Sashe 16
Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Mik'ewa yayi bayan ya idasa cinyewa ya d'au cup d'in kunun ayar ya nufi cikin parlon hajia na fadin "Fruit salad d'in fa? Hannun da ba komai ya d'ago mata ba tare da ya juyo ba yace "bansan ina zan sa shi ba" ya idasa shiga cikin parlon ya kishingid'a saman kujera 2 seater yana d'an kurbar kunun ayar yana kallon T.V,bayan wani dan lokaci itama hajia ta mik'e bayan ta zuba fruit salad din acikin d'an bowl tasa cokali ta nufo cikin parlon tana kwala ma Saude kira,da hanzari sauden ta fito tace "gani hajia" hajia ta juya tace mata"Je ki clearing dining din mungama" "to" Saude tace ta nufi Dining area din ta kwashe duk abubuwan da sukayi amfani ta kai Kitchen banda Warmers d'in Abincin don gidan hajia bai rabuwa da bak'i manyan mutane,ba kamar yau da yake Friday ta tabbatar wasu zasu zo a buk'aci ta basu Abincin,tasa towel ta goge wurin yayi fess kaman ba'a zauna anci Abinci ba.
*💖A SANADIN MAKWABTAKA💖*
*Mallakin*
⬇️
*ZAINAB LALUH*🌹
*(Oummu imam)*
*Littafin A Sanadin Makwabtaka 300 ne,ga mai bukatar ci gaba da karanta shi bayan angama Free Pages sai ya tuntube ni ta wadannan numbers din 09016265659 ko 09013804524,pls just whatsapp banda phone call,Thanks🤝*
*Free page1️⃣4️⃣&1️⃣5️⃣*
Saman kujerar dake opposite da wadda Haisam ke kishingid'e hajia ta zauna tana shan fruit salad d'in da ta d'ebo tana yi tana kallon American film din da Haisam d'in ke kallo,
"Dad called me when I was in office" Haisam yace ba tare da ya kalli Hajiyar ba,d'an ta6e baki tayi tace"Ai nima dai ya kira ni tunda safe,yayi man barka da juma'a" yar daria Haisam yayi yace "Jealous Old Woman" itama dariyar tayi tace "ai don kasan yafi ji dani" gyad'a kai yayi yace "I knew,shiyasa ma koda ya kira ni maganar ki yayi man" da sauri Hajiya tace "Maganata kuma? Kai ya d'aga alamar Ehh,tace "to wace magana ce da ni bai man ba da ya kirani sai kai zai yi mawa,ko dai gulmata ku ka yi?" ta dakata da shan fruit salad d'in tana kallon shi alamar shi take jira ya bata amsa,
sai lokacin ya juyo da kanshi yana facing d'inta yace "gulma kuma,No kema kinsan baza muyi hakan ba" ya d'an dakata,sai kuma yaci gaba "Ya tambayi yaushe zan kai mashi ke ne" wani irin kallo tayi mashi tace "Ka kaini kuma,da can da nike zuwa lokacin baka k'asar kai ke kaini? Yar daria yayi yace "to ai yaga kin dade baki je bane shi kuma yana son ganin ki" d'an ta6e baki tayi tace "to tunda yana son ganina sai yazo ya ganni,haka itama waccan ta lagos d'in last week ta kira ni tana ce man wai don Allah inje ta na son ta ganni na...." Haisam ya katse ta "Aikine yayi masu yawa they're always busy" hajia tace "To ni ban aikin ne?" murmushi yayi yace "Kina yi amman ai ba kaman su ba,ke You are less busy kuma Aikin naki is voluntary ke kika sa kanki...."katse shi tayi da cewa "Ai dai duk aiki aiki ne" tayi maganar a harzuk'e daria yake yace"ni daman ai baki ji nace aikin ki ba aiki bane Celebrity" da d'an murmushi tace "Ni ce celebrityn? Yace " Yeah,anata son ganinki kina wulakanci" yayi maganar cikin wasa,dariya Hajiya tayi tace "Miye abun wulak'anci don nace duk mai son ganina yazo inda nike" dan ta6e baki yayi yace "I think suna son kije kid'an kwana biyu ne" tace "Ai ina zuwan ko,kawai ni haye-hayen jirgin ne ba so nike ba wllh" ta k'arasa maganar fuskarta dauke da damuwa,ta aje bowl din saman sofa table kusa da cup din kunun ayar da Haisam ya sha ya rage kad'an,Sannan ta maida Kallonta kan hoton Sojan mutumin nan ko kyaftawa ba tayi.
