← Book details Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 137

Sashe 59

Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tunkarar inda motar haisam take sukai bayan sun fito daga cikin station din,
"Miye case dinshi ne?" haisam ne yayi tambayar idonshi akan hanya,
"Wllh wai wannan Alhajin ne ke yin gini a unguwarsu shine yaronshi da abokinshi suka je gidan suka sace kofofi da winduna so bayan asirin yaran ya tonu an kamosu shine aka yi ma abubuwan da suka sata kudi don tuni sun salwantar dasu,to shi d'ayan yaron mahaifinshi ya biya,wannan dattijon ya rage ya biya nasu,d'azun da nazo ne na iske shi Alhajin nata korafin wai sau ukku ana mashi uzurin ya kawo bai kawo ba,lokacin dattijon bai kaiga zuwa ba" jinjina kai kawae haisam yayi a lokacin suka iso bakin motar,jingina bayanshi yayi da murfin motar ya kalli Sp,"Nawa ne kudin?"
"Gaba daya 150k ne so da aka raba kowa zai bada 70k an cire 10k" d'aga kai haisam yayi kafin ya maida idonshi kan wayarshi dake a hannunshi ya fara daddannata,
"Your Account no pls",
"U mean my account details?"Sp dake kallonshi ya tambaya,kai haisam ya daga mashi ba tare da ya d'ago ba,nan take ya fara karanto mashi acct details din,
Da sauri Sp yasa hannu cikin trouser pocket dinsa ya fiddo wayarsa jin k'arar shigowar message,duba wayar yayi da sauri ya dago ya kalli haisam"naga ka turo kudi har 200k,na minene?"
A nutse yace"kaba mutumin 150k sai ya biya kudin sauran kuma ya yi amfani dasu"daga haka ya juya yana k'okarin bude Motar,
"What about d remaining 50k,mi za'ayi da ita?",banza yayi mashi,ganin hakan yasa Sp k'ara tambayarshi don yayi tunanin ko bai ji shi bane,d'age mashi kafada yayi"i ave no idea"lokaci guda sp ya gane bashi yayi,shine ba zai iya fadi mashi hakan ba,
Girgiza kai Sp yayi" H,zakee u will never change",fuskar haisam da d'an Murmushi yace"I was born like dat"hannu Sp ya kai ya d'an bugi shoulder dinshi suka yi dariya gaba daya da alama wata sarar su ce ,godiya ya shiga yi mashi sosae shi dae bai tanka mashi ba,saima bud'e mota da yayi ya shige,
Lek'awa ciki Sp ya yi"To sabuwar ma'aikaciyarmu sai munji daga gareki ko"da fara'a yayi maganar,kai kawae fatuu dake zaune ta d'an kwantar da kanta ajikin seat ta d'aga mashi,daga haka sukayi sallama da haisam ya tashi Motar Sp na d'aga masu hannu ya jata suka tafi.

*💖A SANADIN MAKWABTAKA💖*
_*(Love and Destiny)*_

_*BY ZAINAB LALUH📲*_ ~(Oumm Imam)~

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

*_RAMADAN KAREEM_☪️*

_Allah ya kar6i ibadunmu yasa muna daga cikin yantattun bayi,Amin ya Sami'ud dua🤲_

*4️⃣3️⃣*

Lokacin da Sp khamis ya koma ciki dattijon nan nata matsar kwalla don kuwa Alhaji Ubale ya matsa akan a turasu kotu kawae,

"Ya Allah na dogara da kai,fadar kace,duk wanda ya dogara da kai ka isar masa,Ya Ubangijina kafi kowa sanin halin da nake ciki na rashi,nayi imani da jarabani da kake yi, nasan ba don baka sona bane sai don ka gwada imanina,Allah ka shirya man yarona da ya saka ni acikin wannan halin da Sauran Al'ummar Annabi(S.A.W)",
Dattijon na gama yin Addu'ar ya kalli Sergeant cike da k'warin gwuiwa yace"Ku tura mu kotun,duk da nasan ko anje banda halin biyanshi, Amman ubangijin dana dogara dashi nasan zai kawo man Mafita",ta6e baki Alhaji Ubale yayi ya juyar da kanshi gefe irin ko ajikin shin nan,

