← Book details Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 111 OF 137

Sashe 111

Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Chef Zarah kin k'ona man egg ko" ya tambaya had'i da d'age gira, d'aga mashi kai tay alamar eh adaidai lokacin gwaggo ta fito hannunta ruke da buta zata bandaki ganin Fatuu tsaye sototo ga haisam na Murmushi yasa ta tambayeta lafiya tace mata kwan ne ya kone,
"Dama komae Mutum zai yi bai sa kula ba dole yaga ba daidai ba,sai ki maza kije ki amso wani kizo ki soya kafin ya gama" ta fad'a da d'an 6acin rai ta nufi hanyar toilet, tana niyyar juyawa taje ta amso Haisam yace ta barshi, kallonshi tay a sanyaye tace "amman ai bayan ya k'one fa" d'aga mata kai yay yace "sai ki cire wurin",
"Inda ya k'one d'in?" kai ya d'aga mata alamar eh, da sauri tace to ta kwashe acikin plate ta kawo mashi, duk'awa tayi zata cire inda ya konen yace taje ta wanko hannunta tana zuwa wurin gwaggo ta fito ganinta yasa ta tambayeta ta amso wani kwan ne tace mata ai yace ta barshi sai ta cire inda ya k'one d'in wucewa tayi ta nufi cikin gidan tana zuwa inda yake tace mashi miyasa ba zai bari a soya mashi wani ba yace lafiya lou abar wannan daga haka ta shige d'aki, bayan ta dawo ta cire inda ya konen tass ta d'ago tana kallonshi da d'an Murmushi,
"Go bring another fork" taji yace, mik'ewa tayi taje kitchen ta d'aukko wani cokalin mai yatsu kaman yadda ya mata umarni, tana mik'a mashi yace ta zauna taci indomie d'in, da mamaki ta kalleshi kafin tace wani abu ya rigata cewa "kinsan ai ya min yawa kika yi shi haka so da kanki dama kika yi" rantsuwa ta fara mashi wai shi kadai ta dafa mawa yace to ta zauna taci, zaunawa tayi ya juya plate d'in sukae facing juna, suna cikin ci gwaggo ta fito daga cikin d'aki don d'aukko ma Haisam d'in ruwa da lemu don yanzu Amadu harda manyan lemuna yake saidawa, tana ganin Fatuu na cin indomie d'in cikin harshen fulatanci tace ya ta dafa mashi abu kuma zata zauna ta cinye mashi, kafin Fatuu ta bata amsa Haisam d'in yace ba wani abu shi yace taci yayi mashi yawa, ba Gwaggo ba har Fatun saida tayi mamakin jin ya gane abunda gwaggon tace basu san guessing kawae yay ba daga yanayin yadda gwaggon tayi Maganar, Fatuu na ganin ta nufi inda freezer take da karfi tace "Gwaggo Coca cola zaki d'aukko mashi" tana juyowa suka had'a ido tasa dariya tana fad'in ai tasan kalan lemun daya fi sha kenan, ba laifi yaci sosae kafin ya aje fork d'in alamar ya koshi tana niyyar aje nata yace yasan bata koshi ba ta cinye, dariya tayi kafin taci gaba da ci shi kuma yaci gaba da latsa wayarshi, saida ta cinyeta tass ta tsiyaye sauran lemun daya bari mai yawa ta shanye sai lokacin ya d'ago ya kalli plate din kafin ya kalleta aikuwa da sauri ta sadda kanta tana dariya,
"Acici kawae" taji ya fad'a da sauri ta kalleshi ta turo baki tace "Kai Ya Handsome bakai kace in cinye ba" dan ta6e baki yay kafin yace wani abu wayarshi ta fara ringing kai idonshi yay kan screen d'in kafin yay picking call din fara magana a nutse, sanar da mai kiran yay cewa zai kirata in ya koma gida on the other hand aka tambayi yana inane yace yana gidansu Zarah,
"Oh Zarah where is she, let me speak wit her" wadda yake wayar da ita fad'a, mik'a ma Fatuu wayar yay ta amsa tana tambayar waye daga cikin wayar taji ance "is ur Sis Fanan" washe baki Fatuu tayi tace "Aunty Fanan ashe kece, ya India" amsa mata tayi da lafiya lou,
"Ai ina ce ma Ya Handsome ya gaida man ke in naga kuna waya yana fad'i maki?" amsa mata tayi da eh,
"To rannan nasa ya d'auki hoton kayan dana ce ki siyo man ya turo maki?" nan ma amsa mata tayi da eh ya tura mata,
"To kin siyo?"
tace "No, na bari sai zan dawo kinga in an siya yanzu zai iya maki kad'an lokacin"
"To shikenan,amman fa in suna da tsada ki barsu kawae kar ki kashe kud'inki kuma ki rasa na dawowa" har saida ta bata dariya kafin tace "Don't worry sis Zarah, i will definately buy it for u ko don yadda kike kulawa da Ya Handsome d'inki" jin hakan yasa Fatuu washe baki cike da gwaninta ta shiga bata Labarin indomie din data dafa mashi yanzu ya ci saboda Hajiya bata nan, sosae Fanan d'in ta nuna jin dad'inta tay mata godiya, hira suka shiga yi har saida Haisam yaji ya gaji da zaman ya mik'e sannan Fatun tayi sallama da ita tace Ya Haisam din zai tafi, d'akin gwaggo ta leka ta sanar mata zai tafi, fitowa tayi suka yi sallama yayi mata godiya tana fad'in haba ai ba wani abu bane duk yima kaine tunda ai anzama d'aya daga haka ya nufi hanyar fita tana mashi sai Allah ya kaimu Fatuu ta bi bayanshi suka fita tare, suna fitowa waje ya juya yace mata ta koma saida safe, har ya juya ta kirashi ya sake juyowa,
"In shirya gobe tunda ba islamiyya muje yawo?" ta tambaya tana d'an kare fuskarta da tafin hannunta guda, still yay kaman bazai ce komae ba sai kuma calmly yace "baki gajiya da yawo ne?" a ashagwa6e tace "ai to tun fa salla ban k'ara zuwa ko ina ba, kuma koda sallan ma ban gama yawon ba Tk din ya kwanta rashin lafiya kuma ma ciwon kaman na k'arya wllh don washe garin ranar da yace bai lafiyan na ganshi kan sabon mashin dinshi yaci gayu ya fita da nace ma gwaggo zanje mu idasa yawon tunda naga ya samu sauki sai ta hana ni" still idonshi na akanta slowly yace "ina zan kaiki?" watsa hannuwa tay "duk inda ka kaini" shiru yay yana d'an tunanin inda zaije da ita can ya tuna d'azun bayan ya iso sunyi waya da Abbas yake ce mashi ya kamata su kaima Najeeb ziyara don ya kusa barin kasar,
"Zaki je gidan Abbas?" da sauri tace "eh dama ban ta6a zuwa ba"
"Owk ask ur Grandma in ta barki zan kaiki..." tun kafin ya rufe baki ta katseshi "ai zama ta barni wllh",
"ki dai tambayeta, kuma bani nace ba" dariya tasa tana fad'in ai bazata yi mashi karya ba, ganin yana shirin juyawa yasa tace "to da yaushe zamu?" dakatawa yay "ba kince lokacin islamiyya tunda ba'ayi",
"Eh amman dai ba ina nufin da yamma d'in ba, mutafi tunda safe tunda bani zuwa makarantar boko saboda wannan satin aka koma kuma duk mutane basu zuwa" juyawa yay yana fad'in zai sanar ma Auncle d'inta time din da zasu fita, cike da murna ta d'aga murya tace "Thank u Sweetheart Ya Handsome d'ina" hannu guda ya d'an d'aga mata ba tare daya juyowa ba ta juyo da gudu ta koma cikin gidan, lokacin data shiga gwaggo ta kauda komae har ta shige d'aki hakan yasa ta bita cikin dakin ta sanar da ita zancen zuwa gidan Abbas don itama yanzu ta sanshi sosae, cewa tayi Allah ya kaimu kafin kuma tayi mata fad'a kan ta rage takura mashi tace to daga haka ta nufi d'akinta cike da farinciki.

