Sashe 83
Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
" To ya kike so ayi" ya tambaya idonshi akanta,
" Mu koma inda ka fara kaini naga akwae kujerun siminti sai in d'an k'ara hutawa yanzu juwa nike gani" jinjina kai yayi yace suje can d'in, a daddafe suka isa wurin masu tsaron gate d'in wurin nata tambayar miya sameta ganin lafiya lou ta fita bayan ta gama yi masu masifa, Haisam yace masu ta fad'i ne suka shiga yi mata Allah ya kyauta, wani ticket ya siya masu kafin suka shiga ciki, a gefe gefen cikin wurin dogayen kujerun suke,nufar guda sukai yace mata ta zauna zaije ya dawo, bayan ya tafi tabi wurin da kallo wai ko zata ga abokanta da tayi saidai duk babu su sun tafi dama sun rigata zuwa wurin, bai jima ba ya dawo hannunshi ruke da robar ice cream da bottle water tana zaune ta d'age kanta saman bayan kujerar,zaunawa yayi gefenta ya kira sunanta ta d'ago tana kallonshi, ice cream d'in ya mik'a mata ta girgiza mashi kai da sauri alamar bazata sha ba, shiru yayi yana kallonta don hakan ya tabbatar mashi batajin dad'i sosae tunda har tai rejecting ice cream saboda yasan tana sonshi ne ma ya siyo mata,
"Zan sha ruwa" ta fad'a, bud'e mata yayi ya mika mata, ta kafa baki ta shiga kwankwad'a har saida yace kar yasata amai sannan ta daina sha, amsar robar yay ya rufe ya aje su agefenshi harda ice cream din,shiru sukai na d'an wani lokaci ya jingina bayanshi da jikin kujeran yana kallon yadda yara keta wasa, ba zato ba tsammani yaji Fatuu ta kwantar da kanta saman kafadarshi, d'an juyo da fuskarshi yayi ya kalleta sai kuma ya d'ago yaci gaba da kallon yaran, a hankali ta rinka shakar daddadan turaren jikinshi mai sanyin kamshi da yaketa kaima hancinta ziyara, nan take kuma tashin zuciyar da take ji ya fara raguwa ta fara lumshe ido, bayan wasu mintuna Haisam ya fara tunanin ko dai ya kaita asibiti don ya fara gajiya da zaman hakan yasa ya kira sunanta don yaji ya take ji yanzu, jin shiru bata amsa bane yasa ya k'ara kiran nata still shiru bata amsa ba, d'an juyawa yayi ya kalleta sai dae bai iya ganin fuskarta don ta d'an dukar da ita kasa, dago fuskarshi yay yaci gaba da kallon wurin can kuma sai ya kai hannu ya d'aukko wayarshi dake gefenshi, camera din wayar ya shiga ya maida camerar ta gaba ya kaita saitin fuskar Fatuu, nan take ya saki d'an Murmushi ganin yadda taketa bacci abunta numfashinta na fita a hankali ga gashin idonta yai wani irin tsawo da tana baccin, janye wayar yayi ya fita daga camera d'in ya ajeta agefenshi, gyara zamanshi yay ya d'an zamo kafin ya kai hannun damanshi ya gyara mata kan nata yadda zai kwanta kan kafad'ar sosae,almost 30mins ta d'auka tana yin baccin kafin ta fara motsa kanta lokacin yanata latsa wayarshi, kallonta yay ya kira sunanta don dama ko bata tashi ba yana niyyar tadata saboda Magrib ta gabato wurin ma duk an yaye sauran mutane kadan,
"Zarah how are u feeling now?" ya tambaya bayan ta amsa kiranta da yayi, d'ago kanta tayi daga kan kafadarshi tana kallonshi shima ita yake kallo ya dage mata gira alamar uhhuym,
"Na daina jin juwar, aman ma ya koma" ta fad'a da sanyayyar murya, jinjina kai yayi ya juya,
"Ya Handsome..." yaji ta kirashi, juyawa yayi ya kalleta ba tare daya amsa ba,
"Don Allah kayi hakuri naja baka yi abunka ba, wllh ni bansan na ta6a wurin ba" shiru bai ce komai ba yana dai ta kallonta acan kasan zuciyarshi kuma mamakin yadda tayi mashi Maganar yake, ba yau ta fara bashi hakuri ba sai dai ba anutse kaman yanzu ba,
"Kayi hakuri" ta kara fad'a ganin baice komai ba, jinjina kanshi yayi "it's ok",
" To zaka kara fitowa dani?" ta dan bud'a ido, Murmushin gefen baki yayi sai yanzu ya gano dalilin natsuwar,
