← Book details Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 137

Sashe 23

Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washegari Safiyar Lahadi,Fatuu na zaune a ajinsu na islamiyya,tana ta zuba ido taga zuwan Haulat don dama tana riganta zuwa saboda gidansu Fatun yafi kusa da Islamiyyar inta biya ma haulat d'in ta koma baya sosae,sai dai ko in haulat din ta fito da wuri su hade sai in an tashi ne suke tafia tare,
Har aka kusa tashi shiru haulat bata shigo ba,hakan yasa fatuu ta fara damuwa a ranta kuwa tunani ta shiga yi tana fadin"To lafia haulat bata zo ba??,sai kace ba fushi fatun take da ita ba,duk tabi ta damu,har aka tashi islamiyyar Haulat bata zo ba,hakan yasa fatuu ta yanke shawarar zuwa gidansu ta gani ko lafia,
Tafe ta ke ita kadai a hanya don sam bata da k'awar da take tare da ita inba haulat ba, duk wadda ta fara k'awance da ita ba'a daukan lokaci ake rabuwa ta tsiya tsiya,
da fatuu taga mota ta taho sai ta rufe fuskarta wai don kar ace mutumin nan ne na gidan hajia,dama ko da safe da zata zo islamiyyar cikin dar dar ta fito daga gida,karshe ma da gudu ta shige lungun jikin gidan hajiyan duk don kada Haisam ya fito su yi kacibus,a ranta ta ke cewa"Yanzu shikenan sai dai in daina zuwa gidan Hajiar...."ta girgixa kai a fili tace"kam aikam bazan daina zuwa ba tunda ma naga hajiyan bata sani ba ai" "to kuma in ku ka had'e wata rana yace ma hajiyar kece ki ka fasa masa gilashin mota fa?? wani 6angare na zuciyarta yace, sosae gabanta ya fad'i ta kasa cewa komae,
Daidai lokacin da ta karya kwanar da zata hau layin gidansu a lokacin kuma Gaye da Abokinshi suma suka shigo kwanar,kai da kagansu sai dai kace Allah ya shirya,tun daga kan askin kansu har zuwa shigar da suka yi,tsayawa yayi yana yin arba da Fatuu,ya rik'e baki da hannunshi guda yace "Kee! Wai har yanzu kina yawo a gari ba'a damk'e ki ba?
Wani irin kallo Fatuu tayi mashi tace "A damk'e ni akaini ina? Gaye yace" inda ya cancanta akai ki wato gidan yarii...." Idanu waje Fatuu tace "kaji man gaye da Muguwar fata,yo minayi za'a kaini gidan yari??? Wata yar iskar dariya yayi "Oh baki ma san mi kika yi ba ko,to glass din mota da kika fasa ma wannan mutumin rannan.."sakin baki fatuu tayi tana kallonshi cike da mamakin yadda akai yasan hakan,ya ci gaba
"nasan komae yarinya ki ke wani kallo na,don akan ido na kika jefi motar,Oh ke kin d'auka kin jefi banza ko" ya k'ara shek'ewa da dariya "to billahillazi baki ci bulus ba,ruwa kika 6allowa kanki,don kud'in wannan glass din ko wanda ku ka fito ciki d'aya kika fasa mawa na rantse da sarkin da yake busan numfashi bazai kyale ki ba,yo kin kuwa san nawa glass d'in nan yake?
Fatuu dake tsaye kaman gunki zufa har ta fara tsatstsafo mata ta girgiza masa kai alamar a'a,gabanta sai fad'uwa yake,Yace "to wannan gilashin yayi naira miliyan d'aya,don ita kanta motar zata yi miliyan 10..." Fatuu ta zaro idanu waje gaba d'aya,sai Maimaita million d'ayan take a cikin ranta,a razane tace "Nawa ne Miliyan d'aya? Gaye da ke kallonta,da mamaki yace "yo ke dama hakanan kike zuwa makaranta kwalwar kifi ce dake,miliyan d'ayan ce baki sani ba? Da sauri tace"nasani, kawae yawan kudin ne a zahiri ban sani ba don ban ta6a ganinsu ba" Gaye ya gyara tsayuwa yace "to kinsan dubu d'ari?" "dubu d'ari..." ta maimaita tana dan tunani,can tace"Eh nasani,Baffa na ya ta6a saida shanuwa dubu dari da talatin kuma har kud'in ma na rike a hannuwana,daya hannu na rike dubu d'arin,dayan kuma dubu talatin d'in" da sauri yace"Yauwa toh,ita dubu d'arin irinta sau goma sune miliyan daya,kudin gilashin kenan,ai mu ma barshi a kudin shanuwar sau goma kawae..." Cikin tsananin tashin hankali Fatuu ta katse shi, "kace kuma dubu d'ari sau goma yanzu kuma kace duka kudin shanuwar...." Gaye ya katse ta"Oh kina nufin baza'a biya kudin gyara ba kenan,ai dole abashi harda na wanda zai yi aikin sa glass din ko Aljana" Idanu waje fatuu ke kallon gaye tama kasa yin kwakkwaran motsi ga zuciyarta dake bugawa ba k'akkautawa lokaci guda taji fitsari na niyyar zubo mata,kana kallonta zaka fahimci tsananin tashin hankalin da take ciki ba kad'an bane, zuciyarta kuwa tana bugawa tana maimata mata "kudin shanu gomaaa!!!"
Kamar Gaye yasan abunda take fad'a a zuciyanta yace "kin dai san bazan maki karya ba,don ba inda bama fad'awa a Nigeria,har legas dai tasan da zamana,ba kalar motar da bansan kud'inta ba,ke har kudin jirgi na sani balle wata mota k'aramar Alhaki.

