Sashe 114
Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Lokacin da su Abbas suka k'arasa gidan Najeeb dake a Gra wanda katon gidane na gaske, sosae yay farinciki da zuwan nasu haka ma Matarshi Sofeeyat wadda irin matan nan ne da suka waye over tana da kyau daidai gwargwado kuma tana da haske saidae kana gani kasan hasken harda na kanti, taci gayu cikin k'ananan kaya wando da riga sun kamata hakan ya bayyanar da d'an dirin dake gareta, kanta anyi mata kitson k'arin gashi miri miri amman yay kyau sosae ta d'aura bak'in veil ta zameshi daga gaban yadda kitson ya fito sosae haka k'umbunanta an k'ara mata dana kanti shima Najeeb d'in yana sanye da kayan shan iska armless da wando 3 quarter,suna shiga cikin tangamemen falon wanda yake shak'e da kayan alatu suka zauna asaman d'uma d'uman sofas d'in dake kewaye acikinsa set biyu, zama itama soffyn tayi tana facing d'insu cike da kisisina ta shiga gaidasu idonta akan Haisam amman Abbas ne kawae ya kalleta shikam Haisam bai ko kalleta ba ya amsa mata a takaice,
"H,zakee manyan gari ashe ka dawo nan da aiki rannan My ke gayaman" ta fad'a cike da salo, shiru bai ce mata komae ba da alamu ma bai jita bane don ya sadda kanshi yana danna wayansa, d'an ta6a shi Abbas yay yace mashi ana magana sannan ya d'ago ya kalleshi kafin yace wani abu ta k'ara cewa "da alama ta janye mashi hankali ne" kallonta ya d'anyi da d'an Murmushi ba tare daya ce wani abu ba, Najeeb ne yace tasa akawo masu drinks mana tace dama yanzu zata sa ta bari su gama gaisawa ne, mai aikinta ta fara kwalama kira "Murja,Murja" ta kirata har sau biyu sannan ta fito yar dattijuwar mata ce in a auren k'auye mane zata haifeta,
"Baki ji anyi baki bane" ta fad'a ta d'aure fuska had'i da d'aura kafa d'aya kan daya, murya na rawa Murjar tace "ayi man afuwa Hajiya ina can ciki ne banji shigowarsu ba" shiru ta d'anyi kafin cike da bada umarni tace taje ta kawo masu abun sha kuma ta shirya abinci akan table Abbas na jin hakan yace "adai bamu abun shan amman abincin dae abarshi basai an shirya ba....." katseshi Najeeb yay "kana nufin bazaku ci abincin gidana ba?" yar dariya yayi yace "ba haka bane kaima kasan by dis time mutum yaci lunch so duk a k'oshe muke" d'an ta6e baki yayi baice mashi komae ba adaidai lokacin murja ta karaso ruk'e da babban tray ta d'auro bottle water da drinks da glass cups, daurashi tayi kan c-table kafin ta kinkimeshi da k'yar don murtukeke ne ta matsar masu dashi gabansu, tana shirin juyawa ta tafi aikuwa soffy ta daka mata tsawa tace "wai ke dak'ik'iyan inane,da kika aje masu waye bawanki da zai zuba masu?" har saida ta d'an tsorata jiki na kerma ta hau bata hakuri ta juya zata zuba masu Abbas yace ta barshi zasu zuba shidae haisam baima d'ago ba balle ya kallesu saidae yaji tsawar da tayi matan har cikin ranshi don ya tsani wulak'anta dan'adam don shi a wurinshi duk d'aya muke,tsaye Murjar tayi tana binta da ido ta kasa tafiya ita kuma Soffyn taba banza ajiyarta sai juya k'afa take tana wani shan kamshi, a hankali Haisam yay ma soffyn kallon kasan ido cikin sa'a suka had'a ido don dama bunu bunu sai ta kalleshi, ganin kallon da yayi mata ne yasa tasha jini jinkinta ta kalli murjar tace taje amman karta shirya table d'in ta kawo masu abunda zasu ta6a ta amsa da to harda dan rissinawa tayi mata godiya soffyn ta d'aga mata kai kafin ta juya ta tafi, bada jimawa ba ta dawo d'auke da wani hadaddan trayn ta d'auro plates d'in soyayyan naman kaza da kuma na snacks ta aje masu gefe tayi masu aci lafiya gaba daya harda haisam suka d'aga mata kai, fira suka shiga yi ganin haisam bai ta6a komae ba yasa Soffy yunk'urawa tana fad'in "kunsan fa H,zakee saraki ne bari nai serving nashi" dakatar da ita yayi ta hanyar d'aga mata hannu kafin yace ba yanzu zai ci ba, bata san shi k'yamar k'umbunan hannunta ma yake ba, tana zama wayanta ya fara ringing alamar ana kiranta mik'ewa tayi tace masu "excuse me" Abbas ne ya d'aga mata kai ta nufi ciki tana wani karairaiya jiki ba kunya ba tsoron Allah, suna cikin hiran Najeeb ya kalli Haisam yace "H,zakee ina Mom d'inka bafullatana?? Kafin ya bashi amsa cike da tsokana Abbas yace "aikuwa kasan tana gidana ya kawota da har nace mashi mu taho tare ku gaisa" Najeeb yace "halan yak'i ko?" dariya Abbas d'in yasa yace "nidae ai