← Book details Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 137

Sashe 38

Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fitowa gwaggo tayi daga d'aki hannunta rike da buta ta nufi band'aki,bayan ta fito har ta nufi dakinta zata shiga sai kuma ta juyo ta nufi dakin fatuu don ta kashe mata hasken wutan da aka maido bada jimawa ba,tana d'aga labulan da niyyar ta sak'a hannunta ta latsa switch ta hango gadonta wayam bata a kwance ajiye butan bakin kopar dakin tayi ta shiga ciki don tabbatar da abunda ta gani aikuwa dai bata a ciki da mamaki cikin ranta tace"to ina fatuun take ne?ko bandaki ta tafi...ai kuma daga can nike tabbas ba can taje ba" rike ha6a tayi tana d'an tunani can ta tuno da d'azun ta tambayeta zata gidan hajiya ai,a fili tace"kar dai wai har yanzu yarinyar nan bata dawo gidan nan ba" tsoki tayi ta juya hanyar fita tana cewa"fatuu ho badai ayi abun arziki da ita ba sai tasa mutum surutu" hanyar zaure ta nufa tana shiga suka hade da Amadu ya shigo hannunsa dauke da kwali ya kwaso kaya aciki ganin gwaggon yasa shi ajiye kwalin a k'asa yana fadin"gwaggo lafia?" tace"lafiya lau fatuu zaka taimaka kaje ka taho da ita kaman yadda aka saba dai"tayi maganar tana yar dariya,shima murmushi yayi yace"wai dama bata gidan ashe" gwaggo tace"eh dazun bayan na dawo tace man wai hajiyar na nemanta shine nace taje amman kar ta bari har ka tashi amman kaga har yanzu bata dawo ba..." daria yayi yace"yanzun haka suna can bacci ya kwashe su,watarana fa haka zaki ga sun hada kawuna sun saki baki suna ta bacci ita da hajiyar sai naje ne nake tashinsu ita hajiyar ta wuce daki" gwaggo dake dariya tace"ina ruwan hajjaju" Amadu yace"amman ki barta ta kwana kawai mana" tace"ba kwanan ke banson tayi ba inda kamar yau asabar ne da sai ta kwana to gobe Monday kaga akwai makaranta kuma na daina barinta tana kwana saboda makarar da take yi duk in ta kwanan kaga kwanaki fa akwai ranar da saidai fasa zuwa makaranta tayi saboda bata dawo gidan nan ba sai wurin karfe tara na safe,shiyasa ma in na aika a taho da ita hajiyar bata cewa abarta saboda tasan makara take tunda ita ba da wuri take tashi ba" jinjina kai Amadu yayi yace"Ok zanje in taho da ita,amman bari in k'arasa shigo da kayan in kulle shagon" gwaggo tace"eh kagama,ni bari in koma in kwanta bacci nike ji sosae wllh dama farkawa nayi naga bata dawo ba"tana maganar ta juya ta nufi dakinta.

Fatuu ce gaba Haisam na bin ta a baya sai faman waigawa take tana satar kallonshi don duk ta tsorata da yanayin shi ga ciwon da yaji saboda ita, suna zuwa gab da k'arshen katangar gidan hajiya Amadu ya fito daga gida ya tsaya yana kulle kiosk dinshi,haisam na hango shi yace ma fatuu "hey..." alamar ta tsaya,juyowa tayi ta kalle shi,taku ukku yayi ya k'araso inda take a hankali yace"don't disclose what happaned to anyone" jinjina masa kai kawai tayi,ganin haka yace"kin gane mi nace" da sauri tace"eh,cewa kayi kar na fada ma kowa abunda ya faru" alama yayi mata da hannu ta tafi ta juya ta tunkari Amadu dake tahowa Haisam na niyyar juyawa Amadu ya dan d'aga murya yace"Ina yini" tsayawa haisam yayi ya d'aga masa hannu ba tare daya amsa ba,

Juyawa Amadu yayi tare da fatuun yana cewa"dama baki yi bacci ba shine kika ki kidawo kaman yadda gwaggo tace maki,kawai don kibani wahala" ya kai hannu zai rankwasheta tai saurin janye kan tace"wad muyal kawu(yi hakuri kawu)" Amadu ne ya fara shigewa kafin fatuu saida ta dan juya ta kalli haisam da har lokacin yake tsaye da sauri ta shige ganin sun hada idanu.

______________________

Zama haisam yayi kan kujera bayan ya koma ya shiga cikin contacts din wayarsa yayi dialing wata number mai dauke da sunan SP khamis,wayan na shiga aka daga gaisawa sukai da mutumin wanda daga ji abokinsa ne daga yanayin yadda suka gaisan,Haisam ya sanar dashi game da incident din daya faru yace ya samu rauni ne a k'afarsa shiyasa ba zai iya zuwa station din yayi reporting ba,Sp khamis najin abunda ya faru yace ma Haisam ya bari zaizo yanzu wannan ba maganar waya bace daga haka ya katse, kwanciya yayi saman kujeran gaba daya ma ya nemi baccin da yake ji ya rasa al'amarin ba k'aramin tada masa hankali yayi ba,imagining kawai yake da baije wurin akan lokaci ba abunda zai faru,d'an guntun tsoki kawai yake ja.

