← Book details Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 137

Sashe 49

Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A saman tabarmar ta kwanta ta d'ora kanta saman cinyar Gwaggon,warware fakin d'in da akai ma gashin gwaggo tayi ta shafe gashin da mai kafin tasa comb ta fara taje mata,duk yadda take bi a hankali amman fatuu sai cije baki take tana k'orafin zafi can tace "gwaggo tun da dadewa kika ce zaki ban labarinki amman har yanzu kinki ki bani"yar dariya gwaggo tayi"to ke miyasa kike son jin labarina,ba kinsan garinmu da yan'uwana ba...",
"Amman ai bansan su waye iyayenki ba ko,kawu shi6ado na Daura kawae nasani da matansa da ya'yansa sai wasu dae yan'uwanki yan kad'an"gwaggo da har lokacin fuskarta ke d'auke da Murmushi tace"to ai na fadi maki sun rasu tuntuni ko...",
"a ina" fatuu ta katse ta,

"Tunda labarin dai kike so bari in baki a takaice,mu Asali Fulanin tashi ne wato masu caccanja wurare,na taso a kudancin kasarnan acan nayi wayo,fad'a tsakanin manoma da makiyaya ne ya rutsa da mahaifina har ya rasa ransa,to a lokacinne kawuna k'anin mahaifina ya dawo damu arewacin kasarnan ta dalilin wani Abokinsa wanda ke kai shanaye can kudun amman ba'a can yake zaune ba d'an nan Daura ne,bayan wasu shekaru da dawowarmu nan itama mahaifiyata ta rasu sakamakon jinya da tayi daganan ya rage bani da kowa sai kawu shi6adon da kika sani na daura....",
"amman to ke kad'aice baki da yayye ko kanne?" fatuu ta tari numfashinta,

"Ni kad'ae iyayena suka haifa,ina shekara goma sha biyu aka man aure,lokacin wani abokin su kawu ne Bello ya kwallafa rae akaina saida aka bashi ni ba don ina son shi ba amman bani da yarda zanyi,can yankin Safana aka kaini cikin matansa biyu nice ta ukku,matansa suka hade man kai,ba k'aramar wahala nasha ba agidan wannan bawan Allahn k'arshe dae matansa saida sukayi yarda sukae suka sa ya sake ni lokacin shekararmu biyar da aure,to bayan na dawo Daura ne Allah ya had'a ni da kakan ki Abdullahi a kasuwar mashi ina kai tallan nono,farko k'in saurararshi nayi don lokacin tsoron maza nike saboda wahalan dana sha a gidan Bello,daga karshe dae na Amince mashi muka fara soyayya har Allah yasa mukayi aure....",

d'ago kai fatuu tayi"Enye su Gwaggo ashe ansha soyayya" harara gwaggon ta wurga mata kafin taci gaba"shi asalinshi bahaushe ne d'an nan katsina wannan dalilinne ya kawo ni katsina shima lokacin yana da mata guda d'aya Habiba,Mutuniyar kirki ce sam bata d'auke ni kishiya ba face d'iya duk abunda zata yima yayanta shi take man,wani lokacinma in taga kakannaku nayi man fad'a in nayi masa ba daidai ba ita ke kwa6ar shi ta rinka cewa baka ganin yarinyace,shekararmu biyu da aure sannan nasamu cikin Innarki bayan na haifeta kuma saida nayi shekara sha biyu har ma na fidda ran sake haihuwan don nayi tunanin nima irin inna tace haihuwa d'aya zanyi sai ga cikin Amadu to tun daga kanshi ne ban sake haihuwa ba kuma yana shekara biyar babansu ya rigamu gidan gaskiya sakamakon had'arin mota da suka yi"d'an dakatawa tayi alamar jimami,

"Allahu kakana,Allah ya jikanka da rahama yasa ka huta,yanzu to ina ita Habiban gwaggo" Gwaggo ta amsa da "Ameen,ita ma yanzu kusan shekara bakwae da rasuwarta sakamakon jinya da tayi,sai dae ya'yanta da muke ta zumunci,ai kinsan zaliha ko ta kopar k'aura?" kai fatuu ta daga alamar eh,"to ai diyarta ce,da shehu dake zuwa gidannan..."katseta fatuu tayi bayan ta d'ago kanta"Baba Shehu?"Gwaggo tace"eh shi,to shima d'an habiban ne,yaranta shida",
"Allah ya jikansu gaba daya" fatuu ta fad'a,
"Ameen" gwaggo ta amsa.

