← Book details Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 137

Sashe 10

Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Detachable shelves t.k ya nufa wadda ke like a sama d'auke da toilet cleaning items,ya ciro safar roba yasa kafin ya daukko liquid cleaner da scrub sponge komawa yayi gaban bathtub ya d'iddiga liquid cleaner din ya wanke,bayan ya gama ya maida robar cleaner din ya daukko disinfectant spray ya fesa a saman tiles din kasa yasa mop ya goge fess,ya ciro karamin towel dake sagale a jikin rack ya goge bathtub din da ya wanke,ya dawo ba ko digon ruwa jikinsa,ya juya ya bud'e seat shima dai fess yake ba wani dirty illa ruwan cikinsa da kalarsu take blue kaman ruwan swimming pool hakan kuma ya faru ne sakamakon cleaner tablet da t.k ya saka ciki lokacin daya gyara part din da safe,hakan na nufin ba'ai amfani da seat din bama,flushing yayi har saida ruwan suka koma fari kal sannan ya rufe,ya yago wipe daga cikin wipe dispenser dake manne a gefen seat din ya goge jikin seat din dan damshin jikin wipe din yasa nan da nan seat din ya rinka wani irin sheki gwanin burgewa,ya jefa wipe din da safar hannunsa a cikin farin wastebin dake a bayan kofan toilet din,har zai fita sai kuma ya hango cabinet a bude,komawa yayi ya duba ciki ko akwae abunda ke bukatan gyara,su toothpaste brushes,sabulai,da turarurrukan wanka ne shake a cikinta,ganin komae a jere lpy lau yasa ya rufe ta ya juya ya fice hannunsa rike Mop da yai amfani ya maido ta cikin laundry ya aje.
Washing machine ya nufa ya bude,ba wasu kaya aciki sai underwears din da Haisam ya cire dazun,juyawa yayi ya duba cikin cabinet din laundryn ko akwae wasu kayan daudan pajamas kala daya ne da Haisam ya cire da safe,ya daukko su ya saka cikin machine din,a ranshi yace "bari da safe in ya cire wasu sai in hada in wanke"ya rufe,dan karamin farin towel mai laushin gaske ya dauka ya koma bedroom din ya goge furniture din ciki wadanda dama suke ta kyalli,bayan ya gama ya fita parlour desk kawae ya goge sai ya dan tattara bakin kofan shigowa ya dau takalman daya aje na Haisam da floor wiper da dan towel din da yayi Amfani ya maida kowanne wurin da ake aje shi,ya dawo parlon hannunshi rike da Air freshner ya feshe parlon wanda dama yake ta sakin k'amshi mai sanyin dadi,maida freshner d'in yayi ya dawo cikin parlon sai da ya bud'e fridge ya dau lemo Fanta ya bud'e yana sha daga haka ya fice bayan ya jawo kopan ta rufe.
T.k,yaron gidan Hajia ne,tun yana d'an karami,Almajiranci aka kawo sa daga wani kauye dake a k'aramar hukumar birnin magaji jahar Zamfara,ta sanadiyar wani dan garinsu Isiyaku wanda ada shine ke Aiki a gidan,to sukan je tare da t.k yana kama masa suna yin shara,da goge gogen motoci sai Aike in Hajia na bukatan wani abu,daga baya isiyaku ya sanarma Hajia cewa zai koma gida don zasu tafi da yayansa neman kudi lagos,Hajia ta bashi shawaran ya tsaya zata sa shi a makaranta yafi tafiya neman kudin nan,amman yaki tsayawa don ba son karatun yake ba,to a lokacin ne t.k ya ce ma Hajia shi ya rika zuwa yana yi mata Aikin? Hajia na Murmushi tace "d'an malam ai harabar gidan nan tayi maka girma baka iya share ta...da sauri t.k yace "da kwarankwatsa zan iya,a gonar babanmu kunya goma nake nomewa kuma wani lokacin har in kara" Hajia taita yin daria jin zancen shi tace "ya sunanka? Yace"Tukur Halliru,ta amince ya cigaba da yin Aikin amman tana shakkun in zai iya don lokacin baifi shekara 11 ba.
Aikuwa t.k yaba hajia mamaki don sosae yake yin aikin ba wani kuskure,gashi akwae ladabi,daya ci ya koshi to fa ba zama Aiki kawae ko ba'ace yayi abu ba yaga ya dace yi yake,a lokacin hankalinsa da karfinsa sun girmi shekarunsa,nan da nan ya shiga ran Hajia tasa shi makaranta ya fara daga primary 4 don ya fad'a mata a garinsu ya fara karatun kafin aka kawo sa karatun Allo,sosae t.k yake fahimtar karatu don lokacin ya dawo gaba daya gidan Hajia da zama tasa shi a wata makarantar Allo dake nan cikin unguwa amman kafin ta aikata hakan sai da taje da kanta har makarantarsu ta sanar da Malaminsu niyyarta ta bukaci ya bata number din baban t.k,aka kuma ci sa'a baban nada waya lokacin ta kira babanshi sosae ta fahimtar dashi tace in yana son karin bayani game da ita ya tambayi Isiyaku,ta ba t.k wayan ya k'ara yimasa bayanin Isiyakun da take nufi,Sosae baban t.k yaji dadi don kafin ta kira sa malaminsu t.k din ya kirasa yayi masa bayanin abun Arzikin data kaima makarantarsu,na kayan abinci,omo da sabulai,da takalma silifas,harda kudi masu yawa tace a rarrabawa Almajirai.
Cike da zumud'i malam halliru ke sanarma matansa guda ukku abun Arzikin daya samu t.k,mahaifiyar t.k wadda itace ta karshe cikin matan tayi tsananin farinciki yayin da sauran kuma bakin ciki ne ya turnike zuciyoyinsu,dama sun takura ma mahaifiyar t.k don suna ganin mijin yafi ji da ita,don uban gidansa ya bashi auran ta,kullum suyi tayi mata gori suna cemata yar sadaka,ladan noma,ita dae bata biye su don hakuri ne da ita.

