Sashe 101
Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Unhum am all ears, miye ne?" taji ya fad'a idonshi akan tv, shiru tayi tana wasa da yatsun hannunta don tsoron fad'i mashi take saboda gargad'in da gwaggo tayi mata, aje remote d'in yay ya maido hankalinshi kanta a hankali ta d'ago suka had'a ido ganin kallon da yake mata ne yasa ta fara motsa baki amman ta rasa mi ma zata ce mashi,
"Kina sani abubuwan da bana so Zarah, i think i ave told u since banason maimaita mgn right?" ya d'age mata gira, d'aga mashi kai tayi alamar eh,
"Ok ina jinki"
Cikin en ina ta fara Magana "da..daman naji ba anan zakuyi salla ba Abuja zaku tafi"
Shiru kaman bazaice wani abu ba sai kuma yace "yea, akwae matsala da hakan?" girgiza mashi kai tayi "a'a, kawae dai nayi zaton anan zakuyi saboda ina son muyi yawan salla tare da kai",
bud'a ido yay jin wata Magana mai nuna tsantsan yarintarta, d'an Murmushi yay gently yace "ni ai bani yawon salla Zarah"
"Eh ina nufin ka kaini wurare dama, don duk salla ba inda nike zuwa in ba nan cikin Unguwar ba sai gidan wasu yan uwanmu yan kad'an" jinjina kai yay "Ko zaki bi mu Abujar ne?" ba zato ba tsammani taji ya fad'a aikuwa arud'e ta d'ago tana girgiza mashi kai alamar a'a, ya lura da razanar da tayi da jin abunda yace hakan yasashi tambayarta dalilin k'in bin nasu, farko shiru tayi sai kuma ta tuna da baison maimaita Magana hakan yasa kaman zatayi kuka ta fad'a mashi yarda sukae da Gwaggo harda rantsuwar da tayi na daga can tana dawowa sai Yola, shiru yay yana nazarin Maganar tabbas bai kamata ya gifta rantsuwar da tayi ba don yasan tana da dalilin hakan wanda bai wuce k'ok'arin da take yi na saita Fatun,
"Owk tunda ta rantse shikenan ba sai kin bimu ba but ki daina damuwa kan yawon sallan zan sa akai ki duk inda kike so in ma ta hana i will talk to her" d'agowa tai ta kalleshi ya d'age mata gira "are u Happy now?" jinjina mashi kai tayi alamar eh,
"To baki smile ba" ya fad'a fuskarshi a sake, da bud'ar bakinta sai cewa tayi "dama ina wannan ne?" wato abunda yace mata rannan itama ta fad'i mashi aikuwa ya jefo mata throw pillow yana fad'in kin raina ni da yawa Zaraah, duk'ewa tayi tana dariya hakan kuma ba k'aramin dad'i yay mashi ba don shi sam bai son yaga Mutum na k'unci duk sai yaji ya damu shiyasa in dae yana da iko yin yadda zai sa Mutum farinciki sai yayi, shiru su kai na wani lokaci can ta kalleshi idonshi akan tv,
"Naga an kawo man dinkin jiya" kai ya daga ba tare da ya kalleta ba,
"Nagode"
jinjina mata kai yay sai lokacin ya kalleta tana ta wasa da yatsun hannunta,
"Baki yin kunshi ne da salla" taji ya fad'a,
Turo baki tay "da gwaggo ke yi man irin na hausa nan da ake d'ansa Salatef ni kuma yanzu banson tayi man irinshi nafi son irin wanda ake yayi a yayyanka salatef d'in ayi design mai kyau da kuma bak'i da ake zanawa" ta k'arasa tana kwatanta mashi wanda take nufi a hannunta, d'aga mata kai yay alamar ya fahimta ya maida idonshi kan tv, bayan wani d'an lokaci ya d'auki wayarshi yai dialing kira ya karata a kunne, wadda ya ta6a kira mai suna Nana lokacin da zai kaita saloon ita ya k'ara kira, yar wurin aikinsu ce zatayi tsararshi sai dae bata yi aure ba har yanzu amman ba zaune take ba tana ta aikinta da bussiness kuma tana jiran Allah ya kawo mijin (da duk masu neman mijin aure Allah Ubangiji ka albarkace su da mazaje na gari masu wadatar zuci wadanda zasu sosu su kuma ruke su saboda Allah ba don wani abu ba haka ma mazan, masu aure kuma ka kara zaunar damu lafiya da mazajenmu ka k'ara rufa mana asiri ka Albarkaci zuri'armu, Amin ya hayyu ya kayyum, ban mance da masu neman haihuwa ba Allah ubangijin samai da kasai mai ikon akan komae wanda da yace kun faya kun (kasance sai ya kasance (wani al'amari) ka albarkace su da samun zuria d'ayyiba Amin),
suna mugun yin good time dashi dama kuma ita d'in yar barkwanci ce tana d'aya daga cikin Mutanen da ke sashi dariya ba tare daya shirya yin ba, kai tsaye take fad'i mashi itafa Mugun sonshi take ya taimaka mata ya shige da ita mana wato ya aureta, bayan ta d'aga kiran sun gaisa yace yana son ai ma Sister nashi henna ne tace ba matsala in zai yuwu ya kawota gidansu da safe mai kunshi zata zo yi masu sai ayi mata, amsa mata yay da owk daga haka yai rejecting call d'in, kallon Fatuu yay da ta k'ura mashi ido bayan ya aje wayar yace ta tambayi Grandma d'inta zai kaita k'unshi gobe da safe around 10 tace to, mik'ewa yay yace mata yana jin bacci ta d'aga mashi kai ya nufi Bedroom dinshi ita kuma ta koma kan kujera ta d'auki remote ta canja channel zuwa Bollywood ta kishingida tana yin kallon ahaka bacci yay awon gaba da ita, sai da akai la'asar ya fito don zuwa Masallaci ya ganta kwance tana baccin ta dukunkune cikin hijab d'in jikinta, babbuga kujera yay ta bud'e ido yace ta tashi taje gida tayi salla daga haka ya fuce bayan yaga ta mik'e itama.