Ganin yadda ta k'ura ma hoton ido yasa Haisam d'an juyar da kanshi shima ya kalli hoton,girgiza kai ya d'an yi ya juyo da duban sa kan Hajiyar yace "Ba lalle silar ajalin ya zama d'aya ba Sweethrt" "I know" hajiya tace,ta kauda kanta gefe har lokacin da damuwa a fuskarta,
"In bakya son hawan jirgin ne ki fad'a ma Dad sai asamo k'wararran Driver da zai rink'a kai ki",
Uhmm tace batare da ta waigo ba,ya cigaba"Ita kuma lagos d'in in zakije sai ki rink'a hawa luxurious Bus...." da sauri ta juyo tace"Waye zaije lagos a Bus?" Yace "Ke mana tunda bakya son hawa jirgin ko" yayi maganar yana dariya,itama Hajia dariyar tayi tace "tabb inje lagos a mota,aikam in na isa saidai k'ilan a kwashe ni a Wheelbarrow" gaba d'aya suka sa dariya "Saboda me? ba bakya son hawa jirgin ba" tace "Eah amman hakan ba yana nufin zan daina hawa jirgin ba in koma hawa wata Bus can" gyad'a kai yayi ya maida duban shi kan TV,
"Yanzu yaushe zance mashi zaki je? ya tambaya ba tare da ya kalleta ba,da sauri tace "Ina wai? yace "ABJ" ajiyar zuciya tayi tace "zanje amman fa ba yanzu ba,dana samu isasshen lokaci Lagos zani don har ta turo man da kudin jirgi,duk da ma wannan kud'in sunfi karfin kudin zuwa lagos ta dai turo man ne kawai",
"Har nawa ta turo maki kud'in flight? Ya tambaya,tace "1 million" nodding kai yayi yace"kice bribe aka baki kawai,shiyasa zaki ce lagos zaki,to ki maida mata kud'inta ni zan baki 3m ki tafi Abujan..."da sauri hajiya tace "ban mayarwa,wato ka maida ni ma uwar son kud'i kenan" tayi maganar tana ta dariya,shima dariar yake yace "Aikam zanyi reporting d'inki ICPC,ince ga wata Mom din Senator kuma matar Former Minister of Defence ta kar6i cin hanci..." Hajia tace"Yi sauri kar k'uda ya riga ka"gaba daya suka kwashe da dariya.
Hajiya ta ci gaba da magana "ni ina zan iya da jarabar Momynku ta lagos,yanzu abun ince mata bazan samu zuwa wurinta ba,kuma taji na tafi Abuja kaji masifa" Haisam yace "Ai ke ta biyo" da d'an zare ido tace"Masifar?" yace"Eah mana" ta6e baki tayi "tunda fa ka raina ni ai komai kace man" murmushi yayi yaci gaba da kallon American film din da ake,
"Wai ni ya FANAN take kwana biyu bamuyi magana ba nasan dai hakanan bata k'in kirana sai dai ko yanayin karatun ne ya hana,ni kuma ban kira naji ya take ba" d'an lumshe idanu Haisam yayi kafin yace "baki damu da ita bane" hajia tace "Aikuwa ni na damu da ita tunda na damu da kai,tunda duk abu d'aya ne ko" murmushi kawai yayi batare da ya waiwayo ba,
"Ina son yarinyar saboda akwai hankali ga sauk'in kai sam bata d'auki duniya da zafi ba,ba kamar yar'uwarta ba" haisam yace"wa kenan? tace "FARHA mana,kai wannan yarinya sam halinta ba irin na yar'uwarta bane,ta cika girman kai,ta d'au kanta wata tsiya,ni ina ganin acan dangin Babanta Turawa tayo gadon halinta" dariya haisam yake yace"ko kuma danginku ko..."da sauri Hajia tace "Haram,wallahi mu bamu da wannan halin kaima sai dai in ka k'i gaskiya ko akaina ai kaga misali ba ruwana sauk'in kaine dani ba kuma yabon kai ba atoh,yarinyar nan fa ko kirana
bata iya yi ina matsayin
kakarta sai dai in muna waya da uwar in na tambayi yasu Farha,shine fa in tana kusa tace man gata hajiya,in kuma bata nan ne inta dawo sai ta kira ni tace Hajia ga Farha d'in ku gaisa",
Ajiyar zuciya Haisam yayi sai lokacin ya juyo yana kallon hajiyar,ta ci gaba "ko gidan fa naje yarinyar nan bata iya zama muyi fira,bare kuma tazo d'akina don ta gaida ni, ko da safe wani lokacin in mun hadu a dining don yin Breakfast sai ni ce zance Hajia farha antashi lafiya,sannan za kaga ta wani yamutsa baki tace "Good morning granny" hajia tayi maganar tana kwaikwayon yadda Farhan ke yi da baki,shi dai Haisam sai daria yake yace "Ni kuma kinga in muka had'u lafia muke gaisawa though dai bama wani magana ma sosae,tace "Yo kaida ita ai duk kanwar ja ce,kawai dai kai sai mutum ya zauna da kai zai fahimci saukin kanka amman kaima wani lokacin ai ba son magana kake ba,amman Farhaaa huu badai girman kai ba wllh" ta6e baki ya yi yaci gaba da kallon shi.