Malam halliru yaso barin t.k yayi karatun boko don wani malaminsu t.k d'in lokacin har gida yazo ya roki uban daya bar yaron yayi karatu mai zurfi don yana da kokari,amman sauran matan suka tada balae wai sam basu yarda ba yadda aka tura yaransu sukaje suka yi karatun Allo,to dole shima t.k din yaje,ba yadda bai ba ya fahimtar dasu hakan k'aruwarsu ce gaba daya,amman firr suka ki amincewa don bakin ciki,ba k'aramin tashin hankali ya fuskanta ba,ba yadda ya iya haka ya turasa,mahaifiyarsa
Hasiya nata kuka,don ta so yayi karatun,dayake Allah hakimun ne sai gashi tafiyar tasa ta zame masu Alkhairi,rabo kuma ya rantse,Malam halliru ba k'aramin girgiza yayi ba lokacin daya kaima t.k ziyara,ganin cikin daular da d'an nashi yake,bada niyyar kwana yaje ba,amman hajia ta matsa ya kwana,da zai tafi ta hada masa sha tara ta Arziki harda Atamfofi ya kaima matansa.
Zaune malam halliru yayi a tsakan gida yana basu labarin irin Arzikin da t.k yake ciki,ya sanar masu mahaifiyar sanata ce yake wurinta kuma matar tsohon ministan tsaro Gen.Adamu zakee,kaman yadda t.k ya fad'a masa,murna wurin Hasiya kam ba'a magana,sai ma da t.k din yazo da Sallah,har gida aka rinka zuwa ganin tukur dan gidan sanata,haka mutanen gari ke fada.
Private school hajiya tasa shi yayi secondary,bayan ya gama kuma ya tafi Polytechnic dake nan katsina inda yanzu ya shiga ND2 yana karantar SLT,ba faman da Hajia bata yi dashi ba akan aikin da yake ba kaman wankinta da ya hana kaiwar da ake dry cleaning shike wanke mata su fess ya goge a cewarsa baiga abun wahala ba abunda da injin ake yin wankin,Manyan abubuwa irinsu barguna,labulaye da carpet kawae ake kaiwa wurin wanki.
Lokacin da Haisam ya dawo hajiya tace ma tk ya samo wanda zai rink'a gyara masa part dinsa acikin abokansa yan makarantar allon su dake kawo masa ziyara akai akai,nan ma cewa yayi shi duk zaiyi ai ba wani aiki ne mai wahala ba,kuma dama yana bala'en son Haisam,ba k'aramin burgesa yake ba,shiyasa in yana gyara masa part din nasa cike da himma yake aikin,ba algus don dama shi tun yana k'arami aikinsa ba ha'inci,shiyasa in ya dage shi zaiyi abu sai hajia ta kyalesa don tasan zai iya din,kuma ba'a ganin ba daidai ba wani lokacin takan tsokane shi tace "na manta jikan nawa fa kakkarfa ne don tun yana karami kunya goma yake nomewa" sukan yi dariya atare,
Shikam t.k duk yana yin hakanne don hud'ubar da mahaifiyarsa ke masa duk in yaje ganin gida,takan ce ba abunda zamu iya saka masu dashi,haka zakaga ana zuwa gaida t.k in yaje tamkar shine Senator din,iyaye har tura yaransu yanmata suke wae ko zai taya,basu san t.k ya wuce ajinsu ba sai yar birni,in ya tashi dawowa haka mahaifiyarsa zata bashi,su kuka,kubewa,daudawa,barkono da sauran su ya kawo ma hajiyar,mahaifinsa da har hatsi yake bashi ya kawo,Hajiar ta hana tace iya su kayan miyan ya isa ta gode.
Wannan kenan game da Tukur Halliru Birnin magaji,wanda tuni yazama dan gida a gidan Hajiyar sanata don har Senator Ali Adamu zakee yasan da zamansa.

A next page zamu fara nitsawa cikin labarin In shaa Allah,aci gaba da share pls. Thanks as u do so🤝🥰

*💖ASANADIN MAKWABTAKA💖*

*BY OUMMU IMAM📱*

*Paid Book*

*Free Page9️⃣&🔟*

Washe gari juma'a,daga cikin d'aki gwaggo ke magana"Wai fatuu bazaki fito ki tafi ba sai kin makara,kuma a buge ki kizo kina cewa malami kaza ya tsaneki ko" fitowa fatuu tayi sanye da uniform din makaranta hannun ta d'aya dauke da jaka School Bag dayan kuma takalma ne Sandals na roba,a k'arkashin hammatarta ta sak'a jakar ta duk'a tana kokarin sa sandals din saidai igiyan tak'i sawuwa sai faman kici kici take yi dashi a fili tace"Wannan shegen takalmin ni wallahi na gaji dashi" haushi taji ta buga shi da k'arfi a k'asa tace banzan takalmi yaki sanyuwa.
Chapter 10 · 0% Book details