← Book details Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 137

Sashe 47

Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Juyawa tayi ta kalli haisam dake danna wayarsa ya d'an kishingida hadi da mikar da kafafunsa saman kujeran sai kuma ta saci kallon hajiyan ganin ta maida hankalinta kan tv yasa ta mik'e taje gabanshi a hankali kaman mai rad'a tace"in kawo maka fruit d'in?" ba tare da ya kalleta ba ya d'aga mata kai alamar eh,juyawa tayi ta nufi hanyar kitchen,sai da ta bud'e freezer ta fiddo ledan kafin ta shige cikin kicin din,a saman plate mai dan fad'i ta jero mashi bayan ta cire bawon su ta yayyanka amman bata yanka Apple d'in ba,yadda ta jera su sunyi gwanin sha'awa.

Gefen kujeran da haisam yake ta aje kafin ta juya ta kinkimo sofa table hakanne yajawo hankalin hajiya kanta ta bita da ido ganin abunda take,gaban Haisam ta aje table d'in ta daukko plate din fruit din ta d'aura,fuskarta d'auke da d'an murmushi bayan ta mik'e tace"Yaya handsome gashi nan"sai lokacin ya juyo ya kalli fruit din kafin ya d'aga kai ya kalleta shima murmushin yayi ahankali yace"thanks",
hajiya da ta saki baki tana kallonsu tace"ina aka samu fruit ko Tk ya dawo ne?shi naba sakon ya taho dasu d'azun da nace Saude ta had'a man fruit salad take sanar dani sun k'are",

juyowa fatuu tayi ta dawo wurin hajiyan ta zauna"ba shi bane wannan na Yaya handsome ne",
"toh yaya handsome kuma?" hajiya ta tambaya,kai fatuu ta daga mata alamar eh,juyawa tayi ta kalli haisam wanda gabadaya hankalinshi na akan wayansa da alama chatting yake sai faman Murmushi yake tace"kai ka zo da ftuit dinne?" Kafin ya bata amsa fatuu ta amshe"ni na kawo masa abun ciwo ne,baki ga bai lpy ba" da mamaki hajiya ta kalleta"ke kika kawo masa?" jinjina mata kae fatuu tayi alamar eh sai kyakkyafta idanu take hajiya tace"daman kinsan Haisam ne?",
"Eh mana baki ji har sunanshi na fad'i ba" dan ta6e baki hajiya tayi sai kuma tace"amman baki ta6a ceman kin sanshi ba,shi dae nasan magana bata dame shi ba daman ba lalle ya fad'a man ya sanki ba..." da sauri fatuu ta tari numfashinta"to nima ai ina da sirri ko" bud'e idanu hajiya tayi cike da mamakin maganar fatuu tace"ah lalle kam ni shaida ce,amman yaushe kika san ya samu raunin ne?naga jiya da dare ya hadu da tsautsayin" wuki wuki da idanu fatuu tayi ganin kaman hajiyan nason ganota,turo baki tayi tace"kai hajiya bafa kyau zurfafa bincike nasan kin sani,nace maki na sanshi baki ji ma yaya nike ce masa ba,ai d'azun bayan na dawo boko nazo shine naga bai lafiya to ban shigo nan ba saboda lokacin islamiyya yayi shine fa na tafi" jinjina kae hajiyan tayi alamar gamsuwa,