Washe gari jajibirin salla kaman yadda su kai dashi karfe goma tazo part d'in nashi tana sanye da riga da skirt na atamfa ta yafa gyale dama tun jiyan ta sanar ma gwaggo ba 6ata lokaci suka fito don tafiya gidansu Nanar, lokacin da suka hau hanya zasu wuce k'ura ma lungun gidansu Haulat ido tai Haisam din na kallonta ta Mirror
"ko zaki je da ita ne" taji ya fad'a lokacin har sun wuce lungun, kallonshi tay ta d'an d'aga mashi kai alamar eh ba tare daya ce komae ba ya juya Motar suka nufi lungun gidansu Haulat din, abakin lungun ya tsaya bai shiga ba don ba tanan ne hanyarsu ba, ce mata yay taje ta kirata ta amsa da to ta fito, lokacin data shiga gidan ba kowa a tsakar gidan sai yan kannenta k'anana suna wasa hakan yasa ta nufi d'akinsu Haulatun, akwance ta isketa kan yar katifarsu ita da kannanta guda biyu da suma suke yin azumi sunata bacci, gefenta ta durkusa tasa hannu tana tada ita bayan ta farka ta tashi zaune Fatuu ta gaya mata ta taso za'a kaisu kunshi yanzu, tambayarta tayi wanda zai kaisu tace Ya Handsome, d'an jimm tayi tana tunanin anya za'a barta kuwa don da yau da daddare zasuyi na salatef, tana cikin tunanin taji muryar innarsu tana k'wala mata kira hakan yasa ta mik'e ta fita Fatuu ma tabi bayanta, gaishe da ita tayi ta amsa mata da fara'a cikin in ina haulat ta sanar da ita batun zuwa kunshin, da farko k'in amincewa tayi tace in ta tafi waye zai tayata aiyuka tunda tasan karshenta sai yamma koma dare zasu dawo don dole su iske layi sosae saida Fatuu tayi mata bayanin cewa ba gidan kunshi za'a kaisu ba gidan wasu yan uwan Hajiya ne nan mai kunshin zata zo, d'an jimm tayi haulat din ta marairaice fuska tana rokonta kan ta barta bazata dade ba in ma taga za'a kai yamma to zata dawo Fatuu ma ta tayata rokonta sannan ta amince suje, cike da farinciki sukae mata godiya haulat din ta nufi d'aki kaya kawae ta canja don ba lokacin yin wanka suka fice,
Lokacin da suka isa gidansu Nanar dake a Kopar Marusa lowcost wanda da gani suna da hali ba laifi, kiranta yay a waya yace mata sunzo ba tare da 6ata lokaci ba Nanar ta fito, yar gajera ce mai k'iba bata da haske sosae saidae baza'a kirata da bak'a ba don akwae yanayin hutu a fatarta, daka kalleta zaka gane wayayyar yar boko ce tana sanye da kaftan ta atamfa ta yafo gyale asaman kai don bata da kallabi, cikin fara'a sosae ta tarbesu bayan ta gama gaisawa da haisam din ta jasu ciki tace in an gama zasu yi waya, sosae ta shiga haba haba dasu haka ma yan gidansu harda Mahaifiyarsu a mutunce suka kar6esu don tun kafin suzo tayi masu bayanin wadda za'a kawo kunshin saboda ba wanda baisan Haisam ba agidan sosae yake yi masu Alkhairi don wani lokacin shi ke maido Nanar gida in sun tashi daga aiki in bataje da Motarta ba suna ganin Fatuu suka yanke cewa itace kanwar tashi duk da Haulat ma sam ba mummuna bace sai dae yanayin fata, batare da 6ata lokaci ba bayan angama ma wadda suka iske anayi mawa aka fara yi ma Fatuu bayan an gama mata akai ma Haulat lokacin har azahar tayi, ba k'aramin had'uwa kunshin yay ba na salatef da kuma zane dayake ba mutum d'aya ce keyi ba akwae mai kama mata nan da nan aka gama, sosae suka rink'a yaba kunshin ba kamar na Fatuu daya fito sosae kasantuwarta fara, har kitso Nanar ta tambayeta in tanaso ayi mata don da ana kunshi kallabinta ya cire sunga gashinta sosae suka rinka santinshi cikin ransu tace mata bata son kitson dama ita Haulat ta riga tayi kitson sallan, bayan sunyi sallar Azahar a d'akin Nanar Fatuu tace mata ta kira ya handsome ta fad'i mashi yazo ya daukesu an gama tace bazasu bari su sha ruwa ba a gidansu ta fad'i mata ance haulat ta koma kafin yamma ne, bayan ta kirashi ta sanar dashi ba'a d'auki wani dogon lokaci ba sai gashi ya kirata yace yana waje, kayan shafa harda turare dasu Popcorn da gullisuwa irin wanda Haisam ke ba Fatun ta basu kowa ledarshi daban daman a wurinta ne Haisam din ke siya, a tare suka fito falo sukai ma yan gidan sallama har mamarsu Nanar na cewa basu tsayawa su sha ruwa Nana tayi mata bayanin ana jiran d'ayar ne kafin suka wuce ana tayi masu bye bye,