Sashe 119
Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Washe gari Friday bayan sallan Juma'a Haisam da Hajiya na cikin cin abinci Fatuu ta shigo tayi gayun juma'a, bayan ta gaishe su Hajiya tace tazo taci abinci tace ta koshi yanzun ta gama cin abinci tace bata yarda ba sai taci ko yaya ne tunda daga yau ai sai bayan wani lokaci ko, kujera taja ta zauna ta zuba d'an kad'an, Haisam ne ya fara tashi ya nufi cikin falon kafin fatuu ma ta mik'e tace ma Hajiyar ta koshi, kishingid'e ta iskeshi tana niyyar zama ya mik'e yace tazo suje ba tare da ta tambayi ina ba tabi bayanshi ya d'an daga murya yace ma Hajiya zasu je su dawo tayi masu adawo lafiya, parking space suka nufa ya fiddo Mota cikin harabar sannan Fatuu ta hau suka fice, saida ya tsaya adaidai gidansu yace taje ta fad'i ma gwaggo zasu je su dawo sannan suka wuce, Bayan tafiyarsu gwaggo ma ta fito ta nufi gidajen makwabta yi masu bankwana harda gidan Hajiya, saida suka hau hanya sosae sannan ta tambayeshi ya akai bai tafi Lagos d'in ba ko sai anjima yace mata ya fasa tafiya yau sai gobe tace sai yaga tafiyarsu kenan ya d'aga mata kai alamar eh, ganin suna ta tafiya ne yasa ta sake tambayarshi inda zasu yace mata bazata kai ma yan'uwanta tsaraba bane, jin haka yasa tace "tsarabar zamu je siyowa?" kai ya d'aga mata ta kuma cewa "to mi za'ai sai masu?" shiru yayi idonshi a kan hanya sai kuma yace "Biscuits, chocolate and so on" jinjina mashi kai tayi can kuma sai ta fashe da dariya tace "wayaga su Yaya na cin chocolate saniya kenan" d'an juyowa yay suka had'a ido nan take ta tuna da fad'an da ya ta6a yi mata na ba'a had'a mutum da dabba hakan yasa da sauri tace yayi hakuri, shiru yayi sai kuma ya tambayeta wacece yayar tace matar Ardo yace "Grandma d'inki kike ce hakan?" da sauri tace "ai ba itace kakata ba ni kakata ta rasu kuma sunanta ne ma aka sa man Fatee...." shiru tay bata k'arasa ba tunawa da sunan maman shi ne, jinjina kai yay yace "ai itama grandma d'inki ce ko" da sauri tace" Allah ya kyauta wannan muguwar ta zama kakata, kai baka santa bane bata da mutunci kuma ta tsaneni da ina can tai ta k'ala man sharri tana sawa ana buguna kuma har babana ma bata son shi saboda taga ardo yafi ji dashi haka lokacin da Mamata bata lafiya harda ita ta hana a kaita Asibiti da wuri" ta k'arasa Maganar kaman zata yi kuka, shiru yayi kawae matsalar kaima yaro abu kenan don kwakwalwarshi bata mantawa balle abu irin wannan ko babba ma bazai ta6a mantawa ba, juyawa yay ya kalleta ta kwantar da kanta da gani ranta a 6ace yake slowly ya kirata ta d'aga ido ta kalleshi yace "Do forgive her and forget everything" turo baki tayi yaci gaba "Allah ubangiji yana son bayinsa masu yafiya, don shima mai yawan gafara ne in dae ka sa6a masa ka roki ya yafe maka zai yafe maka so kema ki yafe mata ki manta don in kin rike abun zai dame ki ne" tura baki tayi batace komae ba har saida yace bata ji abunda yace bane sannan cike da shagwa6a tace "yanzu duk abunda tayi man sai kace in yafe mata......" katseta yayi "yeah in kin yafe mata Allah zai daga darajan kine kuma kema ai kina son ki laifi a yafe maki ko" da sauri tace "to ni wama na ta6a ma laif...." kasa karasawa tayi ta zuba mashi ido tana mashi kallon rashin gaskiya, ta cikin mirror ya kalleta suka had'a ido ya dan ta6e baki ganin hakan yasa tana tura baki tace "shikenan na yafe matan amman wllh indae nayi kudi zan kai kowa makka banda ita" d'an jinjina kai yay yace "baki yafe matan ba kenan" da sauri ta kalleshi "nace na yafe mata fa, ko kana nufin itama sai na kaita makkan?" kai ya d'aga mata alamar eh, wani kallo tayi mashi kaman zatayi kuka "yanzu duk abunda tayi man kuma sai kace itama sai na kaita Makkan" yadda tayi Maganar sai kace tayi kud'in kaisu makkan ne, cigaba da yi mata nasiha yay kan yafiya idonshi akan hanya har dae ta saukko tace to zata kaita makkan, wata supermarket suka je sosae ya jidar mata kayan zaki harda abubuwan wasan yara itama ya siya mata ice