Bayan kaman 30 minutes SP khamis ya iso a bakin gate ya parker motarsa ya fito matashi ne da bazai wuce 33yrs ba, jikinsa sanye da uniform din yan sanda riga blue sai black wando su Officer na ganinsa suka sara masa,Officer p ne yayi masa jagora ba tare da 6ata lokaci ba zuwa part d'in haisam bayan ya sanar dasu wurinshi yazo,
Tura kopan yayi bakinsa dauke da sallama,k'okarin tashi zaune haisam yayi bayan ya amsa masa,fuskarsa d'auke da murmushi ya mika ma Haisam hannu yana fadin"H, Zakee the big COE" haisam da shima yake murmushi yace"SP,ya aiki", "Alhamdulillah gamu a cikinsa" ya fad'a yana kokarin zama a daya daga cikin armchairs din dake parlon, haisam yace"am sorry nasa ka baro aikinka..." SP khamis ya katseshi"Oh no,don't say dat, nan ma ai aikin na zo ko,uhum kana fad'a man yadda incident din ya faru ta waya inason k'ara jin cikakken bayanin al'amarin",

Sigh haisam yayi kafin ya sake mashi bayani a takaice,Sp khamis nata jinjina kai,cike da takaici yace"yanzu ina yarinyar take?" haisam yace"tana gidansu and I ave instructed her not to tell anyone about d incident" jinjina kai Sp yayi"hope basu yi nasarar yi mata komai ba dai??" shiru haisam ya d'an yi yana tunano maganar da yaji goga yayi,yace"bana tunani gaskia",
gyara zama SP yayi"Ok yanzu inason statement dinka sannan itama dole zamu bukaci nata" haisam yace"Owk,lokacin da kuke bukata just inform me,ni bari in rubuta maka" ya k'arasa maganar yana kokarin mikewa SP nace mashi yabi a hankali,d'akin da fatuu ta shiga fitsari ya shiga,hannunshi rike da plain sheet da pen ya dawo cikin kankanin lokaci ya rubuta duk bayanin daya sani ya mika ma Sp khamis dubawa yayi kafin yace"gud,yanzu shi guy din da yarinyar ta fada maka baka san gidansu bane?" girgiza kai kawai haisam yayi alamar baisani ba,
SP yace"dole kenan sai wurin yarinyar za'a samu information din da ake bukata gashi yanzu dare yayi gaskia" shiru haisam yayi kaman mai dan tunani can yace"I think u can get that from the security at the gate,tunda kagan sun dan jima suna aiki anan bazasu rasa sanin guy din ba" Sp yace"yauwa bari in tuntu6e su don so nike zuwa gobe su zo hannu in sha Allah" d'aga mashi kai haisam ya yi yayin da SP ya fara kokarin mikewa hannunshi rike da takardar da haisam ya bashi,ganin haisam din na kokarin mikewa don ya raka sa yace"kai zamanka kawai da na samu information din da nike so zan wuce,komai ake ciki I will inform u,amman kafan nan kaje a dubata gaskiya" haisam dake d'an murmushi yace"don't worry nayi mata duk abunda ya dace yanzu" SP dake sauraranshi yace"bafa Hardware ko software bace da zaka ce kayi abunda ya dace,u need to go hospital saboda ba dressing kawai kake bukata ba you also need TT Injection and some drugs like anti-biotics nd pain reliaver"

Komawa yayi ya kwantar da bayansa yana murmushi yace"I have taken d pain reliever,amman dama zanje asibitin first thing tomorrow Morning in sha Allah",
SP yace"better,ko kazo na kai ka wani pharmacy a duba ka" girgiza masa kai yayi"thanks,ba sai kayi wahala ba" ta6e baki yayi jin abunda Haisam d'in yace daga haka ya nufi hanyar fita yana fadin"My regard to hajiya pls" haisam yace"Owk zata ji,sai da safe" SP yace"Allah ya tashe mu lpy" daga haka ya fice.

*💖ASANADIN MAKWABTAKA💖*

_A heart touching love story_

_*BY ZAINAB LALUH📲*_

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

*3️⃣1️⃣*

Washegari da safe Gwaggo ce acikin kitchen tana ta kwala ma fatuu kira "fatuu,fatuu.." fitowa tayi jikinta sanye da uniform d'in makaranta ta nufi kicin daidai lokacin da ta iso bakin kicin din zata shiga gwaggon ta fito"wai mi kike yi ne nike ta faman kwala maki kira kin k'i fitowa?" fatuu tace"shiryawa fa nike,a gwallijam" gwaggo dake ta kallon fuskarta tace"Jam sumul,kije wurin Amadu ki kar6o madara da milo ki maza kizo ki karya kumallo karki makara" tace "to biredi fa?",

"a'a akwai wani saura zai ishe
ki"gwaggo ta bata amsa,
"To ke bazaki ci ba,ai badai tuwo tunda bakiyi ba jiya?" Gwaggo tace"eh zan bada a siyo man waina gidan ladidi,ke ki ci biredin kawai" gyada kai fatuu tayi har ta juya gwaggon tace"miya same ki a goshi ne naga yayi ja?"
Damm gaban fatuu ya buga, juyowa tayi tana kyakkyafta idanu tana tunanin k'aryar da zata yi ma Gwaggon don dama ko Haisam baice karta fad'a ba,ba fadin zata yi ba,

"Bugewa kikai ne?"gwaggo ta sake tambaya,da sauri tace"eh jiya ne da Hajiya tagan na fara bacci ta tada ni in taho gida shine cikin magagin bacci na bugi bango awurin fitowa, bayan na fito ne na hadu da kawu Amadu" ta k'arasa tana dan kare gefen bakinta da hannunta don kar ta lura da bakin duk da daga ciki ne ya fashe,girgiza kai gwaggo tayi tace"maganin mara jin magana kenan da kin taho da wuri kafin baccin ya kwashe ki ai da ba haka ba,tafi ki amso abunda nace maki lokaci na tafiya" juyawa fatun tayi ta nufi hanyar fita.
Chapter 38 · 0% Book details