← Book details Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 137

Sashe 7

Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yan mintuna ta d'auka ta dawo dauke da Tray saman shi wata irin Warmer ce mai kyau a gefen warmer din Bowl ne an d'aura Plates kalar bowl din, samansu kuma Cokulla ne da Serving spoon da gani na kulan ne duk anyi Wrapping dinsu,dining table din ta nufa...."Bring it here"ya dakatar da ita daga daurawa saman table din ta nufo inda suke saida ta fara daura tray din saman kujera one seater ta kinkimo sofa table din da kyar hajia na fadin"bi sannu dae kar ki bige kafa," To" tace lokacin ta karaso da table din gaban shi ta maido tray din saman shi ta fara Serving din shi,wata hadaddiyar fried rice ce tasha Vegetables don ba abunda babu na kayan hadinta sai kamshi ke tashi ta warware papern jikin serving spoon din ta fara zuba mashi,ta kusa zuba rabin plate din yace "Is okey.." wani kallo hajiya tayi mashi kana tace da Sauden k'ara masa,"To sauden tace, ta k'ara zuba one spoon tana kokarin karawa..."Ya isa! Yace da dan hanzari waigawa yayi ya kalli hajiar yace "In ta cika man karshe barinshi zanyi ne" ta6e baki hajia tayi tace "kai dai ka sani" d'an murmushi yayi ya juya ga abincin lokacin saude ta rufe warmer din ta bud'e bowl din wanda yake dauke da pepper chicken kamshin sa ba'a magana ta debo wata katuwar cinya ta daura masa a gefe tana kokarin kara masa ya dan d'aga mata hannu alamar ya isa,hajia dai na kallon shi ya d'ago suka had'a ido "Uhm" tace ta juya mashi k'eya,
d'ayan plate din da ta rufo wanda ta zuba mashi abinci ta rufe bowl din da shi ta warware cokullan wanda Spoon ne da Fork ta sa mashi cikin abincin,mik'ewa tayi tace "Wane lemu zan kawo" yad'an daga hannu yace"Just water"
Hajia tace" Ai mu bamu da lemun da ya saba sha" tayi maganar tana ta6e baki" Zan d'auka in zan fita" yace lokacin kuma ya fara cin abincin sa, "Coleslow din ya kare ne?" Hajia ta tambaya,Saude tace "A'a yanzu zan kawo masa da ruwan"
"Just bring the water" yace,hajia tace "kawo masa ruwan kawai,"Toh" Saude tace ta juya don daukko ruwan,Bottled water ne da Acrylic cup ta kawo masa d'ora su tayi gefen tray din ta d'ago,"Thanks" yace,da alama halinsa ne duk akai masa abu yace thanks,"A ci lpy" Saude tace ta juya ciki,
Cikin natsuwa yake cin abincin,hajia ce ta fara magana"Wai yanzu har ka fita d'aga karfen?
