← Book details Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 137

Sashe 54

Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yaya handsome ka gama baccin ne?"a yadda yake ba tare da ya d'ago ba ya girgiza mata kai,
"to ka kwanta ka cigaba da baccinka",still bai d'ago ba yace"I can't sleep if there's someone around", jin tayi shiru yasa shi d'agowa ya kalleta,don kar tayi tunanin korarta yake yasa da sauri yace"Hajiya ma in tana kusa dani ban iya yin bacci" jinjina kai tayi alamar ta gamsu kafin tace"to ka tafi d'aki mana ka kwanta",
"In barki ke kad'ai?" tace"Eh mana ba sai in yi maka gadi ba kar wani ya shigo ta katanga su Officer basu sani ba",d'an murmushin gefe yayi jin abunda tace kafin yace"Yau ba aikin da zaki yi ne"hannu tasa ta ruke ha6a ta d'age ido sama alamar tunani"ba aikin da zan yi,amman yau gwaggo tace zata k'arasa man kitso bansan ko ta dawo ba yanzu",

"Ok,kije ki gani in ta dawon ko",
"To,amman sai na fara gyara ma d'ana parlon shi", tayi maganar tana kare ma falon kallo,shima d'aga ido yayi yana kallon falon kafin ya maida idon kanta"ai ba abunda yayi" jinjina kai tayi"eh amman dae akwae abubuwan da ya kamata a gyara",d'an ta6e baki yayi ya dage shoulders d'inshi daga haka ya mik'e ya nufi Bedroom dinshi,yana kaiwa daidai Corridor fatuu ta juya kai daga kan C-table d'in da take tace"My son kayi bacci mai dadi kuma kayi mafarkin mamanka",d'ago mata hannu yayi murya a kasalance ya furta"Owk,Mom Zaraah",daga haka ya tura kofa ya shige Bedroom d'in.

*** **** ****

Ba k'aramin bacci yayi ba don sai can bayan la'asar ya farka,hannu ya kai ya d'auki wayansa yana duba time,da sauri ya mike zaune ganin karfe hudu da rabi hakan na nufin yayi missing Sallan la'asar,da k'yar ya saukko da kafafunsa ya nufi Toilet don ya watsa ruwa saboda duk kasala ta baibayeshi,

Sanye cikin jeans da T-shirt ya fito ya nufi masallaci duk da lokaci ya kure,bayan ya gama sallan zama yayi cikin Masallacin yana yin azhkar d'in yamma,bayan ya gama yana fitowa daga cikin Masallacin wayarsa dake ruke a hannunsa ta fara ringing,duba mai kiran yayi kafin ya d'aga,tun kafin yayi magana on the other hand akace"Kana ina ne naje part dinka baka nan,nazo na Hajiya ban samu kowa ba",

"Ina a masallaci gani nan fitowa",daga haka yayi rejecting kiran,yana fitowa kopan masallacin ya hango Abbas tsaye agaban part din hajiya,juyowa Abbas yayi ya kafe Haisam d'in da ido ganin yana dangyashi hakan yasa Abbas din k'arasawa wurinshi,hannu ya bashi suka gaisa kafin yace" What happened, naga kana dangyashi

"Na samu rauni ne a kafan",
"rauni,wane irin rauni"Abbas ya tambaya,
"Na taka kwalba ne" ya bashi amsa a takaice,cike da mamaki Abbas yace"kace shiyasa jiya na tambayi ko kana wurin aiki kace man a'a kenan?"
"Yeah,bana zuwa sai na samu sauki sosae"
Cike da jimami Abbas yace"wai garin yaya?A ina ka samu kwalba har ka taka?" bai bashi amsa ba sai cewa yayi"Muje ciki mana"ya kai hannu ya kamo hannun Abbas d'in daga haka suka nufi part d'in haisam,