Kallon Haisam tayi ganin hankalinshi na akan waya bai shan fruit din tace"Yaya handsome kasha mana" ta6e baki hajiya tayi"uhmm karma ki wahalar da bakinki...." maido idanunta tayi kan hajiya"bai shan fruit ne?"ta tambayaa,
"Yana sha amman shi fa komae sai an matsa masa yake ci kaman wani k'aramin yaro,kwata-kwata baison cin abinci ina ga dae tsukakkun yan hanji ne dashi" zaro ido fatuu tayi ta juya ta kalleshi har lokacin idonsa na kan wayar tamkar bai jin abunda ma suke cewa,hajiya taci gaba"kinga dae yadda yake k'ato tubarkallah, kamata yayi ace yana cin abinci hannu baka hannu kwarya,amman sam baison cin abinci k'irar tasa duk bogi ce ta k'arfe ce,yanzu fa inda zai sha fruit dinnan to wllh kina iya ganin ba lalle ya k'ara cin wani abu ba da daren nan,k'ilan sai dae ko tea da biscuit ko snacks,yafa iya yan ciye ciye maras amfani shi ga bature", ta k'arasa tana turo baki, daman rashin cin abincin nashi na damunta,ita kam fatuu tsura mashi ido tayi tana tunani cikin ranta"ashe abubuwan da ya bata d'azun sune abincin shi bai son cin abinci.."ji yayi ajikinshi idanu na yawo akansa hakan yasa ya juyo ya d'an kalleta tana ganin sun had'a ido tayi masa alamun ya sha fruit d'in da hannu tana yamutsa fuska,wani kallo yayi mata mai kama da harara ya juya yaci gaba da lallatsa wayansa.

A hankali yasa hannu ya d'auki Apple d'in ya kai bakinsa ya gatsa,lokaci guda fatuu dake kallonshi ta saki Murmushin jin dadi dama tasan zai so Apple d'in tunda shi d'an gayu ne shiyasa ta matsa sai da mai kayan marmarin yasa dashi,juyo idanunsa yayi ya kalleta, washe baki tayi tana dariya hakan yasa ya d'an mata side chuck kafin ya mayar da kanshi kan wayar yana ci gaba da cin Apple d'in,
"U have a message" Haisam ne yayi maganar,juyowa hajiya tayi tace"sak'on mi?" batare da ya bata amsa ba ya d'an d'aga mata wayarshi lokaci guda wata zazzakar murya ta fara magana,_"Hi Granny!how are u,kin manta dani ko?"_ daga yadda mai muryan tayi magana da hausa zaka fahimci hausar tata bata nuna ba sosae,
lokaci guda hajiya dake kallon haisam ta washe baki tana fad'in"Allah sarki Fanan,ai in dae na manta dake na manta da kaina kenan,kira man ita don Allah in wanke kaina" sauke wayan yayi ya fara kokarin kiran fanan d'in,tana fara ringing haisam ya kalli fatuu yayi mata alamar tazo ta amshi wayan ta mik'a ma hajiyan,tasowa tayi ta kar6i wayan kaman yadda ya mata umarni,hajiya na amsa aka d'aga kiran suka fara waya da Fanan din,

A hankali fatuu ta mik'e ta nufo wurin da haisam ke zaune,tsayawa tayi daga gefe tana kallonshi had'i da yin d'an murmushi,hannu yasa ya daukko ayaba yakai bakinsa yad'an gatseta kafin ya d'ago idanunsa ya kalli fatuu dake atsaye,sauke kafansa guda k'asa yayi d'ayar kuma mai ciwon ya mik'ar da ita kan kujeran,kallonta ya sake yi yace"Seat" a hankali ta zauna d'ayan 6arin kujeran ta d'aura hannunta d'aya kan hannun kujeran tayi tagumi dashi har lokacin da Murmushi akan fuskarta,ci gaba da shan fruit din yayi idonsa akan tv can suka had'a ido da ita,ganin tana ta kallonshi ne yasa shi tunanin ko fruit d'in take so ne,ita kuma yadda yake sha ne abun yayi mata dad'i tayi zaton ba zai sha ba kaman yadda hajiya tace,

d'aukko plate d'in fruit din yayi ya aje agabansa ta yadda ya kasance atsakiyansu kenan,kallonta yayi a hankali yace"eat"da sauri ta girgiza mashi kai"ni da na kawo maka kuma sai in shanye ma" yar harara ya wurga mata"what did i told u yesterday?ba nace in nace kiyi abu ba kawae kiyi"ganin yadda yayi mata maganan yasata saurin cewa"yi hakuri to"hannu takae ta d'aukko 6allin kankana ta fara sha tana satar kallonshi,shikam hankalinshi na kan tv,duk wannan abun hajiya na akan waya sai faman hira suke da Fanan din da aka kira mata,

