← Book details Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 108 OF 137

Sashe 108

Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washe gari ya kama kwana ukku da salla tk na cikin sharar baccinshi da safe ya jiyo sautin bugun kopar dakinshi koda yace waye Fatuu tace itace har saida gabanshi ya fad'i kafin ya taso ya bud'e mata, bin ta da ido yay bayan ya bud'en tana tsaye taci gayu da shaddar da hajiya ta d'inka mata don jiya voile d'in tasa, tana ganinshi ta turo baki tace "kai Tk wai bacci ma kake yi baka shirya ba kullum sai na jira ka"
"Ina zamu kuma" ya tambaya da mamaki,
"Yawon salla mana" jinjina kai yay yace "yanzu duk uban yawon da muka yi bai isa ba, ko inafa munje ina kuma zamu k'ara zuwa?"
"To ai kayan sallan nawa basu k'are ba, ko sai in sanyasu in zauna gida" ta fad'a tanata faman tura baki, d'an Murmushin yak'e Tk yay kafin ya tambayi kayan sallan nata kala nawane tace mashi kala tara ne yau tasa na biyar yanzu saura kala hud'u, waro ido Tk yay jin har nan da kwana hud'u masu zuwa sai sun fita, ce mata yay ta bari to sai zuwa d'an anjima sai su fitan tunda jiyan sun je wurare da yawa, da farko k'in yarda tay sai daga baya ta amince akan kafin sallar azahar zai zo su fita yace to, tana tafiya ya fara tunanin nemawa kanshi mafita don tsakani da Allah ba k'aramin takura zaiyi ba ace har nan da kwana hudu masu zuwa yana fita da ita kuma dae ba yadda zaiyi dole yai mata yadda yake so in ba haka ba yasan fad'i ma Haisam zatayi shi kuma ba zai so hakan ba koda kuwa haisam d'in ya fahimce shi, Wuraren karfe 12 yaje ya dauketa koda suka biya ma Haulat cewa tai su tafi kawae Innarta tace yau bazata fita ba ita zata kula da gidan don innar tasu ta tafi Unguwa hakan yasa suka tafi,

Gaba d'aya Tk baiji dad'in fitar ba har saida ta k'ule shi don gidaje tasa ya rink'a kaita na yan'uwansu su Zaliha da gidan Baba shehu har gidansu Nana saida taje da gidajen wasu k'awayenta gashi in ya ajeta yace zaije ya dawo sai tace a'a sai dae ya jirata ta fito abunda kuma yafi 6ata mashi rai kenan yadda ta maidashi kaman driver d'inta don ko Hajiya bata ta6a yi mashi haka ba ita iyaka in ma zai jirata in ya kaita wani wuri to baifi suje gida biyu ba, sam bai nuna mata 6acin ranshi ba amman yana ta sak'a yadda zai yi daga yau kar su k'ara fitowa, yau ma dae sai wuraren Magrib suka dawo da daddare bayan sallan isha suna zaune a tsakar gida gwaggo ke ce mata amman dai daga yau sun gama yawon sallan ko tace mata a'a ai bata sanya sauran kayanta ba gwaggon tace yakamata dae ta kyale tukur ya huta hakanan amman sai ta turo baki tace to ai dai Ya Handsome yace ya kaita duk inda take so don haka ita sai tagama sanya kowanne kaya sannan zata gama yawon sallan, washe gari ganin jiya basu fita da wuri ba yasata bari sai kaman lokacin sannan ta nufi gidan Hajiyan bayan taci gayu da d'aya daga cikin atampopin da Babanta ya kawo mata anyi mata riga da skirt ga gyale wanda gwaggo ta siya mata da takalma yauma dae tayi kyau abunta atamfar ta amshi fatarta sosae da yake adon flowers pink gareta, lokacin da ta je bakin Gate bayan sun gaisa da Officer ne yake ce mata anya kuwa Tk zai iya fita yau, cikin rashin fahimta ta tambayeshi dalili,
"Ai jiya kwana yayi ba lafiya don da daddare har saida na kaishi asibiti" cikin rashin yadda take bin shi da wani irin kallo bayan ya gama Maganar tace "Tk d'inne bai lafiya bacin ko jiya lafiya lou muka dawo"