Lokacin da suka shiga cikin parlon atare suka ja suka tsaya suna bin shi da kallo,gaba daya Fatuu ta harmutsa shi,sam Haisam bai lura ba d'azun don yanata sauri yaje yayi sallan la'asar da ta wuce shi,Flower vases d'in dake a bakin corridor ta kinkimo su ta jara su a kan carpet d'in falon,yayi mamakin yadda ta iya daukko su don ba karamin nauyi ne dasu ba,ta d'aukko telephone da lamps d'in dake akan desk ta maido su kan C-table,haka Sound systems d'in falon ta rarraba su wasu dogaye ta jajjerasu a bayan kujera L-shape,
Kallonshi Abbas yayi"Waye yayi wannan gyaran,ko duk gwaurancin ne yasa baka iya gyara falo ba" fuskar haisam d'auke da Murmushi ya nufi kujera ya zauna yana fad'in"kasan dae nafika iya komae na cikin gida Abbas,wani yarinyane tayi gyaran"cike da mamaki Abbas ya maimata abunda haisam d'in ya fad'a yana kokarin zama kan armchair,
"Yaushe ka fara shiga harkar yara ko ince yaushe yara suka fara shiga harkar ka?"
"Wannan tafi karfi na ne"

"Tafi karfin ka,wannan wace Yarinyace haka da har tafi karfin ka?"da tsananin mamaki Abbas yayi tambayar idonsa akan haisam d'in,kwantar da bayanshi yayi ajikin kujeran a takaice ya fara bashi labarin Fatuu sai dae ba komae ne ya fad'i masa ba kaman kango da taje har ya taka kwalba duk bai fad'i masa ba,Dariya sosae Abbas ke yi,lokacin da haisam ya gama bashi labarinta yace"kai gaskiya yarinyar yar bala'e ce gashi ta cika abun dariya,amman fa wllh da ni ta fasa ma glass bazan yarda ba" wani kallo haisam yayi masa"what u would hv done,zaka ce a biyaka ne,or what?",

"Ai inma nace a biyanin ba laifi bane kuma ko ba ni ba adai halin da ake ciki yanzu kowa tayi ma hakan wllh cewa zai yi sai an biyasa,ta dae ci sa'a kawae da kaine ta fasa mawa",
Wani kallo haisam ke bin shi dashi ya d'an ta6e baki"in kuma basu da halin biyan naka fa Abbas?"
A d'an harzuke yace"to kuwa jikinta zai gaya mata wllh,don har gidan nasu zan je in zaneta "sosae yaba haisam dariya don yasan da gaske yake maganar don shima Abbas d'in dan balae ne,

"U Know what Abbas,irin yaran nan duka bai masu sai ma k'ara masu rashin ji,yanzu da ban taking wani action kan hakan ba,ba gashi ta canja ba har ta zama Mom d'ina" ya k'arasa maganar yana ta dariya,
Jinjina kai Abbas yayi"U'r right,amman shima gayen daya fad'a mata kudin glass d'in ya iya zuka karya koda yake d'an shaye shaye ne abunda yafi hakan ma zai fad'i,just abunda ba zai wuce 50k ba yace wai 1 million,amman shima ya taimaka tunda yasa ta tsorata har tayi alk'awarin ta daina rashin jin"ya k'arasa maganar shima yanata daria,

"Ina My boy" haisam ya tambaya,
"yanzu haka na baro shi yanata kuka wai sai nazo dashi"
Haisam yace"baka kyauta ba ai da ka kawo man shi mun gaisa yaga babanshi daya dade bai gani ba",

"rabu dashi kawae rigima zai zo yayi maka ba wani abu ba"