Shiru sukae na wani lokaci gwaggon nata gyara mata gashin,can fatuu tace"Amman gwaggo ya akai to Innata tayi Aure a Yola?" fatuu ta tambaya,Ajiyar zuciya tayi kafin ta d'aura"bayan mungama takabar kakanku Abdullahi dole na koma daura don bani da kowa anan,alokacinne kuma kawu shi6ado ya matsa aima Aisha aure acewarshi tayi girma da yawa kuma dae da gaske yake don lokacin duk yankinmu ba babbar budurwa kamarta don shekararta 17 gashi tubarkallah sam jikinta ba irin na ainihin yanmatan fulani bane hakan kuma ya samu asali ne daga mahaifinta da yake cikakken bahaushe dama fuskarta sak shine,yana da kyau da dogon hanci amman baki ne,ita kuma Aisha sai ta daukko haskena don harma ta fini fari sosae kuma batada tsawo ba kuma gajera bace,sannan Allah ya hore ma Aisha kugu tun tana yar k'ankanuwarta ya fara bayyana lokacin da take shekara sha bakwae d'innan in ka kalli kafadunta bazakace k'ugun nata bane don ya bude sosae harda shi kesawa ana ganin tayi girma da yawa,kema naga alamun jikinta ne zaki daukko don sam baki da tsawo gaki nan yar dumurmur...."kyalkyacewa da dariya fatuu tayi"kice nima zanyi hips,ai kaman ma ya fito fa,innasa skirt yana nunawa, Allah shiyasa nike son sa skirt",

Yar harara gwaggo ta wurga mata kafin ta d'ora"lokacin da ake ta maganar ayi mata aure ita bata so karatu take son taci gaba da yi don a katsina tana makaranta harma ta shiga Sakandire,amman fir kawu shi6ado yace baisan zancen wani karatun nasara ba,kan kice mi samari sukayo mata ca bayan komawarmu amman ita bata son kowa ganin tak'i fiddo miji ne yasa kawu yace shi zai za6a mata duk wanda yayi mashi,ana haka sai ga Muhammadu wanda abokin wani yarone makwabcinmu shi kuma yaron abokin dan wajen kawu ne,Muhammadu Dan jahar Adamawa ne,manyan kasuwannin yankin Katsina suka fara kawu shanaye to shine ya fara sauka a wurin abokin yaron kawun dama kuma yan uwansu ne,yana ganin Aisha Allah yasa mashi sonta itama kuma ta amince dashi don tubarkallah ko ni lokacin na yaba dashi ga kyau ga biyayya ba 6ata lokaci akayi bikinsu,to kinji yadda mamanki ta auri baffanki,bayan shekara guda da auren ta haifi yayanki Kamalu nayi murna sosae ganin ba'a dau wani lokaci ba,Kamalu na shekara ukku ta Haifeki kar kiso kiga Murnar da nayi don na fahimci ita bata gado ni ba,ashe duk salesalin Ajali ne....",dakatawa gwaggo tayi fuskarta a yamutse,

"Kina shekara ukku Allah ya kar6i ran Aisha,ba lokacin aka fara man mutuwa ba amman naji mutuwar Aisha nayi kuka su kenan gareni su biyu ita da Amadu,ba yarda banyi ba alokacin amaido man ita nan amman sai kakanki ardo ya hana yace wai ba ciwon Asibiti bane to sanin Aishar nada iska ne yasa na amince da Maganarshi ashe ashe cutace kunshe acikinta....",
Dan ta6e baki fatuu tayi kaman zatayi kuka"Allah ya jikan mamata yasa tana Aljanna"gwaggo ta amsa da Amin ya Allah,kafin ta d'aura"Aisha ba ruwanta tana da halin kirki,har yau ina jin radadin mutuwarta sai dae ba yadda zanyi Allahn daya fi ni sonta ya d'auke abunshi,Wani lokacin sai inta ganin hada sakaci yasa ta rasu,da tun wuri an kaita asibitin angano cutar dake damunta k'ilan da ta rayu,amman Wannan nasan kawae rudun shaidan ne,ko ankaitan in Allah ya k'addaro a ciwon Ajalinta yake nasan dole sai ta mutu,baffan ki ma yaji mutuwarta wllh don yana son Aisha duk soyayyarta ce ya maido kanki,tun lokacin da ta rasu naso ya bani ke,amman duk kunya irinta fulani haka ya dinga rokona yana hawaye akan na barki acan,lokacin duk da halin da nike ciki ya bani tausayi hakanne yasa na kyale mashi ke kawae don nasan zai kula dake yadda ya kamata,"

