← Book details Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 137

Sashe 91

Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Lokacin da suka shiga ba kowa acikin falon hakan yasa ta nufi d'akin Saude Haulat d'in tabi bayanta, lokacin da suka shiga Sauden na kwance tana hutawa don bata jima da gama gyaran gidan ba tana jiran ayi azahar ta fara aikin bud'a baki don ita ke yin na cikin gidan kuma ba laifi shima aikin yana da d'an yawa don ana yin abubuwa sosae don Hajiya na gayyato yan shan ruwa wani lokacin, da sallama suka shiga ta d'ago fuskarta da fara'a ta amsa, mik'ewa tayi zaune tace suzo su zauna ta nuna masu bakin katifa,
"Sai yau muke ganinki" Saude ta fad'a tana kallon haulatu da Murmushi, gaishe da ita ta fara yi kafin tace "ai ina zuwa amsar sadaqa ban dai shigowa nan d'in" jinjina kai saude tayi ta maida idonta kan Fatuu dake zaune fuska a d'an d'aure tace "Fateema ya azumin kinayi yau d'in ko?" kai ta d'aga mata kawae, taci gaba da cewa "in kika daure a hankali zaki ga kin saba" sai lokacin ta bud'a baki tace "amman ai wuya nakesha fa, ko jiya da akasha ruwa har amai nayi" ta k'arasa idanunta sunyi rau rau alamar kwalla, d'an Murmushi saude tayi tace "eh haka naji d'azun abakin Hajiya data kira gwaggonki, amman tace mata ai ruwa kikasha da yawa kuma dama ko babba ne yakai azumi yasha ruwa da yawa wani lokacin amai yake sawa, ki rinka shan d'an daidai daidai in aka kira sallar daga baya sai ki k'ara kinji" ta k'arasa Maganar ta sigar lallashi ita dae kai kawai ta d'aga mata, hira suka ci gaba da d'an ta6awa sai dae yawanci ita da haulat ne suka fi Magana ita kuma ta kwanta gefe guda,suna ahaka aka fara kiran sallar azahar lokacin Fatuu har tayi bacci, alwala suka yo suka kabbara sallah, bayan sun gama ne saude ta tada Fatuu itama tayi sallar, anyi arziki yau batayi rarrafen ba saidae d'an yamutsa fuska da take tana dafe ciki ahaka har ta shige toilet d'in, haulat dake kallonta ta girgiza kai afili tace " naga randa Fatuu zata saba da azumi",
" zata saba ne ahankali tunda gashi yau da kafafunta ta shiga toilet jiya ai rarrafe tayi" bud'a ido haulat tayi ta maimaita abunda saude tace sai kuma ta fashe da dariya tana fad'in Allah ya shiryi fatuu, saude da itama ke dariyar don abun ba k'aramin dariya yabata ba a jiyan ta amsa da Amin, suna zaunen saude tace zataje kitchen ta fara aiki haulatu tace bari tazo ta tayata suka fita atare bayan duk sun cire hijjaban suka bar Fatuu na yin sallah, Bayan wasu mintuna saiga haulat ta dawo d'akin lokacin Fatuu ta dad'e da gama sallar tana kwance kan abun sallar,

" ki taso mu tayata aikin tare zaki ji kin rage jin yunwa, dama in kana yin aiki baka fiye jin azumin ba" haulat dake tsaye akan Fatuu ta fad'a,banza tayi mata sai kace ba da ita take magana ba, har k'ara maimaita mata Maganar tayi amman ko ci kanki bata ce mata ba hakan yasa ta juya ta koma kitchen d'in, suna cikin feraye dankali da doya sai gata ta shigo fuskarta sam ba annuri ta kasa bacci saboda yunwa gashi kuma ta d'an damu da fushin da taga kamar Haisam yayi hakanne yasa ta fito ta d'anyi wani abu wai ko ta daina jin yunwar kamar yadda haulat tace, saude na ganinta tayi d'an Murmushi tace "masu azumi anzo taya mu ne?" kai ta d'aga mata alamar eh,
"To zo ki zauna kuci gaba nikuma sai in gyara cefane" ta fad'a yayin da ta mik'e don fatuu ta zauna saman kujerar, cigaba da feraye dankalin sukai tana yi tana d'an watsa ruwan dankalin a fuska Haulat dai nata kunshe dariya ita kuma tana harararta, bada dadewa ba suka gama Haulat tayi ma Saude sallama zata tafi gida sauden nacewa gashi ba'a gama komai ba haulat d'in tace ba komai, amman duk da haka saida ta bata lemun roba da fruit tai mata godiya tace ma Fatuu kawata asha ruwa lafiya daga haka ta tafi tana dariya ganin hararar da fatun ke mata ta d'aga murya tace ba ita ta kar zomon ba rataya aka bata.