duk wannan abun akan idon Sp,yaji duk maganganun da dattijon yayi,nufar inda suke ya yi fuskarshi d'auke da Murmushi,yana isa gaban Dattijon ya mik'a masa hannu,kasa kama hannun SP yayi ya bishi da ido yana mashi kallon mamaki,hakan yasa SP jinjina mashi kai alamar ya bashi hannun,jiki na kerma ya mik'a masa hannu suka yi musabaha SP yace"hak'ika fad'ar Allah ce acikin Suratul D'alaq aya ta ukku'....Waman yatawakkalu alallahi fa huwa hasbuun....,ka dogara dashi ya kuma isar maka ta hanyar kawo maka Mafita"fuskar Sp d'auke da Murmushi yake maganar don ba k'aramin burgeshi dattijon ya yi ba,
gaba d'aya bin Sp sukayi da ido cikin rashin fahimtar abunda yake nufi,dattijon kuwa har lokacin hannunshi dake acikin na Sp sai kerma yake yi,

"Baba Mutumin da muka fita tare dashi ya baka Kud'in,ya turo su ta Account d'ina don ka biya shi" lokaci guda su Sergeant suka fara sakin Murmushi had'i da fad'in Alhamdulillah,don suma ba k'aramin tausayi dattijon ya basu ba,

Murya na rawa ya fara Magana"Yalla6ai ban fahimce ka ba,wani ya biya Kud'in kace? ko dae ba daidai kunnena suka ji ba?"

"Baba daidai kaji,ai kasan bazan zolaye kaba da magana irin wannan kuma a irin wannan lokacin" jin hakan yasa dattijon duk'awa k'asa yayi Sujjadar godiya ga Allah ,mik'ewa yayi hawaye cike a idanuwansa"Don Allah waye wannan d'an arzikin,waye mai kirkin nan haka,bai sanni ba, hakanan ya d'auki wannan uban Kud'in ya bani...."yana Maganar kwallan idonshi na zubowa ga kuma Murmushi yana yi duk alokaci d'aya,Sp shima dake Murmushi yace"Baba kada ka damu da sai kasan ko waye,don Allah ya baka",

"Nasani Yalla6ai,amman dae yakamata ai insan waye wanda yayi man wannan abun alkhairin da bazan ta6a mantawa ba asauran rayuwar data rage man",

"Ok shikenan tunda kana son sanin ko waye bari in fad'i maka,Sunan shi Haisam,shi d'an gidan Senator Ali Adamu Zakee ne" Sp na rufe baki Alhaji Ubale ya kar6e,
"ahaf d'an gidan dan siyasa ne dake kan mulki,su da ake satar kudinmu ana tara masu ai dole su rinka bada su yadda suka gadama.....",

Wata gigitacciyar tsawa Sp ya kwatsa mashi"Enough!!!kai ka tabbatar kud'in sata ne ya bada?shikenan duk wani mai mulki ya zama 6arawo?idan har cikin mutane akwae na kirki da kuma na banza to tabbas suma shuwagabannin dole asamu na kirki da kuma na banzan tunda daga cikin mutanen ake za6arsu,kuma da kake maganar wai an tara mashi,tabbas kuwa zancenka gaskiya ne an tara masa,sai dai ina son ka sani kud'in halal aka tara masa,kowa anan nasan ya san Mahaifinsa Shahararren mai kud'i ne wanda ya tara dukiyar da har su kare rayuwarsu zata ishesu yin rayuwa cikin jin dad'i,amman hakan bai hana Wannan bawan Allahn tashi ya nemi na kansa ba,injiniya ne na na'ura mai kwakwalwa,aiki yake ba dare ba rana,Kamfanoni da Manyan Ma'aikatu har ma da kananu wad'anda suka danganci aikinsa dake a Jahohin k'asar nan ake gayyatarsa yaje yayi aiki ba tare da girman kai ba ana biyansa kudin da ba komae yake dasu ba face yin aikin Alkhairin da yafi kowanne lada kamar yadda Manzon Allah(S.A.W) yace,Ka Shigarwa da Mutum Farinciki a rayuwarsa,ko ka yaye masa bakinciki,ko ka d'auke masa wata damuwa,babu aikin da yafi Wannan lada,ban tsaya ina maka wannan dogon bayanin ba don baka cancanci hakan ba,inda naso zan iya sa a kulle man kai saboda wannan maganar da kayi akanshi,amman banyi hakan ba don nasan da yawan Mutane irin wannan tunanin naka garesu akan duk wani mai Mulki,a k'arshe ina mai gargad'inka da ka rink'a kiyaye
harshen ka don Mutum irin wannan da kayi ma kazafi nada daraja ba awurin Mutane kawai ba har a wurin Ubangiji don yana daga cikin mafi Alkhairin mutane kaman yadda Manzon Allah(SAW) yace,khairun nas man yan faun nas,khairun nas anfa'uhun lin nas,(Mafi Alkhairin Mutane wanda yake amfanar mutane,mafi Alkhairin Mutane wanda Mutane suke amfanuwa dashi).