Dago kai fatuu tayi"to gwaggo ki k'ara yin aure mana ba sai ki haifi wasu yaranba"harara ta wurga mata,fatuu ta fashe da dariya"Allah gwaggo baki tsufa ba sosae da anyi maki makeup aka nad'a maki gwaggwaro zaki koma kaman Yar budurwa,kinga sai muyi baba anan gidan",banza gwaggon tayi mata,
"Amman to ya akai kika dawo nan garin?",

"wai tambayoyin na miye fatuu,sai kace wata yar Jarida komai sai kin sani",
"Don Allah ni dae ki fad'a man,kinga ko tambayana akae watarana nasani",

"Akwae wani d'an uwan kakanki likita ne sunan shi Doctor Kabeer anan katsina yake,to watarana muka kawo mashi ziyara daga Daura ni da Amadu lokacinne yayi mun tayin aiki yace in inaso zai samarmun don insamu abunda zanci gaba da kula da rayuwarmu,nayi matukar farinciki nan take nace mashi inaso na bashi duk wani bayani da yake bukata,bayan komawarmu da yan kwanaki sai gashi ya kirani ya sanar dani nasamu aikin,lokacin da nazo na iske shi yake tambayata ya na tsara fara yin aikin don bai yuwuwa ince zan rinka zuwa daga daura nan nake sanar dashi zan samu gidan haya in zauna,sai yace in ba damuwa to in fara zama a gidanshi kafin wani lokaci,nan nayi ta mashi godiya naji dadi sosae,cikin sa'a na fara zuwa aikin lokacin Amadu nacan daura amman duk cikin sati sai nasamu lokacin dana je na duba shi,da tafiya ta fara mikawa sai na fara fuskantar matsala da matarshi Rukayya Wanda farko ba haka take mun ba muna zaman lafiya tana jin dadin yadda nike kama mata ayyuka da yake itama lokacin tana aikin koyarwa,amman daga baya duk irin hidiman da nike mata bata yabawa,don lokacin indai banje Aiki ba nike share mata gida,inma yaranta wanka har girki yi mata nike amman duk da haka sai tayi ta wani shan kunu gashi tayi ta nuna man iyaka da wasu abubuwan nasu Abinci ma sai in dafa amman iya wanda taga dama zata zuba man,ta hana yaranta guda biyu Mace da Namiji zuwa wurina da kuwa haka zasu zo muyi ta hira ina masu wasa har Assignment dinsu suke zuwa dashi suyi d'an abunda na sani in fad'i masu dayake lokacin na d'an iya karatu don lokacin da Aisha ke karatun boko tana koya mun,wata rana mai gidan ya aiko wani yaro lokacin tana a d'aki tayi bakuwa,wata aminiyarta ce tazo shine na nufi dakin don in sanar mata sai naji suna wata magana da ta d'aga man hankali,wai ashe dama kawartata ce ta zugeta take man abubuwan da take man alokacin,taci gaba da zugata tana fad'in"yanzu kike yin abunda ya kamata,don wllh da kinyi sake sai dae kiji ana shafa fatiharsu tunda ba wasu shekarune da ita sosae ba gata da kyan jiki,yanzu kamata yayi ki fara yi mata kora da hali har ta gaji ta tattara tabar gidan" jiki a sanyaye na shiga na fad'i mata an aiko wani,daga haka na fito suna bina da wani irin kallo..."dan dakatawa gwaggo tayi tana sauke numfashi,
Chapter 49 · 0% Book details