Yana komawa part d'inshi ya zauna kan kujera ya kira Abbas, yana d'aga kiran ya hau yi mashi iskanci yana fad'in wai baisan lokacin daya dace ya kira mai aure bane, shidae d'an Murmushi kawae yay bayan sun gaisa ya kara yi mashi ya gajiya Haisam d'in ya sanar dashi game da zuwansu gobe shi da Zarah, sosae yaji dadi dama yana ba Feenah labarinta yace ma Haisam amman dae yini zai kawo ta ko yace mashi bai kaiga fidda time ba nan Abbas d'in yace ya kawo ta da wuri sai ya ci Abincin rana anan gidan tunda Hajiya bata nan kuma daga nan ma sai suje gidan Najeeb din ya amsa masa da owk, daga haka yai mashi saida safe Abbas d'in na fad'in bai bari suyi hira yace No baiso yayi mashi kora da hali daga haka yay rejecting call d'in Abbas nata kyalkyatar Dariya, sanin Amadu na shago lokacin yasashi kiranshi ya bashi sakon ya fad'i ma Zarah zasu fita around karfe 1:00 na rana cike da girmamawa ya amsa mashi da to, bayan ya katse kiran ya kira Fanan Vedio call ya hada a laptop dinshi dake kan c-table suka ci gaba da yin hira.

____________
Chapter 111 · 0% Book details