baka ji na fad'i haka ba" d'an ta6e baki kawae yay baice komae ba, hira suka cigaba da yi har aka kira sallar la'asar sukaje masallaci suka yo salla suna dawowa suka ce bazasu shiga ciki ba zasu je wurin Saleem ne Najeeb na jin haka yace su jira su tafi tare ya nufi cikin gidan yana fad'in bazasu yi sallama da soffy ba Abbas yace ya gaya mata sun wuce, bayan wani lokaci ya fito sanye cikin jeans da t-shirt hannunshi ruke da wayarshi yasa bak'in glass ya fito a d'an madararshi, yana k'arasawa wurunsu suka shiga cikin Motar suka fuce, Bayan sunje har wurin Mahaifiyar Saleem d'in sukaje suka gaidata kafin suka shiga part d'inshi sai karfe biyar da wani abu suka baro wurin Saleem d'in Abbas ya tambayi Najeeb gida zasuyi dropping nashi ne dayake shi ke tuk'a Motar Haisam na gefenshi sai Najeeb d'in a baya, ce mashi yay su wuce gidanshi ya gaisa da Feenah, Murmushi kawae Abbas yayi don yasan ba wata Feenah kawae Zarah yake son gani, lokacin da suka isa bakin gate d'in gidan Abbas d'inne ya fita ya bud'e gate kafin ya dawo cikin Motar ya kutsa cikin gidan, suna shiga ciki daidai lokacin Abdul ya fito da gudu sai kuma ga Fatuu ta biyo bayanshi da gudu gaba d'aya gashinta a tarwatse ya zubo mata gefe gefe da kuma bayanta, tun kafin su tsaya Najeeb ya zuba mata idanu, suna yin parking suka firfito da gudu Abdul ya nufi bayan Haisam ya 6oye yana fad'in "Baba zakee kaga Aunty Zarah zata bugeni" d'agowa yay ya kalleta tayi tsaye agabanshi ba damar ta kamo Abdul d'in cikin cool voice d'inshi ya tambayi abunda yayi mata tana tura baki tace "ba game mukeyi ba duk wanda yay winning ya bugi mutum tun d'azun nike cinyeshi amman sai yak'i bari in bugeshi kuma ni da shi yay winning na tsaya ya bugeni har ma ya cire man ribbom" still yay yana kallonta Abbas kuma sai dariya yake Najeeb ma murmushi yake don ba k'aramin burgeshi take ba ba kaman yadda ya ganta a yanzu gashi tana Magana cike da sangarta,
"Baki ga yaro ne ba kiyi hakuri" Haisam ya fad'a, tura mashi baki tayi alamar bata yi hakurin ba, ruk'o hannun Abdul d'in yayi ya dawo dashi gaba yace mashi "Say sorry to her" da sauri yace "Aunty Zarah Sorry" yayi Maganar yana dariya, harararshi tayi kawae haisam yace taje ta d'aukko Abaya dinta su tafi tace to, tana shirin juyawa Najeeb yace "yar bafullatana ba gaisuwa" dakatawa tayi ta juya ta kalleshi sai lokacin kuma tama ganshi don da duk bata lura dashi ba,ganin yana mata Murmushi yasa itama tayi mashi don ta ganeshi ta gaidashi ya amsa mata bayan ya cire glass d'in fuskarshi, nufar cikin gidan tayi Abdul yabi bayanta yana tambayarta tafiya zata yi tace mashi ehh, bada jimawa ba ta fito Feenah da Abdul na biye da ita suka k'araso wurin Motar, gaida Najeeb Feenah tayi tana cewa shine yazo gidan amman bazai shiga su gaisa ba Abbas yace kuma dama wurinta yace zai zo Najeeb d'in yace to yaga ya tafi bai shigan bane ita dae dariya kawae tayi ta mik'a ma Fatuu yar babbar ledar data ruk'o a hannunta, amsa tayi ta lek'a ciki kafin tasa hannu ta fiddo wani Material mai kyau tare da veil d'inshi can k'asa kuma kayan shafa ne wai sai ta rungume Material d'in ta mik'a mata ledar kayan shafan tace "Aunty Feenah ki bar wad'annan na d'auki wannan" d'an waro ido Feenah tayi tace "saboda me ki tafi dasu duka" tace "ai inada su da yawa Ya Handsome yana siya man" kafin tace wani abu Abbas ya riga cewa"ai na Ya Handsome daban wannan daban Mom Zarah don haka ki tafi dasu" kallon Abbas d'in tayi kafin ta kalli haisam ta d'age gira tace "in tafi dasu??" har saida tasa ya d'anyi murmushi yadda tayi mashi tambayar, ganin tayi mashi tsuru tana jiran amsa kuma kowa shi yake kallo yasa ya d'aga mata kai alamar eh, maida Material d'in tayi tace mata ta gode ta nufi Motar da sauri Abdul ya nufi Haisam yace "Baba zakee zaka k'ara kawo man ita?" kai ya d'aga mashi alamar eh ya juya gun Fatun ya kama hannunta yana tambayarta yaushe zata dawo tace sai Ya Handsome ya kara kawota daga haka ta nufi gaban Motan zata shiga Najeeb yace ta shiga baya zasu tafi tare tace to ta shiga bayan shi kuma ya shiga gaban Haisam ya zagaya side din driver ya shiga, lek'awa Abbas yay yana yi masu sallama yace ma Najeeb sai sunzo rakiya Airport, tada Motar yay su Feenah nayi ma Fatuu bye baye Abdul kamar zaiyi kuka suka fuce daga gidan........