← Book details Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 103 OF 137

Sashe 103

Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

ba abunda Gwaggo ke fad'a a fili da kuma cikin ranta face ALHAMDULILLAHI dama kuma kullum bakinta bai gushewa da fad'in hakan koda kuwa ba yadda taso abu ya kasance mata ba, kuma fad'ar Allah (SWT) ce idan ka gode mashi zai k'ara maka haka idan kayi takawa ya kasance ka kiyaye dokokin shi, yayi alkawari zai baka mafita a kowane irin al'amari sannan ya azurtaka ta hanyar da baka ta6a tunani ba, shiyasa ake so bawa ya kasance mai mik'a dukkan al'amuranshi ga Allah kuma ya kasance mai yawan gode mashi a koda yaushe to tabbas kuwa zai rink'a ganin bud'i kala kala (Alhamdulillahi ala kulli halin), gaba d'aya Azumin nan Gwaggo zata iya k'irga nawa ta kashe kud'inta don kuwa ba wasu kud'i masu yawa bane, ko su d'inkin salla da sauran siyayyar da ta yi masu duk cikin kud'in da tay niyyar siya ma Amadu freezer ne, ga Amadu yayi cinikin k'ank'ara sosae a haka ma don makwabta kyauta ake basu kuma sam basu cika mata kud'i ba kamar yadda wasu Mutane ke d'aura buri kan kankara cikin Azumi suyi ta saida ita da mugun tsada sai kace suma ba Musulmai bane suna yin azumin sun kuma san yadda mai azumi ke tsananin bukatar kankara, A maimakon su saukaka sai su tsawalla, A nan nike son jan hankalin masu saida kankara da suke tsawwalawa acikin Azumi da kuji tsoron Allah, kusani duk wanda ya ji tausayin Mutane ya rangwanta masu shima Allah zai tausaya masa akasin haka kuma kaima Allah bazai tausaya maka ba hadisi ne ingantacce, ba kuma iya masu kankara ba harda masu hali wannan ma ya shafe ku, wani sai kaga yana da hali amman har ya iya barin makwabcinshi ya kwana da yunwa wa'iyazubillah, saboda ba kyakkyawar alakar da d'aya zai iya sanin halin da d'aya ma ke ciki, sam wasu basa kiyaye hakkin makwabtaka wani ma ko cikakkiyar gaisuwa bai iya tsayawa yayi da makwabcinsa don yana ganin yin hakan tamkar alfarma ce yay masa, akwae hadisai da dama da sukae magana kan makwabtaka, Misali akwae wanda Manzo (SAW) yace, Mala'ika jibrilu bai gushe ba yana man wasiyya akan makwabci har nake tunanin idan na mutu makwabcina zai gajeni, haka akwae hadisi ingantacce da yay Magana kan duk wanda yay imani da Allah da ranar tashin Alkiyama to ya karrama makwabcinsa, amman sai kaga an koro yaran makwabci daga Makarantar da suke saboda littattafai ko Uniform kodae wani abunda bai kai ya kawo ba amma makwabcinsa nada hali bazai iya taimaka masu ba suna ta gararan ba acikin unguwa ko ajikinshi bai damu ma da ya tambayi dalili ba balle har ya taimakesu shi nasa yaran suna a Makarantu masu tsada har takai ta kawo wani fa ko rage ma yaran makwabcinsa hanya a Motarsa bai iya yi ya kaisu Makaranta yana kallo uban zai kama hannunsu yakaisu bakin titi don hawa abun hawa amman k'arshe saidae ya sakar masu horn ya wuce, ko kuma yaga yaran kan hanya suna d'aga mashi hannu alamar gaisuwa bazai iya tsayawa ya daukesu ba, abubuwan takaici dai da yawa wanda in nace in bayyanasu to fa har sai littafin nan ya idasa k'arewa ba tare da angama fad'in komae ba, Yakamata mu gyara masu hali ku rinka jin tausayin maras hali duk min yadda kake akwae wanda bai kaika ba so ko d'an yaya Allah ya bud'a maka kaima ka taimaki wani sai kaga an rage ma juna radadin talauci ba kaman a halin da muke ciki yanzu da babu tayi ma Al'umma yawa, kowa ya rinka kokarin ganin yasa farinciki ta hanyar yaye ma wani damuwarsa matuk'ar kana da halin hakan, kowa dae karshensa Mutuwa ce ko Mutum ya k'i ko ya so, duk kuma abunda ka mallaka dole anan gidan duniya zaka barshi su zama mallakin wasu, wad'anda suka aikata ayyukan Alkhairi Fisabilillah da dukiyoyinsu ne kadae zasu cigaba da cin moriyarsu ko bayan Mutuwarsu, ALLAH Ubangiji kayi mana Arziki mai amfani ka bamu ikon taimakon juna Amin.

