← Book details Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 137

Sashe 17

Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

"Ai wallahi Allah ya yabawa aya zakinta,da bai sa Farha ce ke da kyau da sura irin ta Fanan ba,Wai! da bansan a ya zata rik'a duban mutane ba a hakan ma ya aka cika,ita kuwa Fanan dayake Allah yasan kyakkyawar zuciya ce da ita sai ya had'a mata harda kyaun sura" juyowa yayi yana duban hajia yace "Kina nufin Farha bata da kyau? da sauri tace "ina taga wani kyau da wani hancinta kamar ansammata,idanuwan ma ba wasu masu girma ba,sai uban kumatu,sak uwarta ta biyo hasken ne kawai na uban sai d'an gashin kuma" haisam yace"You see,if to say wani ya fad'a maki baki da kyau da kinji haushi,amman yanzu da bakin ki kin fad'a".
Hararar shi tayi "Ni d'in ce banda kyau?" yace "yeah,kince Farha bata da kyau...." da sauri ta katse shi "to ni uwarta ce,ko baka ji nace da mamarta take kama ba?
"To miye marabar ki da Mommyn Lagos d'in?" Jimm hajia tayi tana tunani,dariya Haisam yayi yace" I know you won't deny cewa kuna kama dama,don sak fuskan Mommyn Lagos taki ce,she's your duplicate" ya k'arasa maganar yana ta daria ganin yadda Hajiya ta kasa magana,can tace "naji to,amman duk da haka nafi ta kyau" tayi maganar tana daria itama,girgiza kai Haisam yayi "yanzu kina nufin kinfi Farha kyau kenan? tace "Eah hasken fata ne kawai tafi ni sai d'an gashi kuma" nodding kai yayi "Lalle,nan gaba ma har Fanan d'in cewa zaki kinfi ta kyau da alama..." da sauri Hajia tace "nan fa d'aya ai ko giyar wake nasha bana ce nafi Fanan kyau ba yarinyar da har uban nata tafi shi kyau,inaga itama acan cikin danginshi turawa ta samo kyaun nata,kaga kenan ita Farha ta d'aukko hali maras kyau,Fanan kuma sai ta d'aukko kyawun sura" gaba daya suka kwashe da dariya,cikin fahimta suke firar tasu da gani kasan akwai kauna mai tsanani a tsakaninsu.
Telephone ne ya fara ringing alamar ana kira,Haisam ya yunk'ura don ya d'auka hajia ta tsaida shi "Yi kwanciyarka bari na d'auka dama na gaji da zaman" ta nufi inda telephone d'in yake ta kara a kunne tace "Hello,Salamu Alaikum" daga d'ayan bangaren akace "W/salam Hajia you have visitors" tace"Okey,hold on" ta rik'e kan telephone din ta fara waige-waige alamar tana neman wani abu,haisam ya d'an kalleta"lafia? Ya tambaya,tace "Eah nayi bak'i ne ina son inga su waye,na rasa ina na aje ma wayan tawa" yace "I don't think tana parlon nan don tunda na shigo banga wayan ba" tace "Oh! namanta tana bedroom kuwa da zan kwanta na aje ta,bari Saude ta d'aukko ma....." Haisam ya katse ta "Let me change it to CCTV" ya k'arasa maganar yana k'okarin canza kallon da ya ke zuwa cctv,nan da nan sai ga vedios din 6angarorin gidan sun bayyana a kan TV d'in,kan vedion farko mai dauke da rubutun CAM01 daga k'asan rubutun ansa Gate ya shiga vedion wajen gate din gidan ya bayyana,wata mota ce a gaban gate d'in mutanen da suka zo kuma suna cikin motar hakan yasa hajia fad'in"to ni bamma gane su waye ba,sai mota kawai nike gani ko sai nasa glass...."Officer da yake jiran umarnin hajia jin abunda take fad'a ta cikin telephone d'in yasa shi lek'o da kanshi ta d'an karamin windon d'akin da suke zama irin na masu gadi wanda window d'in ta fito waje yayi ma wanda ke a mazaunin driver magana,mutumin ya leko da kanshi,hajiya ta k'ura ma mutumin ido tana k'okarin gano ko waye....can ta buga salati tace ma Officer dake jiran umarninta "Officer let them in" yace "Ok",
Kallon Haisam tayi tace "Kawunku ne fa" ba tare da ya kalleta ba yace"Wane Uncle? tace"kawun ku Mani,na daura" "Ok" yace ya fara k'okarin mik'ewa hajia tace "Ina zaka kuma? Yace "Zan baku space ne",
"to amman ai yakamata ka tsaya ku gaisa ko" komawa yai ya zauna ya ciro wayarshi daga cikin aljihun rigarsa yafara daddanawa.

Wasu Dattawa ne su ukku suka shigo na farkon daya fara shigowa yafi sauran jiki da tsawo,bak'i ne yana sanye da manyan kaya farar shadda had'i da babban riga da hula,sai na bayansa shima shadda ce jikinsa saidai ta d'an ji jiki kuma kalar babban rigar daban ta yan cikin ma daban,sai na ukkun wanda shi yadi ne jikinsa riga da wando da hula kuma duk bai kai girman sauran ba.
Hajiya na ganin mutumin na farko ya shigo ta mik'e fuskarta d'auke da fara'a da alama shine Kawu Manin,shima yana ganinta ya washe baki yana fadin"Hajjaju makkatun wa madinatun,Hajiyar Minister,Hajiyar Senator " cikin dariya Hajia tace "duk ni kadai" yace"Eh mana ai duk sunanki ne" ya karasa maganar yana k'okarin zama a kujerar dake kusa da ta ta,ta kalli wad'anda suka zo tare tace "Bismillah,ku zauna" suka amsa da "to" suka zauna,sannan suka fara gaidata cikin girmamawa,da fara'a ta amsa masu,ta maida duban ta kan Kawu Mani tana fad'in "kuyi hak'uri fa an barku waje kuna ta faman jira,su ba ruwansu ko da mutum yana zuwa indai ba akai akai ba sai suce sai sun tambayi izini zasu barshi ya shigo",
Da sauri Kawu Mani yace "Ah ba komai wllh,ai hakan is part of their work,ba kamar yanzu da ake fama da matsalar Insecurity hakan shine daidai,don shi mugu zai iya zuwa da kowacce suffa ya cutar da mutum" Sauran suka jinjina kai sukace "gaskiya ne" Kawu Mani yaci gaba "Allah dai ya k'ara tsaremu da tsarewarsa,don Al'amarin sai dai Addu'a kawai itace zatai mana magani" Gaba d'aya suka amsa da "Amin" harda Hajia,
Chapter 17 · 0% Book details