← Book details Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 137

Sashe 27

Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dan ta6e baki haisam yayi"U know I was just funning u dude,ina tausayin malamai mana,especially primary and secondary skul teachers suna matukar kokari sosae,but their Salary structure is still poor,kawae al'amarin kasan namu ne sai Addu'a,may Almighty Allah give us responsible leaders"
"Ameeen ya Allah" Abbas ya amsa.
"Yaushe ka shigo gari ne?" gyara zama Abbas yayi yace"ban jima da dawowa ba" jinjina kai haisam yayi kafin ya kuma tambayarshi"yasu Nafeesat and my Boy Abdul? Abbas yace"suna nan lafia,ita feenah ma tayi tunanin zuwa kayi ka koma,nace mata kana a gari hajia ta sa an maido mata kai nan,har take cewa shine ko ka leka ku gaisa"

dan murmushin gefe yayi"in sha Allah zan je,am not well settled har yanzu" kai Abbas ya daga yace" Allah ya yarda dama ai sai a hankali komae zai warware tunda wurin aiki ka canja" daga haka suka ci gaba da hira.

*** *** *** ****

Haulat tace"Ina ganin kije ki bashi hakuri tun kafin goben tayi....."cakk fatuu ta tsaya ko kyafta idanunta batayi kamar an dasa mata aya,haulat ta ci gaba"kinga idan ya hakura shikenan waya kawai zai kira yace ya janye inma yakai karar taki",
juyowa fatuu tayi tana kallon haulat da alamun mamaki tace"tabb lalle kema haulat din nan wani lokacin kaman baki da tunani wllh,kina nufin in kai kaina ma kenan,kinga daga nan sai hajia tasan ni ce in dama ya gaya mata"

"ba kince da aka aikeki gidan,kinga 6angarenshi daban ba?"haulat ta tambaya,
Fatuu tace"Eh,amman in naje ya cafke ni ya kaima hajiyar yace ga wadda ta rotsa masa gilashin fa?" girgixa kai haulat tayi"duk da bansan shi ba,nasan da wuya ya aikata haka gaskia,akwae mutumin dana ta6a gani sau biyu kuma ina tunanin shine....."da sauri fatuu tace"wani fari ko?zaki ga kalar farinsa daban" Haulat tace"ni bazan iya ganewa ba don duk a mota nike ganinsa ya wuce kawae dae fari ne"

"shine ma,don duk garin nan ba mai irin kalar farinsa.." da sauri haulat ta katseta"ke ya akai kika sani" tace"tabb yo nida na ganshi a kurkusa har sau biyu,ko kafin ya rabamu fad'a da murja har in fasa masa glass ai ran Alhamis ma da yamma sai da ya rabamu da jamila ina kokarin zubar mata da Awar...tsit fatuu tayi lokaci guda kamar ruwa ya cita,sai faman zare ido take.

Girgiza kai haulat tayi tace"kin bari yama san halinki kenan,Allah yasa ya hakura" a hankali tace "Amin,ai bazan kara ba"ta6e baki kawae haulat tayi tace"kije ki bashi hakurin,kar kiji wani tsoron wai zai cafke ki yakaima hajia,na tabbatar bazai yi haka ba,don sufa yan gayu aji ne dasu,ba don haka ba yadda Gaye yace yasan gidanku ai da yaso hajiyar ta sa ni da tun ranar ya kaita har gidanku tasan kece amman yadda kika je kaimata abinci bata yi maki maganar ba kinga tabbas bata san kece ba,don haka kije kiyi duk yadda zaki ya hakura,ki nuna masa kinyi nadama kar kuma kice wai don gaye yace za'a kai ki gidan yari in ba'a biyasa ba ki ka je bashi hakurin,inta kama kita kuka ma,in bakije ba har gobe tayi indai har yakai k'arar taki to dole Hajia da gwaggo su sani koda ba'a kai ki gidan yarin ba,kuma kinga shikenan na tabbata hajia 6atawa zatai dake duk kuwa yadda take son ki,ga kawu Amadu hmmm...."

