← Book details Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 137

Sashe 26

Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

cikin kuka Fatuu tace"ai ni nayi zaton tambayana kike ko nasan mutumin" taci gaba da rusa kuka,Haulat tace "ki daina kuka,ki kwantar da hankalinki..." a fusace Fatuu ta katseta tace"amari hakkilo?ya za kice wai na daina kuka,kuma taya zan kwantar da hankalina bacin nasan tabbas duk abunda gaye ya fad'a gaske ne.." Haulat ta juyar da kanta gefe ta dan gwalo ido cikin ranta tace"tabb lalle abu yayi abu,yau su Fatuu harda yin fullanci,ita da bata son yi,wani lokacin inta fama da ita tayi man ta k'i yi" Fatuu dai sai kuka take tana sambatu "ni wllh bansan haka motan keda tsada ba,da bazan ma fara fasa masa gilashi ba,ace kudin shanu gomaa har sau goma ne kudin motar,ba dole gilashin ma yayi tsada ba" Haulat ta jinjina kae ta kalleta tace "nawa yace motar take ne" da sauri fatuu tace"Miliyan goma faaa" haulat tace "bama tada tsada sosae...",a fusace fuska jage jage da hawaye fatuu tace" miliyan goman ne ba tsada,shiyasa nace baki da hankali,koda yake nasan baki taba sanin yawan miliyan a hannu bane shiyasa zaki ce haka,yo inama zaki gansu" girgiza kae haulat tayi sam bata ji komae ba don dama ta saba datsa mata magana,tace "dama ban ce ai na ta6a ganinsu ba ko,kawae dae nasan akwae motoci masu tsada sosae da yan gayu ke hawa,don na ta6a ji yaya Osman dinmu yace harta miliyan d'ari akwae" da sauri Fatuu ta dafe kai tana fitar da numfashi mai karfi a rude tace "kice Allah yaso ni da ba irinta na fasa ma gilashi ba,yasin nasan wannan sai dae a harbe ni kawae" ta k'ara fashewa da kuka,ita kam haulat dan juyar da kanta tayi tana murmushi don dariya maganar ta bata,
Zamewa k'asa Fatuu tayi ta zauna dirshan taci gaba da kuka tana sambatu"mi woni ni fatuu,mi woni..,na bani na,in Gwaggo taji wannan maganar nasan sai tasa kawu Amadu ya kakkarya ni kafin awuce dani kuma gidan yari inje in rink'a cin gabza kwarkwata kuma ta gwaigwaye man gashi,tunda nasan ba yafe man zai yi ba,gaskiyar Gaye wllh nasan ko kawu Amadu nayi ma haka ba zai ta6a kyale ni ba sai ya dau mummunan mataki akaina,balle wannan da ba abunda na had'a dashi,nasan ko hajia taji bazata hanashi ya dau mataki a kaina ba,daman kullum tana man fadan in daina rashin ji,ko jiya ma saida tace zamu 6ata,yanzu kuma taji wannan asaran da na yiwa d'anta ta uban kudi haka,tabb ai nasan ma ba za tace ya yafe ba,to mima muka had'a da ita da zasu yafe,daga makwabtaka....,ga Hajiya dama ta iya masifaa....mi maye ni Fatuu,na mutu kawae" ta d'ora hannuwanta saman kai kafin ta dago tana kallon Haulat wadda tuni dama ita ta ke ta kallo cike da tausayi,tace"dama nasan ba wata shawara da zaki iya bani,wannan babban abu ne ba irin wanda ki ka saba ban shawara bane,nasan dole sai an kaini gidan yarin" ta kai maganar tana ta faman yin sheshsheka.