Hannu fatuu ta kai zata d'auki fruit carab Haisam yaji ta kama yatsan hannunshi,da sauri ya kae idonshi kan hannunta dake ruke da yatsan nasa,da mamaki ya d'ago ya kalleta sam hankalinta na akan tv da ake Indian film,batama san ta kama yatsan nasa ba,jan yatsan ta fara duk a tunaninta fruit d'inne,jin yaki daukuwa yasa ta juyo takai idonta kan fruit din,zaro ido tayi ganin ta kama yatsan Haisam,da sauri ta saki ta dago suka had'a ido dashi a rude tasa tafin hannun damanta ta rufe baki tana girgiza masa kae alamar batasan tayi ba,cire hannun tayi tana kokarin yin magana ya dakatar da ita da hannunshi,cigaba yayi da shan fruit din yana kallo,ganin haka yasa itama taci gaba da sha tana kallon sai dae duk in zata dauka sai ta juyo ta kalli fruit d'in gudun karta k'ara ruke masa yatsa,

Juyowa hajiya tayi bayan ta gama wayan ta kallesu, mamaki ta shiga yi cikin ranta na yadda akae suka san juna haka,shidae haisam tasan ba mai shiga harkar mutane bane balle kuma yarinya kaman fatuu,tunowa da halin fatun na sam bata jin magana kuma bata da shariya sannan tana da saurin shiga ran mutum yasa ta kawar da mamakin,

"Abun yar wariyar launin fata ce kenan" hajiya ce tayi masu maganar,juyowa fatuu tayi ta kalleta tana dariya hajiyar taci gaba"wato don kun ganku farare shiyasa ni bak'a aka ware ni ko"sosae fatun ke dariya,shima haisam d'in da idonsa ke akan tv d'an murmushin gefe yayi jin abunda hajiyan ke cewa,fatuu tace"ai akwae saura a kitchen in kawo maki ne?" kafin hajiyan ta bata amsa haisam ya maida dubansa kan fatuu da ta juyo ta kalleshi tana dariyar maganar hajiya"d'auka kikae mata" da sauri tace"da gaske fa akwae saura bari in..." katseta yayi"ki kai mata wannan na koshi" sukuku tayi da fuska ganin haka yace"zan sha sauran anjima" yayi maganar idanunsa ad'an lumshe,mik'ewa tayi ta dauki plate din ta nufi wurin hajiyan,

"Sauranku zaku ban in sha don kun raina ni ko" d'an murmushi fatuu tayi"to ai shi yace in kawo maki ya koshi"ta aje plate din a gefen hajiyan itama ta raku6a gefe ta zauna,hannu hajiya takai ta fara shan fruit din,itama fatun tasa hannu zata ci gaba da sha,da sauri hajiya tace "a'a sauran ma bazaki barman ba,ke baki koshin bane?"dariya fatuu tasa ta jingina kanta da kujeran,atare suke shan fruit d'in suna kallon Indian film d'in da ake a Bollywood da alama yana masu kyau ne,

Haisam ne ya fara k'okarin gyara kafarsa mai ciwo jin ta sage masa,hakanne ya jawo hankalinsu kanshi,
"Sannu kabi a hankali" hajiyace tayi maganar,d'aga mata kai kawae yayi taci gaba da magana"ni wllh har yanzu mamakin yadda ka taka wai kwalba nike,muda ko lemun kwalba bama amfani dashi,in kaga kwalba a gidan nan sai ta turare ko tasu salad cream su kuma wannan dama iyakarsu cikin kicin ne,da sun k'are kuma sai cikin dustbin amman sai gashi wae ka taka kwalba a part d'inka,abun ya d'aure mun kai,wae ko dai ka fita waje ne?" ta k'arasa maganar idonta akan haisam tana jiran ya bata amsa,fatuu kau gaba d'aya ta zaro idanu ganin kaman hajiyan nason gano gaskia,
Chapter 47 · 0% Book details