← Book details Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 130 OF 137

Sashe 130

Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"What are u doing here?" ta tambaya, Fatun tai mata banza tana binta da ido ta k'ara cewa "am i not talking to u, why can't u sit in ur House, kullum ke kina gidan mutane ne?" sai lokacin Fatun tace "to ai ba wurin ki nazo ba ko wurin ya...." kafin ta idasa Maganar ta daka mata tsawa "Oh u shut up! Is he ur Father, babanki ne shi ko kin had'a wani abu dashi" ta tambaya ta kumburo baki tana huci haka itama Fatun ta kumburo baki jin abunda tace mata, nuna mata hanyar fita tayi tace "leave here now,mai kwad'ayi kawae baki iya tsayawa gidanku kullum kina gidan Mutane k'wak'wa, i don't wanna see u in dis house again" waro ido Fatun tayi baki bud'e take kallonta jin ta kirata da mai kwad'ayi da kwakwa lokaci guda idanunta suka sauya kala tsantsan bacin rai ne acikinsu sam tama kasa maida mata martani duk da yadda Maganar ta daketa kirjinta har wani d'agawa yake da sauri da sauri,
"I said leave before i......." tsit tayi bata k'arasa ba sakamakon jin k'arar bud'e kopar Falon Haisam ta d'aga ido ta kalli saitin kopar, shine ya fito cikin shirin zuwa gym bin su yayi da ido yana tunkaro su ya tsaya a yar matattakalar ba tare daya idasa saukkowa k'asan ba, kallon Fatuu data sadda kai yay kafin ya d'ago ya kalli Farha data tamke fuska hakan ya tabbatar mashi da akwae abunda ke faruwa,
What's happening here?" ya tambaya idonshi akan Farhar, shiru tayi ta d'an kauda kai tana tura baki, maida idonshi yay kan Fatuu yace "Zarah" da karyayyar murya ta amsa mashi yace "mike faruwa ne" girgiza mashi kai tayi alamar ba komae sam bai yarda ba ya sake tambayar Farha itama tace ba komae, shiru ya d'anyi yana nazarinsu gaba d'aya, a kausashe yace "Zarah tell me miye ne!" aikuwa kaman tana jira ta fashe da matsanancin kuka wanda daga jin sautinshi zaka fahimci tana cikin bacin rai, d'agowa yay yayi ma Farha kallon tuhuma kafin ya idasa sauka ya tsaya agaban Fatun ya kirata ta amsa yace ta d'ago ta gaya mashi abunda tayi mata, d'agowa tayi idanunta sunyi jawur cikin kuka ta fara fad'i mashi aikuwa tun kafin ta k'arasa ya juya yana ma Farha wani kallo fuska a matukar d'aure yace "Why, Why Farha!" tana tura baki tace "this is not their House so ta tsaya a gidansu mana zatai ta zuwa ma Mutane gida" takaici ne ya turnuke shi har baisan lokacin daya daka mata tsawa ba yace "shut up and leave my sight" wani kallo ta bishi dashi ya kara daka mata tsawa yace "i said leave else i will slap u!" d'an zaro ido tayi da alamun mamaki tace "u will slap me Ya Haisam because of dis pauper?" wani Murmushin takaici yayi ya jinjina kai had'i da maimaita kalmar pauper data kira Fatun da ita kafin yace "then isn't she a human being?" ya tambaya had'i da d'age gira jin tayi mashi shiru yasa ya fara moving inda take yana maimaita abunda yace mata "ki gaya man ita ba Mutum bace saboda talaka ce?" ganin yadda yake Maganar cike da 6acin rai yasa ta fara ja da baya kafin ta juya gaba d'aya ta nufi hanyar fita shi kuma yaja ya tsaya yana kallonta tana zuwa bakin fence door ta tsaya ta juyo tayi mashi wata magana da shi kad'ai yaji mi tace daga haka ta fuce, d'an guntun tsoki yaja jin abunda tace sai yanzu ya gane dalilin da yasa tayi ma Fatun haka juyowa yay ya kalleta ta fara kokarin bi ta gabanshi zata wuce yace mata su shiga ciki, d'agowa tayi ta kalleshi ya jinjina mata kai hakan yasa ta wuce gaba yana bayanta suka shiga cikin Parlon, armchair ya nuna mata yace ta zauna ta zauna sai faman sheshsheka take, wucewa yay ya nufi frigde ya d'aukko lemu fanta da cup ya dawo shima ya zauna akan d'ayar armchair d'in ta kusa da ita ya bud'e lemun ya tsiyaya acikin cup ya mik'e ya ajiye robar kan c-table kafin ya dawo ya mik'a mata, d'agowa tayi ta kalleshi ya d'an lumshe mata idanu alamar ta amsa maimakon ta amsan sai kawae ta k'ara fashewa da kuka tana Fad'in "wllh na rantse da Allah Ya Handsome ni ba kwad'ayi da kwakwa nike zuwa ba" d'an cije baki yay sam baison jin Maganar ma don yasan tana yi mata ciwo sosae saboda bai manta da labarin wadda tayi mata gorin kallo ba da ta ta6a bashi tun lokacin ya fahimci irin hakan na mata ciwo, shiru yay yana kallonta tana ta faman kuka fuskarta tayi jaga jaga da hawaye ga idanunta sunyi ja, Calmly ya fara Magana idanunshi akanta "i know who's Zarah, so i will never think of dat, ki daina damun kanki akan hakan ki manta kawae ita haka halinta yake ne kawae don ta 6ata maki rai tayi maki wannan Maganar but ni nasan ba haka halinki yake ba" da sauri ta kalleshi da jajayen idanu murya na rawa tace "to su sauran fa?" d'an Murmushi yay yace "suma bazasu yi maki kallon hakan ba don ba halinsu d'aya ba su zasu d'auke ki kaman sis nasu" shiru tayi tana kallonshi ya jinjina mata kai alamar tabbatar mata da abunda ya fadan kafin ya sake mik'a mata lemun ta amsa ta d'an kur6a daga haka ta mik'e ta aje kan c-table ta kalleshi tace mashi zata tafi gida, shiru ya danyi yana kallon face d'inta kaman mai nazarin wani abu kafin ya d'aga mata kan alamar to har ta kama kopar zata bud'e ya kirata ta juyo yace "am so sorry and am apologizing on her behalf" shiru ta d'an yi sai kuma ta jinjina mashi kai daga haka ta fuce, zaune yay a wurin ya d'age kanshi sama na d'an wani lokaci kafin ya mik'e ya nufi hanyar Bedroom, ruke da jakarshi ya fito ya fita daga falon da farko da ya fito lokacin da yaga su Fatun part d'in Hajiya zaije yaci abinci amman yanzu yana fitowa Parking space ya nufa kawae ya hau bike dinsa ya fice, Hajiya na zaune a Falo hannunta ruke da Al'qurani idanunta na sanye cikin gilashi ta jiyo k'arar bike d'inshi,lokacin data kai karshen ayar da take cikin karantawa ta d'ago ta kalli Farha dake Facing dinta ta juya tana lek'en Haisam d'in ta window tace "Fita yayi kenan ba tare daya zo yaci abinci ba" juyowa Farhar tayi ta kalleta ta d'an ta6e baki daga haka ta mik'e ta nufi hanyar Bedroom. Koda Fatuu ta koma gida bata gaya ma kowa abunda ya faru ba dama kuma gwaggon ta tafi aiki taja bakinta tayi shiru saidae acan k'asan ranta tana jin zafin Maganar sosae ba kamar dayake bata rama ba.