Yar daria yayi yace "Nifa ba daga karfe kawai nike ba duk wani abu na motsa jiki wanda naga ina ra'ayi ina yi,wani lokacin ma ball nike bugawa," "Ball? ai nayi zaton ka daina ta tuntuni" yace "Eh na daina football amman inayin Basket ko Volleyball Har Badminton ma in ina ra'ayi" ya karasa maganar lokacin ya kai abinci bakinsa,
Ajiyar zuciya tayi,tad'an tur6une fuska tace,
"To kad'an huta yau mana tunda yamma tayi sosae" ta fada tana kallonsa,sai da ya cinye abincin dake a bakinsa yace "So kike in kasa bacci yau,kinsan fa I'm addicted to it" shiru tadan yi kafin taci gaba,
"Turawan nan duk sun lalata ka,da duk baka wadannan abubuwan inaga kwallon kafa ce kawae ka ke yi itama kace wai ka bari" Murmushi yayi yace "Sun dai gyara ni,Exercise ai is very² important.....har lafia ma mutum yafi in yana yi,yanxu kinga zan iya d'aukanki a hannuwana bama goyo ba inta yawo dake ko'ina batare dana gaji ba,Wani irin kallo tayi masa tace "Tunda ga jaririya ba" yar dariya yayi taci gaba,
"To mi zai hana ka rika yi nan cikin gida tunda akwai wadataccan fili dama kuma naga ai akwae kayan motsa jikin a can G.R.A ko? Kaga kasamu lokacin kanka," yace" No!a Gymnasium yafi dadi cikin sauran players anan dawa zan rika yi,ko ke? dan ta6e baki tayi kafin taci gaba,
"Amman dai bada wancan gingimemen mashin din zaka fita ba ko? Ya fahimci bike dinsa take nufi,"Saboda me kika tambaya"yayi maganar yana dan yagar cinyar kazar da ya d'aukko da fork,tace "hakanan nidai bani son mashin din wllh,baida wani Amfani," dariya ya d'an yi yace "Da baida amfani ayi shi sweethrt...." "to ai nidae had'arin shi kawae na sani, Shifa ya kusa kashe dan gidan tsohon shugaban k'asa da kyar ya rayu,an ma ce sai da akasa masa k'arafa a cikin kai fa" Tana maganar fuskarta dauke da damuwa,
taci gaba "ga yaron nan dan gidan Honorable Dalhatu Mande wanda ya mutu can kwanaki shima fa bike dinne ya kadashi kwanya waje haka aka tattaro shi nasan duk da lokacin baka k'asar bazaka rasa jin labarin ba a social media ko? Gyara zama yayi ya aje sauran naman yace "Ai nama san shi munyi junior secondary tare duk da dai mu muna a gaban su,nasan lokacin da ya fad'i da bike din....." da sauri Hajia ta rik'e ha6a tana salati "Yanzu duk da haka shine ka zuba uban kudi naira na gugan naira,har naira million biyar ka jajibo mana masifa!" Shi dai kallon ta kawae yake "To gaskia ni bana son mashin din nan wllh don aduk lokacin da ka fita dashi hankali na mugun tashi yake har sai naga kadawo nike samun natsuwa to wllh asan yadda za'ai dashi gaskia,hakanan mutum ya zuba mak'udan kudi ya siyo ajalinshi ina dalili" ta k'arasa maganar tana watsa hannuwa.
"Yanzu ya kike son ayi dashi? da sauri tace"A sayar dashi kawae don bana ce aba wani ba tunda ba mashin din arziki bane inma kai baka da abunda zakai da kudin ni kaban ina da abunda zanyi dasu"
Ajiyar zuciya yayi kafin yace " ke mi zaki yi da kudi? da sauri tace"Yo in zuba a Organization din mu mana kudi na yawa ne a wannan wurin ai kullum buk'atar su ake ba kaman yanzu da mutane ke fama kaga kaima ka samu lada kuma an kawo karshen wancan dirkeken mashin din maras Amfani.

D'an ta6e baki yayi yace"In dai kina bukatar kudi ne ki gaya man na baki,Amman maganar saida bike din can bata taso ba,kinsani bana siyan abu in kuma saida,In har na mallaki abu to fa sai dai na bayar badai saidawa ba" ya karasa hadi da d'an girgiza kai,yaci gaba,
"kuma ma ni inason abuna that was why I bought it all the way from US" yayi maganar on serious note,Hajiya tace "Nima ba don had'arin shi ba bazance ka sayar ba,kawai dai ina gudun wani mummunan abu ya faru da kai ne ba fata nike ba" Maida jikinta tayi ta jingina da kujerar,fuskarta har lokacin da damuwa,
Tissue ya yago daga saman table din da telephone yake ya fara goge hannu,kallonshi hajiya tayi sai kuma takai dubanta cikin Plate din abincin da ya ci,ya cinye saidai yabar d'an saura kaman yadda dai yan gayu ke yi,naman dai ne yaci rabi yabar saura.
