← Book details Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 132 OF 137

Sashe 132

Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"The other day bana baki hakuri ba kuma kin nuna kin hakuri miyasa kika daina zuwa?" taji ya fad'a, d'agowa tayi ta kalleshi kafin murya na rawa ta fara Magana "To ai ita wannan fa bata son ina zuwan nasan innaje data ganni sai ta karamin abunda tayi man kuma ko rannan data kada ni k'asa tace wai na taka mata k'afa wllh ni ban taka ta ba kawae bata sona ne shiyasa na daina zuwa" tana kai Maganar kwalla suka zubo mata sharrr tasa bayan hannunta ta goge, still idonshi akanta yace "bana gaya maki halinta ne hakan ba so u shouldn't mind her shit ki rabu da ita kuma a hakan zamu rayu a taren daga d'an abu har kin sare" da sauri ta kalleshi yace "ko ba ke kika ce haka ba?" ya d'age mata gira ta tura mashi baki yay murmushin gefe kafin yace "tunda kin zama matsoraciya ran Monday zasu tafi sai kici gaba da zuwa ko?" tana tura baki tace "ai ni ba tsoranta nike ji ba wllh don ko fad'a mukayi da ita bazata iya man komae ba kawai don ka hanani fad'a ne kuma banson inyi mata abu aga nayi mata rashin kunya kuma nima kamar yar'uwata na d'auketa tunda yar uwarkace" dan bud'e ido yay yana Murmushi jin tayi Maganar hankali tace "ko ba kace ni k'anwarka bace" still da Murmushin yace "Yeah sis d'ina ce Coward" cike da shagwa6a ta d'an jujjuya kai tana Fad'in"Wayyo Ya Handsome bana fad'i maka dalili ba wllh ni ba Matsoraciya bace" dariya yayi har hakoransa suka bayyana acikin ranshi kuma yaji dad'in abunda tayi, ganinta sanye da Uniform yasashi tambayar ta fara zuwa Skul ne tace a'a Registration zataje yi jiya sunje basu samu yi ba saboda akwae Mutane da yawa kai ya jinjina ya fara kokarin tashin Motar tace kaita zaiyi ya d'aga mata kai tace "to amman fa sai naje Kofar Marusa" ba tare daya kalleta ba ya tambayi abunda zata je yi,
"Wai sai an siyo fatanya da tsintsiya in za'ai registration d'in ni sai jiya nasani" kai ya d'aga suka fara tafiya saida suka dauki Haulat kafin suka wuce, Kopar Marusan ya kaisu ya siya masu duk abubuwan dama itama Haulat d'in bata siyan ba yau sukai da Fatun dama zasu biya su siya kafin su wuce, sunata hira abunsu shi da Fatun ita dae Haulat iyakarta Murmushi sai in kuma Fatun ta sakota sannan ta tanka har suka iso Senior section d'in Makarantarsu ya ajesu a gaban Admin ya bata kudi da tak'i amsa wai ai suna da kud'i gashi kuma shi ya siya masu abubuwan saida yace ta rainashi ko sannan ta amsa, cikin sa'a yau suka yi suka koma gida da wuri tayi duk abunda zata yi na aikin gida tayo wanka taci gayun juma'a da fitted gown dinta ta atampa tunda ta gama shiryawar take ta wasi wasi aranta na taje gidan Hajiya ko kar ta je k'arshe dai bayan an gama sallar Juma'a ta yanke zuwa ko don ta nuna ma Haisam d'in ba tsoron Farha take ba kaman yadda yace, Suna zaune gaba d'ayansu harda Haisam saman dining table suna cin abinci kowa ya dau wanka sunci gayun Juma'a ta shigo cikin Falon da Sallama gaba daya suka kalleta ai su twins na ganinta suka saukko daga kan kujerun da suke suka nufota da gudu suna mata Oyoyo duk suka k'ank'ameta ta kamasu tana dariya su Jidderh da Nameer nata Murmushi shidae Haisam tunda ta shigon ya d'ago ya kalleta ya maida kan yana ci gaba da cin abincinshi, janta su twins sukae suka ce tazo suci abinci tana ce masu ta koshi amman suka ki kyaleta har saida ta bisu dining area din ta ja ta tsaya gefe Hajiya ta kalleta tace "Manyan gari sai yau ake ganinki" Murmushi kawae tayi ta gaidata kafin ta gaida sauran duk suka amsa mata fuska sake ba kaman Nameer sai faman sakar mata kayataccen murmushi yake, Hajiya tace ta zauna to itama taci Abincin tana niyyar yin Magana Haisam ya d'ago suka had'a ido ganin kallon da yake mata harda d'an satar kallon Farha da tunda Fatun ta shigo ta wani sha kunu ta duk'ar da kai bata kara kallonta ba yasa ta fahimci abunda yake nufi wato tsoron farhar take hakan yasa taja kujera kusa da Jidderh ta zauna Hajiya ta k'walama Saude kira bayan ta fito tace tayi serving Fatun aikuwa hakan ba k'aramin k'ara ma Farha bakin ciki yay ba a cikin Zuciya sai kace wata mai galihu a gidan harda sawa ayi serving nata, gaisawa sukai da Sauden kafin ta tambayeta abunda zata zuba mata ta fad'i mata tace ba mai yawa ba taci abinci a gida, bayan ta gama tace mata aci Lafiya su twins suka ce ta zuba masu drink, a nutse ta fara cin Abincin tana yi tana satar kallon Haisam duk abunda take akan idon Farha kasa jurewa tayi don zuciyarta har wani boiling take tsabar bakin ciki ta mik'e zata bar wurin suka had'a ido da Fatun tay mata wani kallo mai kaman harara aikuwa ba zato ba tsammani Fatun ta rama kafin ta maida idonta akan abincin gabanta wani uban tsoki ta ja tana niyyar wucewa ta ture Cup din lemu da hannunta ya zube kasa tay gaba abunta duk suka kalleta saidae gaba d'aya sunyi tunanin zubewar lemun ne yasa taja tsokin banda Haisam da duk abunda suke yana gani duk da basu yake kallo ba, girgiza kai kawae Hajiya tayi suka cigaba da cin abincinsu, bayan sun gama gaba daya Falo suka koma suka ci gaba da yin hira banda Haisam da sai ta kama yake sa masu baki yadda suke hiran da Fatuu sai kace sun dad'e da sanin juna saida akayi sallar la'asar suka tashi Mazan suka nufi Masallaci ita kuma Fatuu ta nufi d'akin Saude Jidderh na cewa tazo suje d'akinsu suyi sallan tace zata yi acan ba matsala, tana gama sallar ta fito ta nufi waje anan ta hangi Haisam ya dawo daga Masallaci yana nufar part dinshi ta tsaidashi ta hanyar kwala mashi kira, tana Murmushi ta nufeshi idonshi akanta,
"Yanzu ka yadda ba tsoronta nike ba ko?" ta fad'a tana d'age ido harda ruk'e kugu da hannu guda, d'an Murmushin gefe yay kafin ya d'aga mata kai dama yana ganinta yasan saboda Maganar da yayi matanne tazo, tare suka nufi part d'inshi bada jimawa ba suka dawo tana goye da jakarshi suka nufi parking space ya haye bike bayan ya fiddo shi ta mik'a mashi jakar tana d'aga mashi hannu yaja ya fuce itama ta nufi gida.

