Sashe 5
Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya dau tsawon mintuna a haka da alama dai ya gaji ne sosae kafin ya mike ya tunkari hanyar da zata kai shi Bedroom dinsa har zai shiga cikin koridon ya tsaya cak sakamakon karar da Telephone ke yi,a hankali ya juyo gami da kai idonsa saman desk din da telephone din yake yanata faman kara alamar ana kira,tafiya ya fara yi a hankali saida ya zauna saman daya daga cikin Armchairs din dake gaban teburin sannan ya mikar da hannunsa ya dauko kan telephone din,da murmushi a fuskarsa ya kara shi a kunnansa da alama yasan mai kiran nasa cikin murya mai tattare da gajiya ya fara magana"Hello sweetheart" dan saurarawa yayi kafin yaci gaba da magana "Ok ganinan zuwa yanzu" daria yayi har Hakoransa masu kyau da tsari suka bayyana cikin jaddada abun da ya fada ya k'ara cewa "Don't worry, I'm coming right away" yana fadin hakan ya maida telephone din ya mike har lokacin fuskansa da dan murmushi,Corridorn ya shiga kofa biyu ce a ciki daya tana kallon mutum in ya shiga wurin,dayan kuma na a bangaren bangon dake dama,sai da ya tsaya ya cire takalmin kafansa ya daura sa saman Shoe rag din dake ajiye a wurin anyi mashi design mai kyau da daukan hankali yabar safar dake a kafarsa bai cire ba kafin ya tura kofan dake a bangaren dama ya shiga,masha Allah Bedroom ne mai kyau da tsari bai da hayaniya Italian Bed ne da Bedside drawers din shi sai Dressing mirror wanda ke dauke da yan kwalaben turare da yan mayukan shafawa saidai da gani masu tsada ne don jikinsu kadai abun kallo ne,a bangon dake kallon gadon kuwa Wardrobe ce gaba daya bangon wadda ke rufe ruf a iya hangena nakasa gane yadda ake budata don banga hannun da za'a kama a bude ta ba, gaba daya Furniture din Coffee brown ne masu duhu sosai don inba ka shigo sosae ba zaka yi tunanin kayan bakake ne,haka Labulen dake a jikin katuwar Window din d'akin ma coffe ne mai kyaun gaske ga kauri wanda tsakiyan sa ke a tsage anyi hanging din bari daya,a Angles (sako) din bangon da gadon yake kuwa Floor lamps (dogayen fitilun kasa) ne dogaye ko ina an aje daya.
Gaban dressing mirror din ya tsaya ya cire agogon hannunsa ya daura a saman wurin kana yasa hannu cikin Aljihun wandon sa ya fiddo da wallet dinsa itama ya daura ta a wurin ya juya ya tunkari wata kofa dake a rufe da alama kofan Bandaki ce,kofan na budewa na tsaya kallon Ikon Allah don kuwa ba toilet bane wani dan daki ne mai tsawo sai dai bai cika fadi ba akwai Wall Cabinet (durowar bango) a jikin dogon bangon dakin wadda ke a bude ga kaya nan iri iri wasu a sagale a jikin hangers wasu kuma a ninke daga gafen cabinet din kuma madaidaicin injin wanki ne wato Washing Machine a jiye.a bangon dake kallon inda cabinet din take katon Madubi ne manne da bango daga kasan shi kuma wurin d'aura mayuka ne dasu Shampoo da sabulai kala kala da alama wurin laundry ne,wato wurin wanki dasu kayan dauda,tsayawa yayi gaban tangamemen madubin wurin yana kallon fuskarsa kafin yasa hannu ya ciro wipe daga cikin wani kwali mai kyau a hankali ya fara goge Fuskansa da ita,nikam zuru nayi ina kallon ikon Allah,ya gama goge ko ina ya jefa ta cikin dustbin sannan ya tunkari Wall Cabinet din ya fara cire kayan da ke jikinsa tun daga kan rigan saman zuwa ta cikin da safar dake a kafafunsa yayi hanging dinsu jikin hangers din Cabinet din ya rage daga shi sai Vest da Short acan sama cikin wani gida ya mika hannunsa ya dauko wani abu dake a linke fari sol cikin kayan da ke wurin da alama Bathrobe ce wato rigan wanka wadda duk jikinta gashi gashi ne mai laushin gaske daga haka ya tura kopan Toilet din dake cikin wurin ya shige.
*💖ASANADIN MAKWABTAKA💖*
*By Oummu Imam📲*
*Free Page5️⃣&6️⃣*
Sanye da Bathrobe din da ya d'auka ya fito,sai da ya cire Slippers din dake k'afar sa a bakin kofan toilet din yasa wasu flip-flops dake a waje cikin laundry din,K'arasowa yayi gaban Mirror din dake a Laundry room d'in ruwa na dripping daga cikin sumar kansa da alama wanke kan yayi,Juyawa yayi ya d'aukko d'an farin towel a cikin Cabinet din bangon ya dawo gaban mirror din yana tsane ruwan cikin sumar kafin ya jawo Stool ya zauna ya rataya towel din a wuyansa a can gefen mirror din ya mika hannunsa ya d'aukko Hair dryer wadda dama a jone take ya fara busar da sumar tasa yana dan jujjuya ta da d'ayan hannun yan mintuna ya dauka yana busar da sumar kafin ya maida dryer din inda ya d'aukko ta,Hair Oil ya matsa a tafin hannunsa ya shafa ma sumar sannan ya bude robar da Cotton buds suke ya zaro daya yana kwalkwale Kunnansa ya gama goge duka kunnuwan ya jefa abubuwan wadanda ba wani dirty a jikin su cikin Wastebin.
