← Book details Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 109 OF 137

Sashe 109

Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ai hakanne kawae zaisa mu rabu da ita lafiya tunda kaga sani akai yi mata hakan" jinjina kai Amadu yay alamar ya fahimta suka k'ara d'an yin fira kafin ya mik'e zai tafi,

"Amman ya baka kawo man abun ciwo ba to" Tk ya fad'a yana dariya,
"Wake ta wani abun ciwo nida akace ma cikin ka ya lalace kana ta amai da zawo har na fara tunanin ko wucewa zakai" Amadu yay Maganar yana dariya shima,

"to na biyo ka bashi ka aiko man da kayan dubiya" Tk ya fad'a lokacin Amadun zai fita, akan hanya ya had'u da Fatuu ruke da kula zata kai ma Tk Abinci kallonta kawae yay ya d'an girgiza kai ita kuma ta tura mashi baki, tana wucewa ya kira tk a waya yace sai ya shirya ga Boss dinshi nan zata kawo mashi Abinci, koda ya isa bai tsaya shago ba dama wani yaro ya bari ya jire mashi, cikin gida ya nufa ya sanar ma gwaggo game da ciwon Tk din don ta tashi hankalinta har lekowa tay waje bayan Fatuu ta sanar da ita tace don Allah yay sauri yaje ya gano ya jikin nashi yana ciwo shi kadae a gida ya sanar mata dama yanzu yake niyyar zuwa, Salati Gwaggon ta saka ta shiga tafa hannu jin ciwon bana gaske bane,

"Wllh dama nasan dole ya gaji da wannan yawon, ai yama yi kokari kwana nawa suna fita kuma kullum sai wurin Magrib za'a dawo, ai da baiyi ciwon k'arya ba dama ina niyyar taka mata burki tunda ita bata da hankali bata san daidai ba" girgiza kai Amadu yay ya juya hanyar fita yana fad'in Allah ya shiryi Fatuu, tun daga ranar ba'a k'ara fita yawon ba.

**** **** ****

Bayan kwana tara da yin salla ranar Laraba da yamma Fatuu ta dawo daga islamiyya don sun koma tun salla da sati daya wato shekaranjiya litinin kenan, tana shigowa cikin zaure suka yi kacibus da Amadu da ya shigo daukar abu acikin d'akinshi, da sauri taja gefe don tasan yana iya rankwashinta, yar harara ya wurga mata ya nufi waje ita kuma ta nufi cikin gida, har ya fita ya juyo yace "Ke Ya Ugly d'inki ya dawo d'azun nan naga Tk ya d'aukko shi daga Airport" waro ido tai tasa tafin hannunta ta dafe kirjinta alamar mamaki, juyawa tai zata wurga jakar cikin gidan Amadu ya daka mata tsawa "baki da hankali ne ba akwae Alqur'ani ba!"
sai da yay Maganar ta tuna ta nufi cikin gidan da sauri ta ajeta a gefen dakinta kafin ta juya da gudu ta fita daga gidan ta nufi gidan Hajiyar sanata, lokacin data k'arasa part d'in nashi tura kopar Falon tay ta shige cike da zumudin son ganin Ya Handsome saidae bata samu kowa a falon ba sai daddad'an kamshi da sanyin da yake saki kamar ko yaushe, kware baki tayi ta rafka uwar sallama amman shiru bata ji ko motsinshi ba hakan yasa ta nufi bakin Corridor ta k'ara d'aga Murya tayi wata sallamar nan ma dai shiru ba'a yi Magana ba tana shirin yin ta ukku taji an bud'e kopar Bedroom d'in, sanye cikin Maroon din jallabiya mai gajeren hannu ya fito fuskar nan tai wani fresh ai koda tai arba dashi gaba daya hannuwanta tasa ta rufe bakinta tana dariyar farinciki, tsaye yay a gabanta cikin Corridor d'in ya goya hannuwanshi a kirjinshi yana Murmushi don ta tare mashi hanyar da zai fita cikin falon, sosae farinciki ya lullu6e Fatuu har tama kasa Magana ji take kaman ta ruga ta kankameshi don bata ta6a tunanin zai dawo yanzu ba saboda Hajiya in ta tafi salla sai tayi sati ukku bata dawo ba wani lokacin ma har wata don daga can tana biyawa Lagos, ganin tayi mashi tsaye yasashi yi mata alamar zai wuce da hannu da sauri ta matsa gefe ya fito ta jera dashi suka nufi cikin falon, nuna mata armchair yay alamar ta zauna shima ya zauna a inda ya saba zama, maimakon ta zauna kan kujeran sai kawae ta zauna akan carpet gabanshi tana ta faman sakin Murmushi,

