu ba" gyad'a kai tay sukae shiru ita dae tana ta Murmushi shima fuskarshi a sake take yana cigaba da lumshe ido alamar dai har yanzu baccin yake ji can ya d'an langa6ar da kanshi da alama baccin yake, tsuru Fatuu tay tanata kallon fuskarshi,

"Wllh Allah Ya Handsome kanada bala'en kyau" yaji Maganar ta doki dodon kunnanshi, a hankali ya bud'e idanun akanta yana kallonta tana ganin ya bud'e idon taci gaba da cewa "bakaga da ka rufe ido ba yadda ka k'ara kyau" shiru kaman bazaice komae ba can kuma yace "kije kiga if he's ready"
"Tk d'in?" ta tambaya, kai ya d'aga mata alamar eh,
"To amman in bai shirya ba zan k'ara kiranka" shiru ya d'anyi sai kuma ya d'age gira yace "bazaki barni nayi bacci ba ko" kyalkyacewa tay da dariya ganin yadda yai mata Maganar tace "to na barka kayi bacci Sweetheart Ya Handsome d'ina, amman fa in muka dawo zan kiraka kaima ka nuna man gayun sallan ka" tay Maganar tana jaddada mashi da kanta, d'an guntun Murmushin gefe yay ya daga mata kai alamar to daga haka ta daga hannu tana yi mashi bye bye shima ya d'aga mata hannu guda kafin ya katse kiran, Lokacin data maida ma Tk d'in wayar yana cikin shiryawa don bayan tafiyarta kwanciyarshi yay ya k'ara yin bacci, cewa tay zata jirashi a parking space yay sauri ya fito yace mata to, bayan wani lokaci tana jingine da Motar Hajiya sai gashi ya fito ya dau wankan voile sai kamshi yake zabgawa, tana ganinshi ta fara kokarin bud'e Motar ya dakatar da ita da fad'in "Yau ba cikinta zamu fita ba"
"To a wacce zamu?" ta tambaya, Corolla S d'in Haisam wadda ranar data fara ganinshi ita ya hau tk ya nuna mata, da mamaki tace "To baya rufe abunshi ba taya zamu hau ta?"
"Ai ya bani makullinta yace ko zamuyi amfani da ita" ya fad'a yana kokarin zura key d'in ya bude Motar,Murmushi ta saki tana jinjina kirkin Haisam a ranta, Bayan sun fita saida suka tsaya suka d'auki Haulat kafin suka wuce.

ALBISHIRUNKU MATAN AFRICA DA KEWAYE SHAHARARRAR MAISAIDA KAYAN MATAN NAN WADDA KUKAFI SANI DA MAMAN HAIDAR TANA YIMAKU ALBISHIR DA CEWA ZAKU IYA SAMUN KAYANTA ADUK INDA KUKE AFADIN NIGERIA DA NIJAR, KARKU MANTA MACE MAI GYARA BATA BORANCI💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃08040448621
Akwai zafafan kayan mata masu matukar kyau da arha cikin sauki zamu aika miki da kayanki cikin aminci da yardar Allah su isa har inda kike ba cuta ba cutarwa karku bari abaku labari.
Muna kawo kalolin ingantattun kaya kamar haka 💥💫💥💫👇👇👇👇
1-Maganin sanyi
2-Maganin gyaran nono
3-Maganin hips
4-Akwai gumba kala kala
5-Maganin matsi masu ciko da gaba ki koma kamar budurwa
6-Kalolin garirrika masu bawa mace ni'ima da jimawa ajiki yana aiki
7-Akwai tsumi sha yanxu magani yanzu
8-Akwai jigidar sirri kala kala
Sannan kuma muna dahuwa kamar haka 💥💫💥💫👇👇👇👇
1-dahuwar kaza
2-yan shila
3-ciccibi
Dadai sauran su.Abubuwa dayawa gaskiya bazasu lissafu bah saboda lokaci maiso ta bini PC don ganin Kalolin kayan da muke dasu 08040448621,

ALLAH YAYI MAKI KIMA DA DARAJA AMATSAYINKI NA MACE👰,KADA KI WOFINTAR DA KANKI A WURIN MIJI SABODA RASHIN GYARA KAI, BURIN MAMAN HAIDAR KO WACE MACE TA ZAMA TAURARUWA⭐YAR LELE AGUN MIJINTA😍 SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI🤝

*💖A SANADIN MAKWABTAKA💖*
_*(Love and Destiny)*_

_*BY ZAINAB LALUH📲*_
~(Oumm Imam)~

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

6️⃣3️⃣

.......Bayan sun gama kallon sallan bazama sukae cikin gari ana yin la'asar Tk yace bari ya maidasu gida don akwae taron da zaije shida abokanshi Fatuu tace to ai basu gama zuwa inda suke so ba yace ta bari gobe tunda ba wani hawan za'a k'ara yi ba sai su fito da wuri suje duk inda suke so sannan ta amince ya maidasu gida, a gidansu Haulat suka sauka sai Magrib ta koma gida ana gama sallan isha taje shago wurin kawu Amadu tace don Allah ya kira mata Ya Handsome, tsawon lokaci ta d'auka tana waya dashi duk da shi ba wata Magana yake ba itace mai surutun wani lokacin tayi Maganar arziki wani lokacin kuma mara kan gado shi dae sai dai yay murmushi ko ya bata yar gajerar amsa har tambayarshi Hajiya tayi yace bai gidan ta kira wayanta, karshe dae saida ya nuna mata zaiyi wani abu sannan ta kyaleshi sukayi sallama, Washe gari ma kaman jiya tunda wuri ta shirya taje wurin tk lokacin ya tashi amman bai gama shiryawa ba tace bari taje wurin Haulatu in ya fito sai ya kirata a gidan harda jaddada mashi kar ya dad'e fa ya dai amsa mata da to, bayan yaje ya d'aukesu sosae sukayi yawo don duk wani wurin shakatawa kama daga park, zoo da sauransu dae har wani had'addan eatery ya kaisu suka ci duk abunda suke so suka kuma dauki wanda zasu tafi dashi duk ya biya kud'in, dama kuma duk inda suka je shike biyan kudin shiga da sauran abubuwan don Musamman Haisam ya bashi kudi saboda hakan, sai Magrib suka koma gida sun gaji likis sun kuma yo guzurin abubuwa sosae sannan duk inda suka je saida Fatuu tasa photographer dake wurin yay mata hotuna za'a turo ma Tk shi kuma sai ya tura ma haisam wad'anda akayi masu kuma da Haulat tace in an turo zata yi ma kawu Amadu magana sai ya tura mashi su,
Chapter 107 · 0% Book details