Sashe 88
Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Lokacin da ta koma sashen Hajiya, Saude har ta gama wanke wanken tana ganinta tace sai yanzu ni harma na manta dana aike ki, anan take fad'i mata kamata Ya Handsome yayi tana cin abinci kuma yace dole ta rink'a yin azumi kwana biyu kafin ta huta kwana daya kuma wai daga gobe zata fara, fuska a tur6une take gaya mata hakan yasa saude yin yar dariya itama tasan dama yakamata ace tanayi ko don ta saba, in ba haka ba wuya zata sha nan gaba in ya zamar mata dole karshe ma ta rink'a karyawa don ko shekarar data wuce bazata manta ba karyawar ta rinka yi don batama tunanin tayi cikakken azumi sai dae wani lokacin tana kaiwa azahar sannan ta karya wai intayi na gobe sai yazama d'aya, bata wani dad'e ba tace gida zata tafi Saude nace mata ko ta samar mata wani abu ta k'ara ci tace ta k'oshi, a haka ta nufi gida ranta a jagule don ance tayi azumi kuma dai ba damar tayi yadda ta saba don ta yarda Haisam d'in zai gani.
Da Asuba lokacin da gwaggo ta tada ita sahur dagewa tayi ta ci uban abinci wai don karta ji yunwa bata san in kaci Abinci da yawa bama kafi jigatuwa, da gari ya waye ko islamiyya k'in zuwa tayi wai in taje taya zata dawo cikin rana tana azumi tai wucewarta gidan hajiya lokacin batama tashi ba sai Saude dake gyaran gidan, bayan sun gaisane tace zata je d'akinta ta kwanta sauden ta tambayate ba islamiyya zataje ba tace bata iyawa Azumi take, Maganar har saida taba saude dariya, daga haka tai wucewarta d'akin Saude. Bacci sosae tayi don sai wuraren sha biyu ta farka tana jin wata irin yunwa saukinta ma acikin Ac take, tana cikin juye juye Saude ta shigo d'akin, ganin ta farka ne yasa tace masu Azumi antashi kenan, tambayarta Fatuu tayi wai an kusa kiran Magriba don taga tayi bacci sosae, Dariya saude tayi tace to dama ta k'ara kwantawa don ko karfe sha biyu bata yi ba, sosae gaban Fatuu ya fad'i jin hakan, bayan fitar saude duk yadda taso ta koma bacci abun ya gagara sai faman juye juye take tana yin tsoki dakyar ta samu ya d'an dauketa amman sama sama, shigowa saude ta k'ara yi lokacin an fara kiran Sallar azahar, ganin Fatun ta motsa tace mata ta tashi tayi salla ta amsa da to saidae har ta idar Fatuu bata da niyyar tashi, kiranta ta k'ara yi tace ta tashi tayi sallar inta gama sai ta kwanta, tana tura baki ta tashi zaune, koda ta saukko daga kan katifar ta mik'e tsaye sai taji d'an jiri ya kwasheta, da sauri ta koma ta zauna tanata faman k'unci hannunta guda dafe da cikinta ita dae saude tana ta lazimi bata tanka mata ba, saida ta dau d'an lokaci kafin ta sauka k'asa ta fara yin rarrafe ahaka ta isa kopar toilet din, Saude data saki baki tana bin ta da ido bata san lokacin data saki dariya ba tana girgiza kai tace Allah ya shiryeki Fateema, koda tayo Alwalar matsar da abun sallan tayi can jikin bango ta jingina dashi ahaka ta kwa6a sallar tana gamawa ta baje awurin, da Saude ta lek'o d'akin wurin karfe biyu har kwalla tayi mata wai mutuwa zatayi sauden tace mata bazata mutu ba don da ana mutuwa suma da suke yi duk shekara kuma duka ai da tuni sun mutu, tace wannan zaman d'akin da take yi ne yake sata jin wuyar azumin da zata d'aure ta fita tayi wani d'an aiki zata rage jin wuyarshi, tana jin hakan tace tabb wllh ita ko mik'ewa ma bata iyawa,
Ana gab da kiran sallar la'asar Hajiya na zaune a falo tana kallon tafsir aka aiko wata yarinya kiran Fatuu, da mamaki Hajiya tace anya Fateema na gidan nan kuwa, k'wala ma saude kira tayi ta fito daga cikin kitchen tun kafin ta k'araso cikin falon hajiya tace "wai Fateema na gidan nan kuwa?",
Murmushi tay tace "tana nanl" da mamaki Hajiya ta maimaita tana nan kafin tace "yaushe to tazo gidan ban sani ba?" Saude na dariya tace " Azumi take yi yau tun safe tana cikin dakina kwance" da mamaki Hajiya ta k'ara maimaita maganar Sauden kafin tace "to dama sauran ranakun da take cewa tana azumi bayi take ba?"