Sosae Fatuu ta taya Gwaggon aiki saidae bata yarda tayi aikin da zata ta6a ruwa ba sosae wai kada lallenta ya fice tun kafin sallan, zuwa dare sun kammala komae har kajin sun soya anyo markad'en miya an tafasa shi sai zuwa da Asuba za'a idasa had'a miyar ta kuma tuk'a tuwon, ana gama Sallar isha aka sanar anga wata don haka baza'ai sallar asham ba hakan yasa fatuu ta nufi part d'in Hajiya don ta nuna mata lallenta, suma sosae sukae santinshi ita da Saude anan kuma Fatun ta tambayi Hajiya ya akai basu tafi Abuja ba gashi gobe salla tace mata Haisam ne yace su tsaya sai sunyi salla gobe sai su wuce, dama ita hajiya tana son yin sallar anan Senator ne ke matsa mata take tafiya daren sallah ko saura kwana biyu sallah, sosae Fatuu taji dadi don tasan tare zasu je sallar idi Gobe.

GOBE SALLA, GOBE💃💃

Allahu Akbar, Allahu Akbar La'ila ha ilallah, Allahu Akbar, Allahu Akbar Walillahil hamdu, Allahu Akbar kabeera, Walhamdulillahi kaseera, Wa Subhanallahi Bukratan wa asila, shine abunda Mutane keta fad'a washe gari Safiyar sallah, tun kafin Asuba Gwaggo ta tuk'a tuwonta ta k'ukk'ula acikin farar leda ta ida had'a miyarta da taji naman kasuwa sai kamshi ke tashi, lokacin da Asuba tayi Fatuu ta farka bayan tayi salla gwaggo tace ta share tsakar gidan, ta fiddo mata wankakkun labulaye da zanin gado tace ta gyara dakinta zuwa karfe shiddan safe gidan ya fito fess sai kamshin turaren wuta ke tashi, shirin zuwa sallar idi suka fara gaba dayansu don tun jiya Hajiya ta sanar da gwaggon su shirya tare zasu sallah karfe bakwae don 7:30 za'ai salla masallacin da zasu je, gaba d'aya Fatuu ta baje kayanta saman gado sai faman ruwan ido take ta rasa wanda zata sanya har saida taje ta tambayi gwaggo tace tasa Jallabiyarta bak'a mana aikuwa cike da murna ta nufi d'akinta don sam bata yi tunanin sanya taba kuma tasan inta sata ba sai tasa wata hijab ba, k'arfe bakwai saura gaba d'aya sun gama shiryawa Amadu ya shigo cikin shadda ruwan madara kafafunshi sanye da bakin takalmi da agogo sai hula kalar shaddar ya matuk'ar yin kyau sai k'amshi yake saki haka gwaggo ma atamfa tasa da sabuwar hijab kalar zanen atamfar tayi fess da ita sai kuma Hajiya Fatuu ikon Allah mai jallabiya ta had'u harta gaji, takalmanta golden masu tsini da haisam ya siya mata ta sanya hakan yasa jallabiyar tai mata daidai don dama ta d'anyi mata yawa kad'an, sarka da yan kunnan da gwaggo ta siya mata ta sanya sai agogo Wow abun dae sai Mutum ya gani da idonshi dama bak'ar jallabiyar adon sak'a golden gareta da stones sai tayi kamar yar balarabiya, hotuna Amadu ya fara yi masu cike da farinciki kowa bakinshi a washe suna cikin yin hotunan Hajiya ta kirasu a waya tace su fito, bayan sun fita gwaggo ta rufe gidan suka nufi Jeep d'in hajiya dake fake ita da Saude ne a baya sai Tk dake tuk'a Motar sun sha adonsu suma Hajiya na sanye da rantsattsar lifaya sai salki take, baya tace gwaggon ta shigo shi kuma Amadu tace ya zauna gaba gefen Tk ita kuma Fatuu tace mata taje wurin Yayanta sai ya taho da ita daga haka tk yaja suka tafi, gidan Hajiyar ta nufa a nutse take tafiyar idonta akan kafafunta kaman mai counting steps dinta, tana gab da zuwa kwanar gate Mercedes Benz d'in Haisam ta karyo kwanar hakan yasa ta ja gefe da sauri, tsayawa yay saitinta ta bud'e gaban ta shige, tana shiga suka hada ido da Haisam ta sakar mashi murmushi yana sanye da wata kwankwatsetsiyar, dakakkar, bugaggar hadaddar kuma rantsattsar farar shadda wadda ko makaho ya shafa sai ya gane mai kudi ce sosae, shigar komae white yay ya fito a balarabenshi sak ga wani fitinannan kamshi mai cika hanci na tashi cikin Motar hadi da ni'imtaccen sanyin Ac mai ratsa sassan jiki, barka da salla tace mashi ya amsa ta hanyar jinjina mata kai yaja Motar suka tafi suna dab da lungun su Haulat sai gata ta fito tanata sauri don tun jiya Fatuu ta gaya mata ta shirya su bi su Hajiya sallah, sam bata gane su ba don ba'a gane wanda ke cikin Motar,
Chapter 103 · 0% Book details