cream, bayan sun bar wurin zagayawa yayi da ita cikin gari tana shan ice cream d'in tana yi mashi fira k'arshe ya wuce da ita Gym duk da ba exercise d'in zaiyi ba don baizo da shirin yi ba, lokacin data je wurin Anah sosae tayi farinciki da ganinta harda ma sauran yan wurin wad'anda suka santa koda tace zata hau machine hanata Anah tayi mutane nata masu dariya sai gab da Magrib ya maidata gida, sosae gwaggo taji dadin tsarabar da yayo mata tasa Albarka da Addu'oin da ta saba yi mashi, Bayan sallar isha sai ga Hajiya tare da Saude wai ta k'ara zuwa bankwana, d'akin gwaggo suka shiga dayake akwae wutar Nepa, bayan sun gaisa suka shiga yin hira harda Fatuu data shigo ta gaishesu hajiyar na ce mata zatayi missing dinta Allah yasa kar in taje su ruketa su aura mata d'an Fulani Fatun tace da kuwa ta gudo wllh gaba d'aya suka sa dariya, suna cikin hiran tasa Saude ta bud'e ledar da ta ruko mai d'auke da kaya, atampopi ta nuna ma gwaggon tace gashi nan akai ma Yadikko da Fatuu ke yawan bata labarinta da kuma k'annenta su d'inka sai shaddoji suma tace na Baban Fatun ne da ardo sai kuma yayanta kamalu, saboda tsabar farinciki har gwaggo ta rasa wace irin godiya zatai mata sai faman washe baki take tana sa Albarka daga baya sukai masu rakiya da zasu tafi bayan sun k'ara yin bankwana da juna, Washe gari wuraren Karfe shidda na Asuba Haisam ya parker a kopar gidansu don kaisu tasha dama tun jiya ya kira Amadu ya tambayeshi lokacin da zasu tafin ya fad'i mashi yace zaizo ya kaisu, kiranshi yay a waya ya sanar dashi yana kopar gida aikuwa ba tare da 6ata lokaci ba Amadun ya fara fitowa da jakunkunansu Haisam ya bud'e mashi boot ya fara sakawa yana gamawa Gwaggo da Fatuu suka fito gwaggo na sanye da lace da Hijab kalar kwalliyar fulawoyin leshin itama Fatun lace d'in da Haisam yayi mata ne da k'aramar salla tasa ta yafa golden gyalenta da takalmanta masu madauri hannunta ruke da jaka sai dae sam Fuskarta ba walwala saida gwaggon tayi Addu'a tasa Fatun tayi don neman tsari sannan suka fito, Amadu ne ya bud'e ma gwaggon kopar baya ta shiga yace ma Fatuu ta zagaya ta shiga shi kuma ya koma ya kulle gidan kafin ya dawo ya bud'e gaba ya shiga, gaisawa sukae da gwaggon ita kuma Fatun saida suka had'a ido ta mirror sannan tace mashi ina kwana d'an Murmushi yay kafin ya amsa yana kokarin kunna Motar daga haka kuma yajata suka tafi, ktsta ya kaisu cikin sa'a kuma suka samu Motar da zata tafi direct Yola don da ta Kano zasu hau in suka je can sai su hau ta Yolan, yaron Motar da Amadu ne suka fiffito da jakunkunan daga cikin boot suka saka cikin Motar, bayan an gama kintsa kayan aciki aka nuna ma su gwaggo seats na biyun karshe akace nan zasu zauna shi kuma Amadu daga gaba inda maza suke, Godiya tayi ma Haisam ta k'ara mashi sallama yayi mata Allah ya tsare, shiga gwaggo tayi ita kuwa Fatuu k'in shiga tayi tay tsaye tana kallon Haisam daya jingina da Mota yana sanye da farar jallabiya shima idonshi na akanta yayi folding hannayenshi a kirji da dan Murmushi akan fuskar bai dai ce mata komae ba bai kuma kirata ba don ya lura abu kad'an take jira tayi kuka, daga cikin Motar gwaggo tace mata tsayuwar mi take yi ne wai bata shigo ba hakan yasa ta juya ta shiga, kiran Amadu Haisam yay ya fito yaje wurinshi, Mota ya bud'e ya shiga batare daya rufe ba ya kirgo kudi masu yawa ya mik'a mashi amsa yay tare dayi mashi godiya shi kuma yay mashi Allah ya tsare daga haka yaja kopar Motar ya rufe shi kuma Amadun ya koma Motar lokacin idon Fatuu na akan Haisam din ta dan lek'a kanta ta tagar Motar da yake glass din a bude yake, tada Motar yay lokacin kuma glass d'in kopar ya fara sauka kasa slowly d'an lek'a kanshi yay suka had'a ido da ita a hankali ya d'aga mata hannu itama a sanyaye ta d'aga mashi daga haka kuma yaja Motar ya tunkari gate d'in fita glass din yana komawa sama a hankali ya fice, tana ganin ya tafi ta kifa kanta a cinya bata d'ago ba har Motar ta tashi, sai Fatan Allah yasa a sauka lafiya,