Daga haka ya mike ya nufi kofar shiga Bedroom din har lokacin Bathrobe din na a jikinsa,gaban dressing mirror ya tsaya ya fara matso mayuka yana shafe jikinsa bayan ya gama wardrobe d'in dakin ya tunkara wadda na k'osa inga ta yadda ake buda ta gefenta na dama ya tsaya,sak'a hannunsa gefenta yayi ya latsa sai ga shi ta fara zugewa da kanta,Iko sai Allah ashe Sliding ce,a tsakiyan murfin ta akwae tsaga wadda ta raba marfin biyu daidai,in ta daman aka bud'e sai ta zugo ta rufe ta hagun haka ma in ta hagun aka bud'e,komai dai na masu arziki na daban ne,Allah kai mana Arziki mai Amfani,Amin.
Kayan sawa ne birjik a cikin ta wasu a rataye jikin hangers,wasu a ninninke gasu nan a tsare abun gwanin burgewa. Kowane kaya da wurinsu,Jeans,Shirts,Suits,Shaddoji,Yadiddika,wasu ma kayan a cikin leda suke alamar sabbi ne,ga Underwears suma wurin su daban tsarin kayan dai kaman Boutique,fiddo kayan da zai sa yayi had'i da underwears sannan ya latsa jikin marfin daga ciki ta fara rufewa ya juya ya nufi gefen gadon ya d'aura kayan.......
Bayan ya gama sa kayan wanda T-Shirt ce coffe brown da bakin wando tracksuit wanda yad'an tsuke daga k'asa gafe da gefensa akwai zip wanda sai ka k'ura idanu zaka gani,rigan kuwa ta zauna cib ajikinsa hannun rigan ya kama cinyar hannunsa wadda take a murd'e da gani yana Bodybuilding,gaban Dressing mirror ya koma ya matso wani hadaddan mai ya shiga mutsitsika ma tafin hannuwansa,bayan ya gama ya dauko Hair Spray ya fesa ma gashin kansa sannan ya daukko turaren jiki wanda kwalbar shi kanta abun kallo ce ya faffesa ma jikinsa maida kwalbar yayi ya daukko wata itama mai matukar kyau ya fesa.....saida ya fesa turare kala ukku kafin ya dau Comb yana sharce kanshi wanda yake nad'e ko ba'a sharce ba bai yamutsewa,Drawer chest ya jawo ya fiddo da wani kwali mai kyau da k'yalli ya d'aura shi gaban mirrorn sannan ya bude,wasu irin agoguna ne masu kyaun gaske designers kala daban daban kowacce a dan gidanta ya fiddo mai fata kalan rigarsa ya daura sannan ya dauki wadda ya cire d'azun ya maida ta ciki ya mayar da kwalin hadi da rufe drawer.
A corridorn ya tsaya ya ciro takalma Slide Sandals bak'ake daga cikin Shoe rag kafin ya fito parlor a daidai nan kuma telephone din ya sake fara ringing,dan girgiza kai yayi yana murmushi bai kalli inda yake ba yasa hannu ya dauki wayarsa da ya aje dazun ya fice.
Ta Corridorn daya bi dazun ya fito cikin farfajiyar gidan mai girman gaske cikin natsuwa yake tafiya ya tunkari k'aton flat din dake a cikin farfajiyar wanda sak fentin shi kalar na gidan ne,Wani farin d'awisu ne ya fito daga bayan flat din ya bude jikin shi yana kuka gwanin burgewa,bansan lokacin da ni mai rubuto maku labarin na furta"lah kuga wani hadaddan dawisu,abun ka da ba'a saba gani ba,shi kau yalla6an ko kallon shi bai yi ba ya shige Entrance din,a wani dan corridor ya tsaya ya cire takalmansa da alama nan ake aje takalma kafin ashiga main Parlour din don akwai wasu takalman jere a gefe,shiga yayi cikin parlon wanda yake mai girman gaske fentinsa milk colour yana dauke da Royal Sofas masu kyau yadin su Maroon design din kwalliyarsu golden mai kyau ga Table dinsu aje a tsakiya daga can bayan kujerun kuwa dining area ce mai dauke da dinning table da kujerun shi irin design din kujerun parlorn, gaba kad'an da dining din kofa ce ke kallon su wadda corridor ne anan kuma kofofin bedrooms suke,Pop Casting din dake a bangaren da kayan kallo suke irin na d'akin mutumin da ya shigo ne sai dae hotunan dake wurin sunfi yawa har a sauran bangarorin bangon parlourn duk an kafe hotuna manya manya,hotunan wata dattijuwa sunfi yawa wasu tayi da family dinta wad'anda suke kyawawan gaske,wani kuma tayi da turawa akwai wanda tayi da Governor yana bata Award,da kuma wanda tayi da mutananmu na nan da alama a wurin aiki ne,akwae wanda take ita kadai ta nad'a lifaya fuskanta sanye da glasses tayi daria har hak'orin makkan ta ya bayyana daga kasa an rubuta sunanta,HAJIA HAUWA ADAMU ZAKEE,Akwae hotunan wani babban mutum wanda yayi suna gaisawa da shugaban k'asa,wani kuma tare da dattijuwar matar ya riketa fuskarsu d'auke da fara'a,akwae wanda kuma yake zaune a majalissar tarayya wato National Assembly k'asan hoton an rubuta sunan shi,SENATOR ALI ADAMU ZAKEE. Akwae flowers a Angles din parlorn da A.C manne a jikin bango,Labulayen cikin parlorn kuwa maroon ne da ratsin golden masu shegen kyau.