Ranshi a Matukar 6ace ya k'arasa Maganar,shikam Alhaji Ubale yayi wuri wuri da ido sai faman bashi hakuri yake yana fad'in su6ul da baka ne,banza yayi mashi,ganin yanayinshi yasa su Sergeant had'a baki wurin fad'in"Sorry Sir," shima Dattijon Mutumin hakurin yake bashi,sai da ya d'auki d'an lokaci ba tare daya tanka masu ba kafin yaba Alhaji Ubale Umarnin ya fad'o masa Account details d'inshi,baki na rawa ya soma fad'i mashi,ba tare da 6ata lokaci ba Kudin suka shiga yace mashi ya duba,dubu 70 cuf ya gani ya d'ago ya fadi mashi cewa sun shigo,shiru Sp yayi mashi don ba k'aramin kule shi yayi ba,ba don ya kai Zuciya nesa ba da sai ya hukunta shi,
k'okarin barin cikin Station d'in Alhaji Ubale ya fara,dakatar dashi Sergeant yayi"Hey,Alhaji waya baka izinin tafiya ne?"da sauri ya dawo yana fad'in"Oh kuyi hakuri pls,nazata shikenan" a rud'e ya yi Maganar,

K'aton littafin da ke abud'e saman kanta Sergeant ya duk'a ya d'an yi rubutu kafin ya d'ago yaba Alhaji Ubale Umarnin yasa masu hannu,cikin kermar hannu ya fara sa hannun bayan ya gama Sergeant ya duba sai kuma ya kalli dattijon ya nuna masa inda zai sa hannu,bayan duk sun sa hannun yaba Alhajin Umarnin tafiya,hannu ya d'aga yana yi masu Sallama ya nufi Hanyar fita buguzum buguzum,

Bayan fitarshi su Sergeant da dattijon suka shiga k'ara ba Sp hakuri,sauke ajiyar zuciya yayi yace masu ya wuce kawae,daga haka ya bukaci su zauna saman wani benci dake acan gefe shida dattijon,bayan sun zauna ne yayi masa bayanin ainihin kud'in da aka bashi,ya nuna mashi dalilin da yasa bai fadi mashi tun farko ba don yana ganin hakan na bukatar sirri ne don haka yanzu idan yana da Account ya bashi details dinshi zai tura mashi cikon dubu tamanin din,

Jin dattijon yayi mashi shiru ne yasa shi kallonshi yace"Baba kaji abunda nace?"shiru har lokacin bai ce uffan ba,hakan yasa Sp kai hannu saman kafadarshi ya d'an girgiza shi had'i da fad'in"Baba!"gaba d'aya Mutumin ya kifo jikin Sp,cikin tsananin tashin hankali ya d'ago shi yanata faman girgiza shi had'i da fad'in"Baba!Baba!!...."da alama fa kaman ba rai a jikin Mutumin,a rud'e Sp ya juya gun su Sergeant da k'arfi yace"Sergeant Bala pls come and help me!" suna jin haka suka zagayo da sauri inda su Sp suke,suma jijjiga dattijon suka shiga yi Sp dake kallonsu cikin tashin hankali yace"Sergeant ya Mutu ko?innalillahi wa'inna ilaihir rajiun....",
Chapter 59 · 0% Book details