" Eh wai wuya yake bata shine take karyawa wani lokacinma wurina take zuwa in bata abinci to jiya na aiketa ta d'aukko Basket a part d'in yalla6ai haisam shine ya kamata tana ci ",
Salati Hajiya ta saka ta ruke ha6a cike da mamaki tace "yanzu dama duk marairaicewar da take tace tana yin azumi k'arya ne bata yi ko d'aya ba, kai Fateema Allah dai ya shiryata wllh, ke kuma ya da haka Saude ya zaki rink'a goya mata baya tana karyawa?" Hajiya ta kafeta da ido hakan yasa ta dan sunnar da kai kafin ta d'ago tace "ta ce man wai bata fara jinin al'ada bane kuma a islamiyyarsu ance sai Mutum ya fara azumi ya zamar masa dole kuma nima haka nasani shiyasa",
jinjina kai Hajiya tayi tace " to ai koda bata faran ba tunda alamomin balaga sun fito mata ya wajaba arinka sata tanayi amatsayin ladabi shiyasa ma Dijen ke sawa tana yi, kuma in bata saba da azumin ba taya zata rinka yi inya zamar mata dolen, aikuwa ya kyauta daya sata dole tayi in ba haka ba to kuwa ba ranar da zata yi azumin, kema kuma kar ki k'ara goya mata baya ta hanyar bata abinci abarshi a yadda Haisam d'in yace ta rinka yi" jinjina kai Saude tayi cike da ladabi tace "insha Allahu bazan k'ara ba",
Umarnin tado Fatun Hajiya taba sauden, lokacin da taje dakin tana nan dae malale a k'asa kaman ruwa tana ganin sauden ta fara juye juye tana fad'in wayyo cikinta,
" Sannu Fateema, ki daure ai ankusa ma shan ruwa tunda la'asar ta kusa",
wani kallo tayi ma Sauden tace "wai har yanzuma bata yi ba kenan, Aunty saude kodae lasifinkan masallacin ne ta lalace shiyasa baki ji ankira ba" ta k'arasa Maganar tana ta nishi, yar dariya tayi tace lafiyar lasifikan masallaci lau kawae lokacinne bai idasa ba, lokacin da ta sanar mata Hajiya tace akirata don an aiko kiranta cewa tayi ita wllh bata iya tashi sauden tace to taje ta fad'i ma hajiyan hakanne tace a'a ta kamata sai suje, kamar wata mai jinya haka Saude ta kamota suka fito hajiya na ganinsu ta saki baki tana kallon ikon Allah, a tsakiyar falon ta zauna tana gaida hajiyar da kyar,
"Yanzu duk azumin ne haka Fateema?" kai ta d'aga mata kawae,
"To sannu, ki tashi kije Dije ta aiko kiranki"
Yamutsa fuska tayi kaman zatayi kuka ta kalli saude tace don Allah ta k'ara kamata suje gidan, Hajiya ta hana tace ta daure ahaka zata saba, da k'yar ta tashi ganin hajiyar ta d'an d'aure fuska ta tafi tana layi kaman wata yar maye, tana fita waje ta dawo cikin falon kamar wadda wani abu ya biyo har saida hajiya ta d'an tsorata takai idanunta kopar shigowan, can gefen Hajiyar taje ta zauna ta jingina da kujerar da take zaune idanunta cike tab da kwalla, ganin hakan yasa hajiya tambayarta lafiya,murya kaman zata yi kuka tace "Wllh Hajiya rana yayi yawa baki ji ba dana fita kaman an watsa man wuta a fuska, ban iya zuwa gidan cikinta" tana kai Maganar kwalla suka zubo mata sharr, jinjina kai Hajiya tayi tana kallonta tace "to yanzu ace ma Dijen baki zuwa kenan duk da tun safe baki gidan?" shiru ta d'anyi sai kuma tace "A'a zani amman don Allah ki ara man lemarki" waro ido hajiya tayi bata san lokacin data sa dariya ba tace "lema kuma fateema" kai ta d'aga mata tana ci gaba da zubda kwallah, kwala ma Saude kira tayi tace ta aro ma fateema lemarta wai bata iya zuwa gida cikin rana, Saude nata dariya ta d'aukko mata lemar, dakyar ta mik'e tun acikin falon ta bud'eta ta d'aga saman kanta daga haka ta fita sunata mata dariya hajiya na fad'in yau Manya na Azumi.....