Bayan tafiyar Haulat bada jimawa ba fatuu ta tambayi Saude karfe nawa tace mata ukku saura yan mintuna kad'an nan take tayi yar dariyar da duk ranar bata yi ba jin lokacin yayi sauri, ci gaba da taya sauden aiki tayi har tana ce mata taje ta huta tace ai lokacin baya gudu in ta kwanta, dama kuma Fatuu ba raguwa bace tana da zafin nama kawae azumine yasata tayi laushi, duk bayan d'an lokaci sai ta tambayi Saude karfe nawa yanzu kuma, da ta d'anyi aikin sai ta zauna ta huta in na tsayuwa ne, tana cikin yankan fruit da za'ai fruit salad aka kwad'a kiran salla cike da mamaki tace "kai, wai har la'asar tayi?" gyad'a mata kai Saude tayi tana yar dariya aikuwa nan take ta fara murna tana washe baki, ashe da sauran dariyar azumi bai k'arar da ita ba, bayan sunyi sallar la'asar ne saude tace taje gida ta taya Gwaggo aiki amman da ansha ruwa ta dawo susha ruwa tare tace to, dama ko ba wannan azumin ba agidan hajiya take wuni tana taya saude aiki don ita da wuri take farawa, gwaggo kuma sai yamma wani lokacin ma in aikin rana take tunda safe take yin rabin aikinta koma fi ta bar ma Fatun d'an wanda zata karasa, koda ta koma gidan bata kwanta ba aiki ta shiga taya gwaggo wanda hakan ba k'aramin mamaki ya bata ba don tayi zaton tana can baje bata iya ko mik'ewa ganin yadda ta tashi hankalinta da Asuba shiyasa ma bata yi niyyar kiranta ba sai ankusa shan ruwa tunda can zata fi shan iska, gab da kiran sallar Magrib sun gama komae fatun ma ce ke jera abubuwan shan ruwan asaman katuwar darduma hakan kuma ba k'aramin dad'i yay ma gwaggo ba, ba kamar da ta tambayeta kodae ta karya azuminne ta rantse mata da Allah bata karya ba tace to taje ta watsa ruwa kafin akira sallar, lokacin da tayo wankan ta fito wani nishadi ta rinka yi tanata washe baki sai kace ba Fatuu mai kukan azumi ba gwaggo dae sai girgiza kai take tana Murmushi tace taje ta samu kaya maras nauyi tasa ta amsa da to, yar shimi da wani dogon wando ta sanyo tazo ta zauna gaban kayan shan ruwan da ta jere kiran Salla kawai take jira, aikuwa bata dad'e da zama ba liman ya kwad'a kiran salla kaman don taji, da sauri takai hannu zata dauki jug d'in ruwan sanyi sai kuma ta tuna da abunda Ya Handsome yace na tasha abu mai dumi in zata iya hakan yasa ta aje Jug d'in ta janyo bokitin kunu ta kafa baki ta kurba kaman sau ukku sannan ta aje ta d'auki ruwan sanyin shima ta kafa baki saidae sam bata sha da yawa sosae ba sakamakon abu mai d'umi da ta fara sha kuma tajita tayi wasai cikinta daidai kuma bata jin wata kasala, bud'a baki ta fara hankalinta kwance sai ta janyo wannan ta d'an ci ta maida ta janyo wani ta tsakura tana ci har wani rawa take da kai ita kam gwaggo saida tayi sallah sannan tazo ta zauna alokacin shima Amadu ya shigo suka ci gaba da yin bud'a bakin atare yana tayi ma Fatuu tsiyar abunda tayi jiya sai faman kyalkyatar dariya take sai kace ba ita ba, bata cika cikinta sosae ba don tasan Saude zata aje mata kayan shan ruwa dama ko ba yanzu ba tana aje mata intaje sallar asham sai taci ko kuma bayan angama sallar shekaranjiya dae saboda ansata azumin dole da jiya duk bataje sallar ba,

Mik'ewa tayi ta d'aukko Hijab acikin d'aki bayan ta fito tace ma gwaggo ta tafi salla Amadu na fad'in shifa bai yarda da ita ba anya cikakken azumi tayi yau, lokacin da ta kai bakin kopar zaure ta juyo da karfi tace "Da kenan" daga haka ta fuce sunata mata dariya, Lokacin da ta shiga Falon Hajiya suna saman table ita da Haisam jin sallamarta yasa ta juyo ta kalleta banda haisam d'in, alamar tazo tayi mata da hannu hakan yasa ta nufe su ta tsaya agefen hajiya tace "Hajiyar Sanata ansha ruwa lafiya" saida ta cinye abunda ke bakinta sannan tace "Lafiya lou kema kinsha ruwan lafiya ko?" kai ta d'aga mata tana satar kallon haisam da bai ko kalleta ba yanata bud'a bakinshi a nutse,
" Ya Handsome barka da shan ruwa" ta fad'a a sanyaye don taga kamar yayi fushi da ita, hannu kawae ya d'an d'aga mata ba tare da ya ce mata komae ba hakan kuma ya tada mata hankali sosae,
Chapter 91 · 0% Book details