Sashe 135
Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"tabbas nasan hakan amman fa ba wanda yake ma kalan naki don ke alkhairin da yake maki special ne, haba Fatuu kiyi tunani mana tun farkon haduwarku abunda ya had'a ku har kawo yanzu gaba daya ya canja rayuwarki dubi uwar dawainiyar da yake dake, ya dauki nauyin ki gaba daya komae shi yake maki, yasa an gyara maku gida an jawo maku ruwa daga gidansu ya siya maku kayan kallo harda Solar aka sa maku ke kanki yanzu d'akinki carpet ne, gaba daya kayan gadonki an gyarasu sun zama na yan gayu don ma nasan saboda na mahaifiyarki ne yasa bai canja maki wasu ba, ji d'ayan d'akin nan da aka idasa gininshi yadda ya gyara maku shi ya zama hadaddan falo, da dai sauran abubuwa da yake maki har ni fa dana shafe ki yana mana alkhairi sosae, yanzu duk sai kice hakanan yake maki wannan d'awainiyar, Come to think of it mana" kasak'e Fatuu tayi tana kallonta don jin zancen take wani iri sam ta kasa yarda da Maganar Haulat d'in ta wani bangaren kuma zuciyarta nason gasgata hakan,
"Ni ina tunanin bari yayi sai kin gama Makaranta sannan ya bayyana yana sonki shiyasa yake ta kulawa da abunshi" tayi Maganar tana dariya, ganin Fatun tak'i cewa komae sai kallonta take taci gaba da cewa "ko baki sonshi ne" ta d'age mata gira sai lokacin tace "amman ai yasan ni karatu nike son yi ni gaskiya ban tunanin hakan" ta k'arasa Maganar tana tura baki,
Haulat tace "Uhm su karatu manya, ke yanzu in yace yana son zai aureki sai ki k'i yarda saboda wani karatu can kin kuwa san irin tsadar da maza irin Yaya Haisam ke yi in ma an samesu kenan, ke baki ganin yadda kowace mace ke sonshi tun da can ma, ai wllh kar ki sake ki bari damar nan ta wuce ki in ba haka ba zaki mugun dana sani ne, yana cewa yana son aureki ki wuff kice kin amince ya aureki kuyi tafiyarku k'asan da zai koma kinga acan cikin sauk'i zaki karatunki ga kuma mijinki a gefe inyee" bakin Fatuu fa ya mutu murus sai zare ido take ga zuciyarta sai wani irin bugu take mata tana fasalto mata face d'in Haisam yana sakin kayataccen Murmushinshi,
"Sai wani faman bina kike da ido kema fa nasan kina son shi...." da sauri Fatuu tace "yaushe mukai haka dake?" tace "Uhm dama ai ke bazaki gane hakan ba tunda yana tare dake kullum, da zaki rasa shi misali kiga wata tayi wuff dashi a lokacinne zaki fahimci kina son shi" ajiyar zuciya Fatun tayi kafin tace a sanyaye don duk jinta take wani iri "amman kina ganin da gaske Ya Handsome na sona kuma zai aure ni?"
"Shakka babu kema don baki karatun Novel ne da da kanki zaki gane haka Mrs Haisam Zakee, wai zanso inga ranar nan Allah yasa kafin inyi aure ne, ke wllh koda nayi aure ne sai nazo don dai nan da Niger ai ba wani abu bane mu da ke k'irjin biki, amman fa zanyi missing dinki sosae in kuka tafi kasan wajen nan ta wani bangaren kuma zanso hakan tunda cigaban kine yar'uwata, wayaga su Fatuu Amarya kuma a gun Handsome wai nasan dai zaisha hauka don ma dai kin d'an natsu yanzu, wata tara ki san6alo mana twins tunda naga suna da gadonsu, kai Ya Allah, har na hango kyawun da yaran zasu yi wllh Madarar kyau" da sauri Fatuu ta kai hannu ta bugi Haulat d'in tace "Wayyo Haulat stop it pls kinsa na fara imagining abubuwa wllh" tai Maganar kaman zatayi kuka Haulat na dariya tace "imagining din mi keda baki san kuna son juna bama, ni kinga bani wayata inci gaba da abunda nafi auki" tay Maganar tana mik'a mata hannu fatun ta bata wayar ta duk'a tana mata dariya taci gaba da karatunta.
Tunda suka yi Maganar take jin wani bak'on yanayi a tare da ita ga suffar haisam da zuciyarta keta tariyo mata, mik'ewa tayi ta nufi hanyar fita daga Class d'in Haulat ta d'ago ta kalleta kafin ta girgiza kai ta koma taci gaba da abunda take, a saman barandar class d'in ta zauna ta jinginar da kanta jikin katangar data rufe gaban Office d'in dake tsakiyan ajin nasu da d'ayan ajin wato Sci B, shiru tayi tana ta tariyo rayuwarsu ta baya ita da Haisam tun daga farkon haduwarsu har kawo yanzu, sai faman sakin Murmushi take, jin shiru Fatun bata dawo ba yasa Haulat biyo sahunta nan ta ganta zaune yadda take da mamaki ta k'arasa wurinta tace "ni duk nayi tunanin fitsari kika je ashe da kina nan kin fad'a kogin tunanin sahibinki" ta k'arasa tana kokarin zama, da Murmushi Fatuu ta juyo ta kalleta tace "wani abu nike ji Haulat wanda ban ta6a ji ba game da Ya Haisam sai yanzu da muka yi Maganar nan dake" Haulat na dariya tace "So kenan yan mata, ai na fad'a maki wllh kina sonshi kawae dae baki san da hakan bane saboda baki san miye son ba to shima nasan hakan take a wurinshi tunda shima ba soyayyar yake ba balle yasan micece ita" gyad'a kai kawae Fatun tayi daga haka suka ci gaba da hiran Haisam d'in har Malamin da zai shiga yazo sannan suka tashi suka shiga Ajin.