Ranar Monday bayan sallar La'asar ta shigo gidan yi masu Jidderh bankwana jikinta sanye da Uniform d'in islamiyya, tana shiga ta hangosu tsaye gaban parking space Haisam na kokarin fiddo mota don kaisu Airport, da Murmushi ta nufesu su twins na ganinta suka kamata suna fadin "Sis Fatuu yaushe zaki zo gidanmu" dariya tayi tace "karku damu ina nan zan zo" d'agowa tayi ta kalli Nameer dake ta faman sakar mata Murmushi itama Murmushin take mashi yakai hannu yaja kumatunta yace "Yar fillo sai wani lokacin ko" yar harararsa tayi kafin ta d'aga mashi kai yace "Don nasan baza'ayi man aure ba yanzu da ina komawa zance ma Dad nifa nayi mata kinga sai kawai in aureki ki koma Abuja" wani kallo tayi mashi su Jidderh da twins suka sa dariya yace "Yess ko bazaki aure ni ba?" kafin ta bashi amsa Hajiya ta nufosu tana gyara mayafinta zata yi masu rakiya Saude na biye da ita ta janyo trolley duk suka juya suka kalleta daidai lokacin Haisam ya gama fitowa da Motar ya sauke glass yace su taho su tafi Farha ce ta fara shiga dama duk abun nan tana gefe tasa earpiece ko kallon inda suke batayi ba, Nameer ne ya zauna agaba sai Hajiya da jidderh a baya suka rike su twins a jikinsu, Hannu Fatuu da Saude suka d'aga suna yi masu bye bye suma suka sauke glass suna yi masu yaja Motar suka tunkari gate su Officer na masu Allah ya kiyaye suka fuce, tun akan hanyarta ta zuwa islamiyyar ta rink'a jin kewarsu kamarsu dawo tana tunawa kuma da Farha a fili tace "Dama wannan mai idanun magen kad'ai ta tafi banda su" tana ta tuna abubuwan da suka faru tsakaninsu har ta isa islamiyyar ta shige.

Rayuwa ta koma ma Fatuu kamar da bayan tafiyar tasu, taci gaba da zuwa gidan hajiya kaman yadda ta saba.

Bayan wani lokaci
Chapter 132 · 0% Book details