Abokin gaye da tunda suka tsaya bai tanka ba kunnansa d'aya mak'ale da earpiece yana sauraron waka yana dan jujjuya kai,yasa hannu ya cire earpiece din yace"Baabah wai yane? mi tayi ne naji sama sama kana ta mata bayani harda uban lissafi?" Gaye yace "ruwa ta 6allo ma kanta baabah....,nan ya bashi labarin abunda fatun ta aikata,
yace "na gidan da muka wuto yanzu ka ke tambayata gidan waye,nace ma gidan Uwar Sanata ne kuma Matar tsohon Ministan tsaro? Abokin ya gyad'a kai alamar"Ehh,gaye yace"to mutumin gidan ne ta yi ma wannan aika aikar,don ni farko ma bansan d'an gidan bane ina dai d'an ganinshi kwanan nan yana wucewa a Motoci kala kala,har wani gangamemen Bike yake hawa,ina jin wannan bike din yayi million goma shima ko ma fi, sai shekaranjiya tsoho yaja ni zuwa sallar juma'a a Masallacin gidan,na ganshi tare da Hajiyar sun zo suma,to nan nagane dan gidan ne ashe"
Ya cigaba"Kasan masu kudin nan da shegen wayo,in suka gina tangamemen gida sai suyi dan Masallaci wai Allah ga naka,don kar a masu surutun basuyi ba,duk da dai su nasu babba ne" yana maganar yana watsa hannuwa sai kace mai yin debate,
Abokin fuskarshi da mamaki yana jinjina kai yace "kai kace master ce ta rashin ji" Gaye yace"ehh mana,wannan da kake gani furofesa ce ba master ba,don inta 6allo wani aikin yasin ko ni jinjina mata nike,dubi dai abunda ta aikata yanzu ni yaushe zan fara haka,ban aje ba,ban ba wani ajiya ba,Iyaye kuwa sai dai ace lahaula saboda talauci" yana maganar yana wani janta,
Abokin ya kwashe da daria yace kama aikatan ai kasan inda za'ai da kai,billahillaxi gidan yari straight inbaka biya ba,aje aita cin gabza.."Gaye ya tuntsire da dariya yana rik'e wando,
Yace"Allah yai man tsari da cin gabza baabah,shiyasa nike taka tsantsan,nadai je cell inyi kwanaki in fito don wannan yama zama gida,don ina daraja tuwon gyatuma ta,baka sanin dadin shi sai an had'aka da gabza yasinn..." gaba d'aya suka tuntsire da wata yar iskar dariya,ita dai Fatuu sai kallon su take tamkar yau ta fara ganinsu,zufa kuwa tuni ta lullu6e fuskarta,sai had'iyar miyau mai d'aci take.
Abokin gaye ya kalleta cikin nuna tausayi yace"Wayyo baiwar Allah na tausayi maki wllh,yanzu zaki bar tuwon gyatumarki ki koma cin gabza,duk wannan hasken fatar naki da kyawun fuskar ki sai ya disashe qur'an,in kuma kina da gashi to duk kwarkwata sai ta cinye shi,sai dai ko in kuna da kud'i sai ku biya shi abunshi kawae...."
Gaye ya katse shi da sauri "yo ina suka ga wani kud'i duk kanwar ja ce yasin,itafa kakarta ke ruk'onta kuma in fada maka kakar attendar ce a asibiti irin masu share share da goge gogen nan,ina zata ga miliyan d'aya ai yasin ko nayi rantsuwa bazanyi kaffara ba,ko kwatan miliyan bata da"
Abokin yace "Kace dai dole sai anje an had'e da gabzar dai...." da sauri Gaye yace "Comfat,don a ranar sai da ya tambayeni nayi masa kwatancen gidansu,shiyasa nayi mamaki dana ganta har yau ba'ai ramm da ita ba, amman nasan kilan sunje basu samu kowa a gidan ba,kuma kaga jiya da yau ba aiki,amman na tabbatar gobe Monday dole azo a damk'e ta",