"Ki tashi muje magrib yayi" yayi maganar yana kokarin tashi, da sauri ta kai hannu ta kama hannunshi tace "bakai man hotunan ba" yar harara ya wurga mata, wato ta samu har Maganar pics take, fasa mik'ewar yayi dama wayar na ahannunshi, camera ya shiga ya juya zai mata hoton amman sai ta d'aga mashi hannu alamar ya tsaya,tace "To ai da fa nida abokai na zaka yi man yanzu kuma basu nan sun tafi sai kayi mana tare ni da kai" ba tare daya ce komae ba ya maida camerar ta gaba yayi mata alamar ta lek'o kawai sai ji yayi ta dafe kafadarshi, ta cikin camera d'in yayi mata wani kallo hakan yasa da sauri ta cire hannun tana d'an murmushin da ba har Zuciya take yinshi ba tana d'an kallonshi, alamar ta maida hannun yayi mata da kanshi, a sanyaye ta d'an dafa shi yayi masu hoton, ya d'auku sosae saidai ba wanda yayi dariya,sake shiga camerar yayi kafin ya d'auka yace "baki iya dariya bane" jin hakan yasa tayi dariya duk dimples dinta suka lotsa, yana shirin sake d'auka itama tace "to kaima baka iya dariya bane" jin Maganar tata yasashi yin d'an murmushin da bai shirya ba, tana ganin hakan da sauri tace "yauwa to kar ka daina yi" ta k'ara dafeshi sosae ta d'an kwantar da kanta tana k'ara yin irin dariyar da tayi daga haka ya dauka, lokacin da ya bud'e hoton har wata yar k'ara fatuu tayi don murna saboda hoton ya matukar yin kyau gashi ya d'auku tar tar dashi, ita tayi dariya shi kuma murmushi gaba daya dimples dinsu ya fito sosae, kitson fatun na gaba daya zubo gefe da gefe yasa tayi kyau sosae dama tunda ta gigice har ta suma ya warwaro daga daureshin da gwaggo tasa tayi,
(Nima dae saida na leka hoton, Ma Sha Allah shine abunda nace kuma masu karatu duk wanda ya kalla yace Ma sha Allah kar a lashe masu kyau 🤪)
"Ya Handsome bari in hau lilo ka dauke ni hoton" tana fad'in hakan ya mik'e yace"Next time" daga haka yace ta daukko ice cream da robar sauran ruwan da ta rage suka fita daga wurin.
(Uhmmm Allah ya kyauta gaba to, ni dama jinina kan akaifa yake game da wannan zuwa Gym din, team Fatuu ina mik'o sakon jaje su Fatuu anga bala'e harda su suma😹)
*💖A SANADIN MAKWABTAKA💖*
_A heart touching story of Love and Destiny_ 💔
*Mallakin*
⬇️
*🌹ZAINAB LALUH*📲✍
_~(Oummu imam)~_
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
5️⃣4️⃣
......Suna niyyar shiga mota Anah ta fito tana rataye da jakarta, nufo su tayi fuskarta a kwa6e ba walwala, agaban Haisam ta tsaya yana ganinta ya dakata don har ya bud'e kopar Mota, a sanyaye ta fara Magana,
"Am so sorry Zakee about what happened, i know it's all my fault but it was a mistake" ta k'arasa idonta cike da hawaye,
Sigh yayi a tausashe don yaga hankalinta ya tashi sosae yace " it's ok Anah, just let it be past " d'an guntun Murmushi tayi tace "thank u" kai ya d'aga mata kawai ta nufi inda Fatuu take tsaye ta dafa kafad'arta,
" Zarah ina fata kina lafiya?" jinjina mata kai tayi alamar eh,,
" akwae abunda ke maki ciwo yanzu?" girgiza mata kai tayi alamar babu,
"Am sorry kinji, ki hakuri pls" ta fad'a a marairaice, Murmushi Fatuu tayi mata hadi da d'aga kai, maida idonta tayi kan Haisam tace mashi sai gobe, kai ya d'aga mata ta wuce wurin da ake aje mashina don mashin take hawa roba roba, har ta d'anyi nisa Fatuu ta kwala mata kira " Aunty Anah",
juyowa tayi ta kalleta Fatun tace " zan k'ara dawowa ki koya man wani kala",
zaro ido tayi sosae jin abunda fatun tace hakan yasata kyalkyacewa da dariya, itama Anar dariyar tayi ta girgiza kai daga haka ta juya ta tafi, shiga cikin motar tayi donshi tuni ya shige ya jata suka bar wurin,
saida ya tsaya yayi mata siyayyar kayan kwalama yayi sallar Magrib a wani Masallaci sannan suka wuce, A bakin kopar gidansu ya tsaya da motar Fatuu ta fito shima ya fito ya zagayo bangaren da take, kopar baya ya bud'e ya fiddo ledojin siyayyar da yayi mata harda ta littattafan, Amadu na hango su ya fito ya nufo su, gaida haisam yayi ya amsa kafin yace ya tayata shiga dasu ya amsa da to,bayan ya tafi Fatuu ta kalleshi tana Murmushi tace "Nagode Sweetheart",
wani kallo yayi mata ta kyalkyace da dariya, tana ganin zai juya tace "Don Allah Ya Handsome karka fad'i ma Hajiya abunda ya faru fa",
d'an juyawa yayi ya kalleta sai kuma ya d'aga mata kai alamar to, har zai shiga cikin motar ya dakata ganin tayi tsaye bata shiga gida ba yace "ki shiga kiyi sallah sai ki kwanta, in kinyi bacci sosae u wll feel much better" kai ta d'aga ta kai hannu ta d'auki ledar data rage, ganin zaija motar yasa ta d'aga hannu tana mashi bye bye yay mata horn daga haka yaja motar,