Misalin karfe 2 saura kwata aka tashi saidae basu samu fitowa da wuri ba saboda malamin dake da period d'in karshe ya rike su saida suka gama kwafar rubutu sannan, atare suka fito bayan sun gama zasu nufi gate kamar ance Haulat ta kalli gefenta ta hango Motar haisam yazo daukarsu dama wani lokacin in yasamu time ya kan zo ya daukesu amman wurin zuwa kullum shi ke kaisu, da sauri Haulat ta ta6o kafad'ar Fatuu tace "ke ga mijinki yazo d'aukarmu da alama yaji firar da mukayi a jikinshi" da sauri Fatuu ta juyo ta kalli inda Haulat d'in ke nuna mata kafin ta kalleta suka had'a ido suka sakar ma juna murmushi, lokacin da suka k'arasa bakin Motar hannu Fatuu tasa ta bud'e gaba haulat kuma ta bud'e baya ta shiga ganin yana waya yasa fatun yin tsaye ta dafa kopar tana ta kallonshi ba kaman yadda yake yin Maganar a nutse hakan yasata jin yanayin data rink'a ji dazun har bata san ya gama wayar ba ya kalleta ganin tanata kallonshi yasashi d'age mata gira yace "ya dae?" sam bata jishi ba har saida Haulat ta d'an d'aga murya tace Fatuu ana magana sannan ta dawo hayyacinta ta shige cikin Motar tana mashi Murmushi shima Murmushin ya mayar mata ta rufe kopar suka tafi, tunda suka hau hanya take ta faman zabga Murmushi tana juyar da kai saidae duk abunda take Haisam na lura da ita ba tare data sani ba can ya kira sunan Haulat idanunshi akan hanya ta amsa da sauri tace "Na'am Ya Haisam" yace "yau ko kun samu kudi ne a skul" d'an bud'a ido tayi cikin rashin fahimta tace bata gane ba, shiru ya d'anyi don dama sama sama yake Magana da ita can yace "naga friend dinki is in happy mood i thought ko kudi kuka samu" tana jin abunda yace tasa dariya itama Fatun kallonshi tayi tana dariya tace "ai Ya Handsome abunda na samu yau yafi karfin kudi don bai iya siyar manshi" d'age gira yay yace "really, dama akwae abunda yafi karfin kud'i yanzu" da sauri tace "eh mana baka sani ba" d'an ta6e baki yay bai ce komai ba can kuma sai taji yace "inason sanin wane abune haka" d'an juyawa tayi ta kalli Haulat suka yi dariya k'asa k'asa kafin ta kalleshi tace "sirri ne" d'an ta6e baki yay baidae ce komai ba, suna shan round about Fatuu tace "Lah Haulat kalli Baba mai ice cream gaban gidan man can shine yau yak'i kawowa makarantarmu ashe yana nan, juyawa haulat tayi tana kallon inda fatun ke nuna matan kawae sai ji sukai Haisam d'in ya tsaya kafin ya fara reverse da Motar ya tsaya saitin mai ice cream d'in yace ta bud'e ta siya ta amsa mashi da to ta juya zata bud'e kopar ta saci kallon haulat suka d'an bud'a ma juna ido suna guntse dariya, mai ice cream d'in na ganinta ya washe baki yana mata dariya tace Sannu Baba mai ice cream shine yau ka k'i kai mana ka tsaya anan" yace "wllh naje wanccan makarantar kudin ta kusa daku ne to lokaci ya k'ure ban samu na k'araso taku ba har aka koma tara" jinjina kai tayi tace abasu ya tambayi wanne tace Fan ice yace na roba tace a'a ya basu na leda zai fi dad'in sha tunda a mota suke, guda ukku ta amsa manya ta mik'a ma Haulat d'aya ta aje sauran gaban motar tana kokarin curo kud'i Haisam yace ta bud'e glove box ta d'auki 5k ta bashi tana Murmushi tace to, sosae ya shiga yi masu godiya da fatan Alkhairi bayan ta bashi suka tafi, mik'a ma Haisam d'ayan tayi ya dan kalleshi kafin ya girgiza mata kai alamar bazai sha ba cike da shagwa6a tace "pls ka amsa kaifa na amso mawa"? K'ara girgiza mata kai yay idonshi akan hanya yace ta had'a ta sha, kawae sai gani yay ta aje duka harda nata a gaban motan ta koma jikin seat tana tura baki, d'an kallonta yay ganin abunda tayi ya d'an girgiza kai da Murmushi yaci gaba da driving can bayan wani lokaci kawae sai gani tay ya kai hannu ya d'auka ya kai baki bayan ya fasa ya fara sha a hankali dama abunda yasa yace bazai sha ba saboda bai cika son shan abu a leda bane, wani kallo tay mashi kafin ta juya ta kalli Haulat ta kashe mata ido d'aya ta juyar da kai tana Murmushi, tabbas yanzu ta fara gasgata Maganar Haulat ta Haisam na sonta.......
A takaice.......