← Book details Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 118 OF 137

Sashe 118

Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

........Sosae Fatuu taji dadin sallar don sun fita yawo da haisam duk da bai biye mata ba na iya rana d'aya kawae suka fita tare kuma yawanci gidan Abokanshi yaje da ita ciki harda gidan Abbas sosae Abdul da Feenah suka ji dad'in zuwan nata taci gayu da shaddar da yayi mata, shima Abbas d'in bayan sallan da kwana ukku ya kawo Feenah yini gidan Hajiya suka wuni tare da Fatun harda ma Haulat tazo suka gaisa ta kuma je gidansu Fatun suka gaisa da Gwaggo bayan Magrib Abbas yazo ya daukesu. Bayan sallah da sati biyu su Fatuu suka fara jarabawar gama junior secondary wato JSCE, Haisam yayi mata abubuwan graduation sosae su littattafai masu d'auke da hotonta da key holder, biro, handkerchief jotter gaba d'aya tafi kowacce d'aliba yin abubuwa don har Malamai ta raba mawa,ranar da suka gama yakama ranar laraba ne cike da farinciki ta dawo gida da yamma sam bata ji wahalar jarabawar ba ba kamar da yake tana da kokari kuma Haisam ya taimaka mata wurin koya mata abubuwan da suka shafi jarabawar hakan yasa tayi ta cikin sauki ba tare data ji wahalarta ba, tana shiga Gwaggo ta taso ta rungumeta cike da farinciki, bayan ta gama tayata Murna ta kuma yi mata Addu'oi ta nufi gidan Hajiya ba tare data cire uniform d'inba gwaggo na ta tsaya taci abinci tace sai ta dawo, can ma Hajiyar Murna ta tayata da Addu'a ita da Saude, bata dad'e da zuwa ba Haisam ya dawo tana jin k'arar bud'e mashi gate ta tashi da sauri ta nufi hanyar fita,yana fitowa bayan ya gama parking Motar ya hangota ta nufo shi hakan yasashi dakatawa har ta k'araso sai faman washe mashi baki take, shima Murmushi yake yace mata Congrats tace mashi tagode, bud'e baya yayi ya fiddo flower da card na fatan sa'a a jarabawar da tayi mai shegen kyau sai d'aukar ido yake ya mik'a mata harda Flower d'in, waro ido tayi alamar mamaki kafin ta amsa tana kallonsu d'agowa tayi ta kalleshi baki washe tace nata ne ya daga mata kai alamar eh ta hau yi mashi godiya, hannu ya kai ya d'aukko jakarshi kafin ya rufe Motar da sauri ta amshi jakar suka nufi part d'inshi, bayan sun shiga ya amshi jakar ya nufi hanyar Bedroom ita kuma ta zauna tana k'ara kallon abubuwan daya batan sai faman dariya take, mamakinta abunda take gani yan kasan waje nayi a Tv suba mutum kyautar flower yau shine itama akai mata dama ba k'aramin burgeta hakan keyi ba, tana ta farincikinta har bata san lokacin daya d'auka ba saidae ganinshi tayi ya fito cikin workout outfit yace mata suje part d'in Hajiya ta mik'e tabi bayanshi, suna shiga cikin Parlon ta nufi Hajiya tana nuna mata kyautar da Haisam din ya bata ta yaba sosae sai bayan daya gama cin abinci zai fita ne tabi bayanshi yana tafiya itama ta nufi gida. Washegari Alhamis da rana Fatun na kwance kan tabarma gwaggo na gyara mata kai ta sanar da ita cewa ta shirya kayanta ranar Asabar zasu tafi Yola gaba d'ayansu amman su zasu kwana biyu ita dawowa zatayi, sam Fatuu bata ji dadin Maganar ba ba kamar da gwaggon tace can zata baro su ita da Amadu har ce mata tayi to su dawo tare mana tace a'a ai tunda ta baro garin bata je ba don haka yakamata taje ta kwana biyu,