"Duk Murnan ganin Ya Handsome d'in ne yasa kika kasa Magana" ya fad'a had'i da d'age mata gira, d'aga mashi kai tay alamar eh sai lokacin tace "Ya Handsome ashe yau zaka dawo?" shima kai ya d'aga mata,
"Tare da Hajiya kuka dawo?" girgiza mata kai yay alamar a'a,
"To ya akai kai ka dawo?" fuska a sake yace "aiki" jinjina mashi kai tay tana dae ta dariyar hakan kuma ya bayyanar da tsantsar farincikin da take ciki shidae sai kallonta yake da d'an Murmushi saidae acan kasan zuciyarshi yaji dadin ganin yadda take ta farinciki saboda dawowar tashi,

"Amman Ya Handsome ya akai baka gaya man zaka dawo yau ba kuma ko jiya fa munyi waya" ta fad'a ta d'an turo baki,
"Nayi laifi ne?"
"Eh mana daka fad'i man ba sai in dafa maka abinci ba" ta fad'a a shagwa6e, Dariya Maganar tata ta bashi yace "ai bana jin yunwa"
"Amman dae ai daga tafiya kake yakamata kaci abinci ko" d'an kwantar da kanshi yay jikin kujeran idonshi akanta yace "Don't worry naci abinci kafin na taho kuma tafiyan baida tsawo so bana jin yunwa yanzu"
"To anjima fa da daddare ina zaka samu abinci tunda Hajiya bata nan?"
"Zan siyo a restaurant" ya bata amsa,
"A'a gaskiya ka bari sai in kawo maka kawae" d'age gira yay ya bud'e ido ganin hakan yasa tace "ko bazaka ci na gidanmu ba?"
Shiru kaman bazai bata amsa ba can yace "to ai bada ni akai ba kar in cinye maku"
"Ni dai ko nawa ne sai na kawo maka" ta fad'a tana turo baki,
"Ke kici mi kenan?"
"Yo ko garin kwaki sai in sha" waro ido yay alamar mamaki yace "zaki ci wannan ki kwanta zai saki ciwo ai"

"Ai ina sha in banson cin abincin" d'an ta6e baki yay kawae can kuma ta ruk'e ha6a tace "kai na manta wllh tuwo miyan busassan ku6ewa gwaggo tayi kuma ansa daddawa fa"
d'an Murmushi yay "kinga dole ki bar ni in siyo kenan" da sauri tace "to sai in dafa maka indomie",
"Da indomie d'in kika ce zaki sha wannan abun ki kwanta?" da alama Maganar shan garin kwakin ta tsaya mashi, d'an sosa kai tayi tace "ai indae akwae abinci nace banci to ko nace zan amso indomie din wurin kawu Amadu na dafa gwaggo hanawa take tace in banci in bari amman yanzu tunda kai zan dafa mawa nasan zata barni na amso" girgiza mata kai yay "ki k'yale kawae"
Magiya ta fara yi mashi tana rantsuwar ta iya dafawa ko kawu Amadu ita yake ba ta dafa mashi ganin yak'i amincewa tace "Allah in baka yarda ba kuka zan maka kuma bazan ci abincin dare ba nima" dariya yay har fararen hakoransa suka bayyana yace "You can start now akwae tissue da yawa" tana jin hakan ta d'age kafafunta sama ta tura kanta ciki, kallonta kawae yake yana Murmushi sanin halinta na saurin kuka yasashi kiran sunanta ta d'ago aikuwa abun mamaki sai ganin kwalla yai sharere a fuskar, ta6e baki ta farayi alamar kukan zata yi sosae, girgiza kai yay cikin cool voice d'inshi yace to zai ci indomie d'in kawae sai ta kyalkyace da Dariya tana fad'in dama tasan ai data yi kuka zai amince tunda baison kukanta shi dae Murmushi kawae yake yana kallonta,