"Why? haisam ya tambaya a takaice,
gyara zama Abbas yayi kafin yaci gaba"kagane wani toy ne that looks exactly like a real laptop da ake talla a mbc,shine yasa rigima sai an siya masa ya takura man,so ganin toy d'in zai yi amfani wurin taimaka ma yaro ya koyi abubuwa,don akwae educational apps da cartoons sannan yaro zai iya yin typing kuma za'a iya tura masa wasu apps din kaman islamic haka,so na neme shi anan ban samu ba gaskia,sai nayi ma wata colleague d'ina lecturer magana da yake tana ordern kaya daga waje ko zata samo masa,tace zata bincika man,nace amman in ansamun ta fara fad'a man price d'in kafin tasa akawo,aikuwa kaman yadda nayi zaton zai yi kudi sai gashi tace man ansamu price din zai kama 40k,ai sai kawai nace ta barshi yayi ta rigimar in ya gaji ya daina,aikuwa yaron nan ya kaunaci Allah ya hana man zaman lpy dole na samo mashi wani karami dan 5k ai koda nakai mashi sai yayi wurgi dashi wai shi bai son shi har ya d'an fashe da yake roba ne,ya ban haushi na zane shi,aikuwa sai na k'ara tado ma kaina rigima dole na koma lallashin shi nace ya fara amfani da wannan d'in babanshi Zakee yana can k'asar da ake saida waccan da yake so zan mashi waya in zai dawo zai kawo masa,shine fa nasamu ya shafa man lpy,wai d'azun da nike fad'a ma Feenah zanxo wurinka in na fito yaron nan ashe bai manta ba da yake banzan kai ne dashi kaman naka,bai mantuwa kawae sai yaje ya sanyo takalma wai zaizo ya kar6i kwamfuta d'in shi wurin Baba zakee tunda ya dawo,kasan Allah ni nama manta,dubara ta fad'o man nace mashi wannan wanda zani ba shine baba zakee ba shi H,zakee sunanshi baiji na fad'a ma Momynshi ba,yace shi H,zakeen baida ita,nace mashi eh ai shi tare muka dawo daga Abuja ba shine a k'asan da ake saida computer din ba,shine fa na samu na gudo,feenah nata man Dariya"

Sigh haisam yayi yace"ai da ka siya masa tunda zai masa amfani,from d way kai describing nashi it will help him learn things easily so kudinsa ba abun damuwa bane"
"Uhm kudinsa kam abun damuwa ne,ka kuwa san da kudin zaka mallaki buhun shinkafa harma ka hada da d'an galan d'in mai,koda yake kai fa ba siyan shinkafar kake bama shiyasa zaka ce hakan,kyale sa kawae yanzu ba komai dama ake so akuma samu ba,rayuwan yayi tsada ta abinci ake ba wani abun wasa ba" k'ura masa ido haisam yayi ya cije lip d'insa na kasa kaman ba zai kara cewa komae ba,

"Da kana yaro me ka ta6a nema ka rasa Abbas? shine kai yanzu za kai denying yaro abunda yake so" sosae Abbas ya kyalkyace da daria "wuuuh h,zakee kai fa na manta you don't give up easily,shi yasa ko da muna skul abokan adawan ka na debate ke shan wuya,is hardly ai nasara akan ka,kai baka ganin rayuwan yayi tsada yanzu,"
girgixa kai haisam yayi"kawai dae zaka cutar man yaro,thank God he has another father,ka turo man picture din toy en,akwae computers da za'a turo man next week zan tura masu su bincika masa sai a hado man nasan baza'a rasa ba,koda ba exact irinshi nasan za'a samu mai irin features din shi"

Abbas yace"ah haba ka rabu dashi wllh...."haisam ya katse shi da fad'in"ina ruwanka ne,wait Abbas....,badai so kake ka nuna man iyakata a gun yarona ba..."da sauri Abbas ya daga hannuwanshi alamar ban hakuri yace"Apology baban Abdul "ta6e baki haisam yayi kafin yace"Don ma he's too young ai da ta gasken za'a kawo masa,don so nike ya zama expert tun yanzu don babanshi zai gada shima Computer engineer zai zama insha Allah"
"Allahu yashaa,Hakan nada kyau ai daman kyan d'a ya gaji mahaifinsa"Abbas ya fad'a yana murmushi don kar ya k'ara wani laifin,shi dai Haisam d'an ta6e baki yayi ba tare da yace masa komae ba.
Chapter 54 · 0% Book details