Fatuu dai tayi zuru tana saurararta sai zare ido take gabanta na faduwa ta kalli haulat tace"amman kina ganin zai hakuran,ya yafe man haulat,kudin fa da yawa wllh ke baki san yawansu ba ne hmm"ta karasa maganar tana jinjina kai,haulat tace"In sha Allahu ina sa ran zai hakura,tunda na tabbatar yafi karfinsu,kuma ba ita kadaice motarsa ba,ko ni da nace maki na gansa sau biyu duk ba a mota kala daya nake ganinsa ba...."da sauri fatuu ta katseta "nima a mota daban daban nike ganinsa kuma kwalabo yake yi da kayan jikinsa da motar da ya hau" Haulat ta gyada kai"to kingani,kije dai ki bashi hakurin,kinsan wani duk zafin sa idan ka bashi hakuri akan laifin da kayi masa ka nuna kayi nadama bazaka kara ba,yana hakura"
Fatuu tace"ni wllh gabana sai faduwa yake kar inje yasa akamani ko tuwon gwoggo na karshe ban ci ba..." wani irin kallon mamaki haulat tayi mata"ke da baki son tuwon kullum kina k'orafin za'a kashe ki da shi" tace"ai na daina,yanzu nagane ba shine mai kashe mutum ba,gabza ce,in kasamu tuwon kawae ka godema Allah kaci"tasa hannu tayi tagumi,ita dai haulat dan girgiza kai kawae tayi tana murmushi don tasan irin nadamar fatuu.

Shiru sukayi nadan lokaci can fatuu ta kalli haulat tace"don Allah haulat to kizo ki rakani" da sauri tace"in raka ki ina? Fatuu tace"muje mu bashi hakurin....."girgiza kai haulat tayi da sauri"lokacin da kika yi masa 6arnar ai ba tare muke ba,hasali ma ba yadda banyi dake kiyi hakuri ba ki ka kiya,sai yanxu kice wai in raka ki,salon kija man balae" ta k'arashe maganar tana kallon gefen hanya.
Fatuu tace"oh dama kinsan wani abu zai iya faruwa innaje shine kika tura ni don cuta? da sauri haulat ta juyo tana kallonta tace"kindai san ni bazan ta6a cutarki ba ai,kawai ina gudun babana ya ganni tunda kinga limamin masallacin gidanne,kuma kinsan ni ba wani zuwa gidan nike sosae ba sai in na raka ki wani lokacin,dama dai cikin azumi ne shine kullum sai naje kar6ar sadaka da yamma,wani lokacin kuma in raka ki da rana inje insha A.c ko don rage yunwar Azim..." cike da tsiwa fatuu ta katseta"dalla kin cika ni da wani bayani,kawai in zaki raka ni ki rakani,in kuma baki zuwa ki fada man in kama gaba na"

Haulat tace "shikenan muje in raka ki amman iyakata wajen gate gaskia" wata irin harara fatuu ta wurga mata tace"to banso kisha zamanki,zanje ni kadai,kuma insha Allahu zai hakura,d'an bakin ciki sai dai ya mutu"daga haka ta mike ta kakka6e jikinta hadi da zura takalmanta ta juya zata tafi,itama haulat ta mike tana fadin"ai da ni yar bakin ciki ce da ban baki shawara ba ko,amman ba komae gobe ma rana ce,ko godiya bazaki man ba sai ma ki kira ni da yar bakin ciki"
Juyowa fatuu tayi ta k'ara harararta tace"sai ki jira kiga shawarar taki in tayi aiki,kafin kiyi maganar wata godiya" Haulat tayi dan murmushi tace"insha Allahu ma zatayi kawata kuma kanwata,ba inda za'a kai ki muna tare mutu ka raba" wani kallo tayi mata tana turo baki daga haka ta juya fuu ta tafi.