"To amman shi kawu Amadun ba yana zuwa Makaranta ba?" ta tambaya tana yamutsa fuska gwaggon tace "eh amman yace zai tambayi izini don shima yana son zuwan saboda ya kwana biyu baije ba, inaga ma da hankalinshi ai sau d'aya ya ta6a zuwa" turo baki tayi kawae ita dai har cikin ranta bata son taje ta wani dad'e, tana gama gyara mata aka fara kiran salla tace ta tashi tayi salla itama ta mik'e, can bayan sun gama sallan ne ta bata kudi tace tayi sauri taje ta siyo mata kuka da daddawa zata yi miya nata sun k'are sai taje kasuwa zata siyo, d'aukar hijab dinta data aje bayan ta gama salla tayi tasa ta mike ta nufi hanyar fita, tana fitan maimakon ta tafi aiken da akai matan sai kawae ta nufi gidan Hajiyar Sanata don taga in Haisam ya dawo, tana zuwa ta iske ya dawo amman bai cikin falon sanin kaman yanzu shirin zuwa gym yake yasa ta zauna kan carpet tana jiranshi sai faman kunci take, tana zaunen ya fito kallo d'aya yayi mata yasan akwae abunda ke damunta, gaidashi tayi bayan ya zauna ya amsa mata kafin ya tambayi abunda ke damunta kaman zatayi kuka tace "ba gwaggo bace....wai Adamawa zamu tafi ran Asabar kuma acan zata baro ni nida kawu Amadu wai sai munyi sati biyu zamu dawo" jingina bayanshi yay da kujera da d'an Murmushi akan fuskarshi yake kallonta yace "to ai ba wani abu bane u supposed to be happy instead, zakije kiga relatives naki especially ur beloved dad baki son ki ganshi?" tura baki tayi tace "inaso amman dae sati biyu yayi yawa ni banson ta baro ni can nafi son mu dawo tare" sigh yay gently yace "ai ba wani dad'ewa zaku yi ba 2 weeks is just like tomorrow da kunje zai yi ku dawo" d'aga kai tayi ta kalleshi kaman zatayi kuka tace "shikenan bazan rink'a ganinka ba har sai mun dawo?" fad'ad'a Murmushinshi yay dama yasan duk wannan damuwar saboda shi ne don ya lura bata son abunda zaisa ta daina ganinshi, hannu ya kai ya shafi gaban kanshi kafin yace "in kin dawo ai zaki ci gaba da ganina besides akwae vedio call ko" jujjuya kai tayi kaman zata yi kuka tace "to ai shi kawu Amadun ne fa ba lalle ya rink'a kira man kai ba yana iya hana ni wayan" shiru yay kaman yana tunanin wani abu can taji yace "ko in sai maki phone d'in?" a d'an rud'e ta kalleshi sai kuma ta fara girgiza mashi kai tace "Gwaggo bata son in rik'e waya yanzu ko ka siya man hanani amfani dashi zatayi, kasan miyasa?" ta bud'a ido girgiza mata kai yay alamar a'a, taci gaba "wai wata abokiyar aikinta ce wani saurayi yay ma d'iyarta wayo saboda ya siya mata waya yayi mata ciki kuma har ta haifi d'an shegen" bilhakki take bashi labarin shidae shiru yay yana binta da ido saidae sam bai ji komae ba don yanzu yama saba da halinta na ya6o Maganar da duk tazo mata, ganin yayi shiru yana kallonta yasa da sauri tace "bafa ina nufin kaima wayon zaka man ba kawae na fad'i maka dalilin dayasa bata son in ruke waya ne amman tace in zanje jami'a zata siya man da kanta ma" jinjina mata kai yayi yace ya fahimta zai rink'a kiran Amadun yace ya bata, amsa mashi tayi da to amman still ba don ranta na son tafiyar ba can tace "ko muje tare da kai?" d'age gira yay kafin yace "aiki fa?" tura baki tayi tace "to ai tunda ran Asabar zamu tafi kaga ba aiki sai ka rakamu ka dawo ran Monday kaga rana d'aya ne bazaka aikin ba" d'an Murmushi yay yace mata shima zai je Lagos gobe ne da mamaki tace "shine kuma baka gaya man zaka tafi ba ko wayo kaso yi man?" daga mata kai yay alamar eh yanata murmushi ta turo baki, shiru sukae na d'an wani lokaci tana ta jujjuya kud'in hannunta taji yace "ba an aike ki bane?" tana yamutsa fuska tace "eh wai kuka da daddawa zan siyo mata ita bata gajiya da yi mana tuwo wllh" Murmushi ya dan yi "ai shima abinci ne mai kyau" tace "to amman ai kai baka ci"
"Ina cin wani" ya bata amsa tace "na shinkafa?" yace "yeah and semovita" tace "itama miya baka shan mai daddawa ko?" wani kallo yay mata ba tare da ya bata amsa ba tasa dariya dama da biyu ta ambaci daddawar sarae tasan bai shan, tura baki tay tace "nima wllh na tsani miyan yauki mai daddawa hakanan nike sha" yace "kije ki siya mata in na dawo sai kizo kici dinner nan" da sauri tace "amman tare zamu ci na bankwana?" tayi Maganar tana jaddada mashi, Murmushin gefe yayi kafin yace ai zata dawo ko tace eh amman dae ai sai ta dad'e yace owk tazo sai suci tare daga haka ya mik'e itama ta mik'e suka fita,
Chapter 118 · 0% Book details