yar dariya Officer yay kafin yace "in baya ga abunki hajiya fatuu ai yanzu yanzu sai Allah ko, ina tunanin wani abu yaci ya lalata mashi ciki shine ya d'ingi gudawa harda amai gaba d'aya yau da safe dana duboshi baida kuzari don ko Magana ma da k'yar yake yi" sototo tay tana kallon Officer alamar kaman dae bata yarda ba ganin hakan yasahi cewa ta shiga ta ganshi, wucewa tay ta nufi cikin gidan yana ganin ta tafi ya d'aga waya da sauri ya kira Tk lokacin yana kwance yanata sharar baccinshi kiran wayar ya tada shi don tana kusa da kanshi, bayan ya d'auka ne da sauri Officer ya sanar dashi ga Fatun nan ai kuwa wata wuntsilawa yay ya saukko daga kan k'atuwar katifarshi ya d'aukko wasu tarkacen Magunguna acikin drawer ya watsasu agefen katifar, bottle water dake saman drawer d'in ya d'aukko ya ajeshi a k'asa kusa da katifar, da sauri ya nufi kopa ya bud'e kafin ya koma kan katifar agurguje ya kwanta hadi da lullu6e jikinshi gaba d'aya da bargo yaba kopar baya, sai bayan d'an wani lokaci ta k'araso don akwae yar tazara daga gate zuwa bayan, tana niyyar kwankwasa kopar ta ganta a bud'e, d'an tura kopar tay ta rafka sallama shiru bai amsa ba ta k'ara yin sallamar sannan ta jiyo muryarshi can kasa yana cewa ta shigo kopar a bud'e take, a hankali ta tura kai ta shiga tana hango shi taja ta tsaya kaman taga abun tsoro ganinshi a kudundune cikin bargo, d'an matsawa tayi ta kira sunanshi shiru bai amsa ba ta k'ara sannan ya amsa da kyar,
"Ashe wai baka lafiya?" ta tambaya tanata zare ido, kai kawae ya jinjina mata ba tare da yayi Magana ba,
"Mike damunka?" shiru kaman bazai bata amsa ba can ya dan fiddo fuskarshi amman bai juyo ba don yasan daya kalleta yana iya yin dariya don dama akwae shi da yawan yin dariya, da kyar cikin irin muryar mara lafiya yace "ina tunanin Food poison ne naci ya lalata man ciki, jiya nasha wahala dakyar na samu na kira Officer ya kaini hospital har saida akai man k'arin ruwa na d'an samu sauki" yadda yake Maganar sai ka rantse da Allah bai lafiyar ita kau Fatuu k'ara zaro ido tai a rud'e jin harda k'arin ruwa akai mashi don ita a wurinta da anyi ma Mutum drip to ciwon yayi tsanani, kaman zatayi kuka ta shiga yi mashi sannu don dama ita badai tausai ba in taga mutum na ciwo duk ta damu, da kai ya rinka amsa mata can tace ya kawo wayarshi ta kira Ya Handsome ta fad'i mashi, da sauri yace " a'a ki kyaleshi kar a tada masu hankali tunda Officer ya kaini asibiti"
"To bari inje in fad'i ma gwaggo, in ta gama abinci kuma zan kawo maka" ta kai Maganar tana nufar hanyar fita da sauri, yana jin k'arar rufe kopa alamar ta fita ya yaye bargon daga jikinshi tare da juyowa yana dariya a fili yace "haka kawae ki nemi maida ni bawanki, ko shi Yaya Haisam d'in nasan da yasan wahalar dani zaki bazai sani kaiki wani yawon salla ba" ya kai hannu ya d'auki wayarshi ya hau yin chat abunshi,

Ko ta kan Officer dake tambayarta ta gano shi bata bi ba iyaka ta d'aga mashi kai kawae tayi gaba, gaban kiosk din Amadu ta tsaya da damuwa ta fad'a mashi Tk bai lafiya don Allah ya kira ya Handsome ta fadi mashi, ganin yadda ta damu ne yasashi tambayarta miya samu Tk din ta fadi mashi, kiran Haisam din ya shiga yi bugu d'aya ya d'aga ya mik'a mata wayar bayan ta gaidashi ne ta kwashe komae game da ciwon Tk din ta fadi mashi a rude tana ta zuzuta ciwon yace zai kirashi daga haka sukai sallama, tana shiga gida ta iske gwaggo cikin kicin itama ta hau fad'i mata, sosae ta shiga jimami har tana cewa ko wannan yawon ai yasa ma mutum ciwo, jin abunda gwaggon tace ne yasa fatun yin wuri wuri da ido jin kaman harda laifinta yake ciwon.

Tk na cikin yin chat kiran Haisam ya shigo har saida gabanshi ya fadi don yasan tabbas Fatuu ta gaya mashi bai lafiya ne, a d'arare ya d'aga kiran bayan sun gaisa ne ya mashi ya jiki yace da sauki sosae jin hakan yasa haisam din cewa Zarah tace har drip aka mashi shiru yay ya kasa cewa eh don mugun jin nauyin yi mashi k'arya yake kuma yasan in yace eh zai iya tada masu hankali ba kaman Hajiya in taji,

"Any problem?" yaji haisam d'in ya tambaya, cikin sanyin murya yace "ba wani abu daman ba ciwo nike ba ita na fad'i ma hakan kawae" shiru Haisam d'in yay kaman bazaice komae ba can kuma ya furta "why", ba tare daya yi mashi karya ba ya kwashe yadda sukae da Fatun na cewa sai kayan sallanta sun kare zasu daina yawon sallan kuma duk inda ya kamata suje sun je, sigh Haisam yay ta cikin wayar jin rikicin Fatun,

"kayi hakuri Ya Haisam in banyi maka daidai ba" Tk ya fad'a cike da girmamawa, gently yace "No, i understand, amman kana ciwon k'arya in ya kamaka fa?",
yar dariya Tk yay yace "ai ya haisam akwae inda dole saida karyar"
d'an guntun murmushi yay ta yadda har saida Tk d'in yaji daga haka yay mashi sallama tare da rejecting call din, cike da murna Tk ya fad'a kan katifarshi don sai yaji kaman wani nauyi ya sauka daga kanshi, yana kwancen Amadu ya turo kopar ya shigo, turus yay ganin Tk d'in kwance yana mashi dariya hakan yasa Amadu murza idonshi don wai ko ba daidai yake gani ba,
"Kaga patient na dariya ko" Tk ya fad'a yana tashi zaune, nufarshi Amadu yay yace "to ai ni waccan burkakkar ce man tayi wai kana kwance magashiyyan fa" k'ara sautin dariyar tk yay "ai hakan ta ganni ne, amman fa lafiya ta garas wllh" nan ya yi ma Amadun bayani dalilin ciwon karyar
"Yarinyar nan fa ba hankali ne da ita ba wllh kai jakinta ne, amman baka ce mata ka gaji sai kayi ciwon karya?"
Chapter 108 · 0% Book details