Cike da tsokana Haulat ta dan daga murya tace"kawata bazaki rakani ba,aike na akai in mun dawo sai muje in jira ki a bakin kofan ki shiga ki bashi hakurin" a fusace ta juyo ta kara watsa mata harara had'i da mummurgud'a baki daga haka tayi gaba abunta.
Daria sosae haulat tayi ta juya tabi hanyar da tafara bi d'azun a ranta tana fadin"haka kurum kija man yanzu babanmu yaji wannan abun duk da badani aka aikata ba ai sai ya sa6a man wllh,taje dai ina mata fatan nasara,in ma fushi tayi ma shirya daga baya.

Tafiya take sam hankalinta baya tare da ita,ta tafi duniyar tunanin shawarar da haulat ta bata,gani take anya kuwa zai hakura don a ganin da tayi mashi sau biyu tana ganin kaman ba zaiyi mutunci ba,ranar farko daya rabasu fada da jamila fuskarshi a murtuke take haka ranar da suka yi fada da murja daga magana bata ma idasa fadin abun da zata fadan ba ya gaura mata mari,tunanin hakan ne ke k'ara mata fargabar zuwa wurinshi,amman ba yadda zatayi dole taje kafin gobe tayi.

Daidai shagon kawu Amadu ta tsaya tana jiran ya sallami wani yaro,kallonta yayi bayan yaron ya tafi,fatuu tace"sannu kawu" jinjina mata kai yayi ganinta sukuku yasa yace"har yanzu jikin?" girgiza masa kai tayi"da sauki sosae"ta fada a hankali,d'aura jakar islamiyyarta tayi saman kiosk din tace"kawu jakata zaka aje man,zan dan je gidan Hajia yanzu zan dawo"sanin ba kowa acikin gidansu yasa shi daga mata kai alamar toh,daga haka ta juya ta nufi gidan hajiyar sanata,kirjinta na bugawa damm damm tamkar ana mata luguden ta6are haka ta daure har ta karasa,ta karamar kopa dake a bude ta bi ta shige.

_*Littafin A Sanadin Makwabtaka 300 ne,ga mai bukatar ci gaba da karanta shi bayan angama Free Pages sai ya tuntube ni ta wadannan numbers din 09016265659 ko 09013804524,pls just whatsapp message banda phone call,Thanks🤝*

*💖ASANADIN MAKWABTAKA💖*

*BY ZAINAB LALUH📲*
~(Oummu Imam)~

*page 24⃣*

......Suna cikin fira Abbas ya juya yana kare ma parlour din kallo kafin ya juyo ya kalli haisam"amman dai ya tsaru sosae,order din furnituren kai daga can i guessed" daga yadda haisam din yake ba tare da ya dago ba ya dage masa gira alamar ehh,
"da gani ai,sunyi kyau parlourn ma yayi kyau sosae,amman bai kai na gidana ba tunda ba mata a cikinsa,don inda da mace sai yafi kyau" ya karasa zolayar tashi yana ta daria,

"na lura dae ba zuwa kai mu gaisa ba,iskancin daka saba kazo yi mun...." da sauri Abbas ya katseshi da fad'in"pulling my best friend's leg,Allah zuwa nayi mu gaisa sosae don nayi missing din ka guy irin sosai din nan,kasan kana zuwa nayi tafiya so bamu wani gaisa sosai ba,and we ave'nt spoken like this for long,ko da yaushe sai dai phone and vid call,shiyasa na tara hira da tsokanan da zan maka sosae,Feenah fa har rigima tasa bazan fito ba,wai daga dawowa na zan wani kama fita,sai da nace mata wurin H,zakee zani sannan..." haisam ya katse shi"ai tana da gaskia dama bata barka ka fito ba,for gud 1 week basu saka ka a idonsu ba,kamata yayi yau througout ka zauna gida kafin gobe ka dasa zuwa aiki kuma"
Chapter 27 · 0% Book details