"Ya Handsome kaga hotunan sallan da tk yace ya tura maka?" d'aga kai yay yace "yea sunyi kyau yan mata" rufe fuskarta tay alamar kunya adaidai lokacin aka fara kiran sallar Magrib, kokarin mikewa ta fara yi tace bari taje tayi salla sai ta dafo mashi indomie din, ce mata yay sai bayan sallan isha zai ci ta bari sai lokacin ta dafa kar ya huce don bai iya cin shi in ya huce, amsa mashi tayi da to har zata tafi kuma yay tunanin bayan isha dare yayi bai kamata tazo kawo mashi ba a wannan lokacin hakan yasashi tsaidata yace ta bari zaizo gidan bayan isha prayer sai ta dafa mashi lokacin, cike da murna ta amsa mashi da to ta nufi kopa tana jaddada mashi da an gama sallar ya taho fa ya d'aga mata kai daga haka ta fuce shima ya mik'e ya nufi Bedroom don yin Alwala........

ALBISHIRUNKU MATAN AFRICA DA KEWAYE SHAHARARRAR MAISAIDA KAYAN MATAN NAN WADDA KUKAFI SANI DA MAMAN HAIDAR TANA YIMAKU ALBISHIR DA CEWA ZAKU IYA SAMUN KAYANTA ADUK INDA KUKE AFADIN NIGERIA DA NIJAR, KARKU MANTA MACE MAI GYARA BATA BORANCI💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃08040448621
Akwai zafafan kayan mata masu matukar kyau da arha cikin sauki zamu aika miki da kayanki cikin aminci da yardar Allah su isa har inda kike ba cuta ba cutarwa karku bari abaku labari.
Muna kawo kalolin ingantattun kaya kamar haka 💥💫💥💫👇👇👇👇
1-Maganin sanyi
2-Maganin gyaran nono
3-Maganin hips
4-Akwai gumba kala kala
5-Maganin matsi masu ciko da gaba ki koma kamar budurwa
6-Kalolin garirrika masu bawa mace ni'ima da jimawa ajiki yana aiki
7-Akwai tsumi sha yanxu magani yanzu
8-Akwai jigidar sirri kala kala
Sannan kuma muna dahuwa kamar haka 💥💫💥💫👇👇👇👇
1-dahuwar kaza
2-yan shila
3-ciccibi
Dadai sauran su.Abubuwa dayawa gaskiya bazasu lissafu bah saboda lokaci maiso ta bini PC don ganin Kalolin kayan da muke dasu 08040448621,

ALLAH YAYI MAKI KIMA DA DARAJA AMATSAYINKI NA MACE👰,KADA KI WOFINTAR DA KANKI A WURIN MIJI SABODA RASHIN GYARA KAI, BURIN MAMAN HAIDAR KO WACE MACE TA ZAMA TAURARUWA⭐YAR LELE AGUN MIJINTA😍 SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI🤝

*💖A SANADIN MAKWABTAKA💖*
_*(Love and Destiny)*_

_*BY ZAINAB LALUH📲*_
~(Oumm Imam)~

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

*6️⃣4️⃣*
Chapter 109 · 0% Book details