"Yanxu cinyar kazar ma bazaka iya cinyewa ba? "Na k'oshi ne" ya bata amsa "To da ka barta waye zai ci sauranka" "Ke mana" ya bata amsa a takaice.
ta6e baki tayi,tadan d'ago daga jikin kujerar "Ni kam bazan ci ba kai zaka ci......."bata samu damar karasa maganar ba saboda sauran naman daya dauka ya tura mata a baki ya rike kanta da hannu daya sai kace ya rike karamar yarinya,bugun hannunshi ta fara yi tana kiran"HAISAM! HAISAM!,mi kake yi hakane" baki cunkushe da nama take maganar,bai kyale taba har saida ya tura mata ita duka ya mik'e yana daria "Ba gashi ansamu wanda ya cinye saura na d'in ba" baki cunkushe da nama tana taunawa take harararsa,duk'awa yayi a gabanta ya kama dukkan hannuwanta sai kace wasu Saurayi da Budurwa,koda yake a hak'ikanin gaskia suma cikakkun masoyan juna ne suna kaunar junansu sosai,suna sa junansu yin abu,haka suna hana junansu,ya fara magana cikin nutsuwa"Nasan don kin damu da ni ne that was why kike zullumin kada bike nima ya kasheni..."dan murmushi yayi kafin yaci gaba "Itafa mutuwar nan d'aya ce sweethrt sabubbanta kuma da yawa,so don ina hawa bike ba yana nufin dole shine zai kashe ni ba ko ya lahanta ni kaman yadda yayi ma wasu,Kowa akwai silar Ajalinsa wasu ma hakanan suna a kwance ko a zaune suke mutuwa,kamar dai yadda kike zaune din nan sai kiga na hau bike din naje na dawo lapia ke kuma kin mutu a zaunen...." da sauri ta tsaya da taunar naman da take tana mashi wani kallo,Daria yake sosai ganin yadda ta yi, lokacin ya mike ya nufi dining area gaban Handbasin ya tara hannuwansa yana wankewa kafin ya bude k'atowar Deep Freezer din dake jikin bangon kitchen ya d'aukko Canned Coke ya rufe,"I know why u look all worried,saboda wancan tsohon ne" ya fad'a yana nuna k'aton hoton wani mutum da Coke din hannunsa dake a gidan saman da Plasma t.v take,sanye yake da kakin Sojoji babban mutum ne sosai kayan sun kar6i jikinsa yana da kyau ba laifi ga dogon hanci,kalar fatar shi kuwa za'a iya kiranshi da wankan tarwada wato shi ba bak'i ba,ba kuma fari ba,daga kasan hoton anyi rubutu kaman haka,GEN. ADAMU ZAKEE,daga k'asan rubutun kuma shekarun daya dauka a raye ne zuwa shekarar daya mutu,kallon hoton hajia take da wani irin yanayi kafin ta juyo da kallonta kan Haisam wanda yake kokarin fita,d'an murmushi tayi sam ba walwala a tare da ita tace,"Take good care of ur self for me,pls banda tuk'in gangancii".
"Don't worry beb zan dawo lapia,ba yanxu zan mutu ba...tare ma zamu mutun amman sai nayi aure,nayi ya'ya harda jikoki kaman ke,da nayi Achieving all my goals,then sai mu mutun" Ya karasa maganar yanata faman daria adaidai lokacin kuma ya kai bakin kofan fita...da dan d'aga murya hajiyan tace kace sai nazama leda kenan" Daria sukai su duka,a lokacin kuma ya fice,ita kuma hajia ta maida dubanta kan hoton sojan mutumin nan tana girgiza kai,
A yanayin Haisam bazaka ta6a tunanin za'ai wannan dogon hiran dashi ba don kallo daya zakai mashi ka yanke cewa irin miskilan mazan nan ne, masu ji da kai,kuma hakan ne don ba kowa yake sake mawa ba yayi fira haka,sai mutanen da ya shak'u dasu sosae suma d'in sai yana jin yin firan,Amman tsakaninsa da hajiyansa wannan ko yaushe yana da lokacinta kaman yadda itama hakan yake a wurinta.

*💖ASANADIN MAKWABTAKA💖*
Chapter 7 · 0% Book details