A hankali Haulat ta durk'usa kusa da ita ta kalleta tace"duk da haka ina da shawarar da zan baki,kuma ina tunanin Insha Allahu zata yi aiki..." da sauri fatuu tace"kenan kina ganin in nayi amfani da ita ba za'a kaini gidan yarin ba?mutumin zai hakura?" d'an murmushi haulat tayi"tace ehh,in Allah ya yarda zai hakura nike tunani..." fatuu ta k'ara katseta da sauri"toh don Allah fada man abunda zan yi ko minene zanyi indai za'a kyale ni nidai" Haulat tace "saurin mi kike,zan fad'i maki amman sai kin yi mani Alkawarin in dae aka kyale ki bazaki kara aikata makamancin wannan abun da kika yi ba" wani irin kallo fatuu ta juyo tana mata mai kama da harara,can kuma ta dauke fuskarta ta kalli gefen haulat d'in tace "da yake kare mai bak'in baki ne ya cije ni zan k'ara aikata hakan,ko baki ji tun d'azun nace maki nayi dana sani kuma bazan k'ara ba" ta kai maganar tana turo baki,Haulat tace"nasan halinki ne kin iya tuban mazuru,sau nawa kike cewa baki k'ara yin abu kuma kizo ki karan" Cike da gatse Fatuu tace"to gwaggo kiyi hakuri...,don kawae kinga ina neman taimakonki zaki taman maganganu sai kace ni mahaukaciya ce zan sake,ni in zaki fada man abunda zan yi ki fada man lokaci na k'urewa" ta kai maganar tana dan turo baki tana kallon hanya,
Karasa zaunawa a kasa Haulat tayi,ta juyo tana kallon fatuu tace"KI JE KI BASHI HAKURI........

*💖ASANADIN MAKWABTAKA💖*

*BY ZAINAB LALUH📲*
~(Oummu Imam)~

*Paid Book*

*Free Page23⃣*

*Haisam*

Zaune a cikin parloun sa yana operating laptop wadda take mai kyaun gaske jikinta sai shining yake yayin da bayanta ke dauke da tambarin Apple,jin ana k'okarin shigowa cikin parlon kai tsaye batare da anyi knocking ba yasa ya dan waiga ya kalli kopan,

A hankali aka turo kopan ta bud'e,wani matashin mutum ne wanda bazai wuce tsaran Haisam din ba ko ya girme masa da kad'an ya shigo,jikinsa sanye da jeans da longsleeve shirt,kalar fatarsa kuwa za'a iya kiransa da wankan tarwad'a don ba bak'i bane,fuskansa na dauke da k'asumba mai gashi da dan yawa sai dai bai tara a saman kansa ba,gashin fuskan nasa yasha gyara sai kyalli yake da gani yana kashe masa kudi yadda ya kamata.

Suna had'a ido da Haisam wanda ya jingina bayansa jikin kujeran da yake zaune ya washe baki yana daria hakan ya bayyana wushiryar dake a bakinsa,shikam haisam murmushi kawae yake yana kallon mutumin,a bakin kofan ya cire takalmansa kafin ya nufo cikin parlon yana fadin"Haisam Alee zakee,yaro dan Senator jikan Minister,na hajiyar sanata sai dubu ta taru,kowa yake son ganin 6acin ran hajia to ya ta6a ka,yaro mai tsananin farin jini,har makiyanka burgesu kake inma akwae su kenan,yadda farin ka yake na daban,haka aniyarka ma take ta daban,kaine uban duk wani mai tsafta.....a 6angaren aiki kuwa,you are the best computer engineer in the whole nation,kai kasan hardware kasan software,a bangaren Networking da robotics kau baka da tsara,ana mutane ruwa biyu kai d'in ruwa ukku ne,kaine hausa,kaine fulani,kaine larabawa.....",
Tunda ya fara magana Haisam dake zaune tamkar wani saraki,hannunsa na dama rike da beard dinsa yasa index finger d'insa yana dan bubbuga bakinsa,yanata bin mutumin da ido,ganin baida niyyar tsayawa da kirarin nasa yasa shi cire yatsansa daga bakinsa Calmly yace"Abbasss...." jin kiran sunansa da haisam din yayi yasa Abbas din kyalkyalewa da dariya ya miko masa hannu suka tafa kafin kuma suka gaisa,ya nufi dayan side din kujeran da haisam din yake ya zauna yana fadin"to ya kaji praising din nawa,am i good at it?"
dan ta6e baki Haisam yayi hadi da d'age gira"Not bad"yace, still Abbas d'in daria yake"kace inna maida shi sana'a zanci Abinci dashi kenan?"ya fada,