Ranar Alhamis bayan Azahar duk suna zaune kan dining suna cin abinci banda haisam da bai kaiga dawowa ba Jidderh ta kalli Hajiya tace "wai nikam hajjaju ya akai kwana biyu yar gidan Ya Handsome bata zo ba ko dama ba ko yaushe take zuwa ba?" saida ta idasa cinye abincin dake cikin bakinta ta ajiye cokalin kafin tace "wllh kin riga ni ne a baki amman abun na raina ace yau har kwana ukku bata zo ba inata so in maganta kwana biyu da ba zaune nike ba shiyasa nama yi zaton ko tazo ban nan ne" girgiza mata kai jidderh tayi alamar a'a Hajiyar tace "to Allah dae yasa lafiya" tana rufe baki Nameer yace"Lafiyarta lau ko jiya naje gidansu mun gaisa da granny dinta" sai lokacin Farha ta d'ago tayi mashi wani kallon mamaki Hajiya tace "shanshani ashe har kasan gidansu kana ma zuwa kenan" murmushi yay gaba d'aya dimples d'inshi suka lotsa yace "Ran Monday da tazo na rakata ne naga gidan har muka gaisa da Uncle d'inta mai kiosk so wurinshi nike zuwa fira shine har na shiga cikin gidan" jinjina kai Hajiya tayi Jidderh tace "to muma zamu je mu gaisa",
"haka yakamata kuje ku gaishe da kakarta har ku gano mana ita kuji ya akai bamu ganta ba kwana biyu" Hajiya na rufe bakinta Jidderh ta mike su twins ma suka saukko daga kan dining chair alamar suma zasu je kallon Farha tayi ganin yadda ta wani tamke fuska yasa bata ce mata komae ba ta nufi cikin falon Nameer na mata kwatancen gidan yace ko tayi ma Officer Magana zai nuna masu tace to, dama akwae gyale akanta don bata cika son zama ba kallabi ba suka fuce, suna fitowa bakin gate tayi ma Officer Magana ya tashi ya rako su har wurin kiosk d'in Amadu ya nuna masu gidan yayi masu adawo lafiya yana daga ma su twins hannu suma suna d'aga mashi, a bakin kiosk d'in ta tsaya ta gaida Amadu yana ganinta ya washe baki yana amsawa tace mashi sunzo gun Zarah ne ko tana nan yace eh bari ya rakasu ciki ya fito yay masu jagora yana gaba suna biye dashi har bakin kopar d'akin Fatun ya d'aga labulen baiwar Allah tana kwance kan gado tunda ta daina zuwa gidan Hajiya take jinta kaman bata lafiya ko gidansu Haulat ta daina zuwa duka sau d'aya taje shima kasa zama tayi ta dawo gida saidae taita kwanciya a d'aki har gwaggo ta gano akwai abunda ke damunta taita tambayarta amman sai tace mata ba komai,
Chapter 130 · 0% Book details