Ya juya kan Fatuu yace "To Aljana,sai ayafi juna,sai Allah kuma ya k'addara za'a sake ganawa,don can d'in ba sauki, wasu ma wuya ke kashe su, nidai na yafe maki" daga haka ya juya kan abokin nashi yana fad'in "hayya,Baabah mu ware ko.." suka yi gaba abunsu suna wata yar iskar tafia.

Kasa motsawa Fatuu tayi daga inda take don k'afafunta ba k'aramin nauyi sukai mata ba,Kalaman gaye na k'arshe sun matuk'ar razana ta"Ashe mutumin har yasan gidansu...! Shine abunda ya kara tada mata hankali,kallonsu gaye tai tayi har suka 6ace ma ganinta, irin su Gaye sai su kashe mutum,don halin da Fatuu take ciki tsaff zuciyarta zata iya bugawa don tunda take bata ta6a janyo rigima irin wannan ba,iya ta 6arar ma yara abu gwaggo ta biya ko ta bugi mutum har ta raunata shi gwaggon ta biya kudin zuwa chemist ta tsaya,yau gashi ta janyo rigimar da tabbas tafi karfin gwaggon,duk'awa tayi a wurin don kafafunta rawa kawae suke,ga kwakwalwarta sai tariyo mata da maganganun gaye take,bugun zuciyarta na k'ara tsananta ga zufa da ta wanke mata fuska har wuyan Hijab dinta ya fara jik'ewa,da za'a auna jinin Fatuu a lokacin tabbas daba k'aramin hawa yayi ba.
Tsawon mintuna Fatuu na duk'e a wurin kafin tayi k'arfin halin mik'ewa ta fara tafiya a hankali,da kyar ta ke taka k'afafunta da sukai mata wani irin nauyi,a ranta kuwa ba abunda take Maimatawa fa ce "Kud'in Shanu Gomaaa..!!!!"

*Littafin A Sanadin Makwabtaka 300 ne,ga mai bukatar ci gaba da karanta shi bayan angama Free Pages sai ya tuntube ni ta wadannan numbers din 09016265659 ko 09013804524,pls just whatsapp message banda phone call,Thanks🤝*

*💖ASANADIN MAKWABTAKA💖*

*BY ZAINAB LALUH📲*
~(Oummu Imam)~

*Paid Book*

*Free Page 21
Chapter 23 · 0% Book details