Haisam wanda har lokacin fuskansa na dauke da murmushi yace"shi kuma lecturing d'in ka kaishi ina?" zama sosae Abbas yayi ya d'an kwantar da bayanshi jikin kujeran yace"baka ga yadda ya zama ba,duk yana neman komawa shiririta,that's why na fara neman wata sana'ar kaga sai yazama inada alternative in ba wanccan sai inci gaba da bin yaran masu kudi ire-irenka ina masu kirari,nasan ba karamin kudi zan rinka samu ba"

Haisam da shima ya dan kwantar da kanshi cike da zolaya yace"wani ke shiriritar da aikin naku baku ba?nan gaba ma in aka biye maku kashe ilimin zaku yi gaba daya,yakamata tun wuri ai taking action akanku" Abbas dake ta daria yace"wani action kuma banda hanamu salary da ake" dage gira haisam yayi"I mean sacking...." da sauri Abbass ya d'ago da kanshi yace"amman kai mugu ne H,zakee,wato kai burinka kenan a kora mu ko" sai lokacin haisam yayi dariyar da hak'oransa suka bayyana,

"in an kora mu sai akawo suwa su koyar? ko su ku za'a maido tunda an fada ma lecturing d'in wasa ne",

"banyi tunanin zaka yi man wannan tambayar ba,seems like ka manta a wace kasa muke ko,kuma nima kasan dae zan iya ai,miye a ciki,all i need to do is Pgde,tunda ba education nayi ba,kai tsaya kaji ko banyi ba zan iya lecturing din,harma in fi wasu da suka dade a fannin" ya karasa maganar cike da tabbacin abunda ya fada.
Abbas yace"aikuwa da kasa mata sun rinka tara c.o"
"Why?" haisam ya tambaye shi.
"Muddin kazama lecturer ai shikenan kuma zaka janye hankalin mata ya dawo kan ka,ba kamar yan matan jami'a da basu shakkar nuna ma malami suna sonsa komae tsaurinsa,basu damu da zai wulakanta su ba,na tabbatar hakance zata faru da kai,ai gaba d'aya nike gaya maka attention dinsu kanka zai dawo,instead of focusing on their studies,kaga ba karamar barna zakai ba kaima,don kasuwa zakayi sosae abokina" ya karasa yanata faman daria.

Shi dae haisam still yayi yana kallon Abbas,tsaf ya fahimci dalilin da yasa abbas din cewa mata zasu maido attention dinsu akansa,don tunda ya taso yana k'arami ake fada masa yana da kyau na musamman har kuma yanxu da ya girma ba'a daina fada masa hakan ba,haka kuma da wuya a kalle shi ba tare da ansake waiwaya wa ba.

Abbas smiling broadly ganin haisam din yayi shiru yace"ko ba daidai na fada ba,I lie? Sauke 6oyayyan ajiyar zuciya haisam yayi kafin yace"in tambayeka Abbas...?"abbas yace"I'm all ears zakee" haisam ya cigaba"have u ever talk completely without mentioning women?na rigada na fahimci is hardly a kare magana da kai baka ambaci mata ba,to ni wannan ba matsalana bane,nothing concern me wit dem,kaima da suke kula ka ai don kana kula su ne,ko bansan ka bane"

Dariya sosae Abbas keyi harda buga kafa yace"to in ban rink'a ambaton mata ba,maza zan rinka ambato H,zakee,ai mata namu ne,muma kuma nasu ne" d'an ta6e baki haisam yayi yana girgiza kai kafin yace"to ya Abuja?"
"sai da ka gama caccaka ta har kana man mummunar fata sannan zaka tambayeni,ashe kaima baka tausayin malamai bayin Allah",
Chapter 26 · 0% Book details