Sashe 125
Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
A 6angaren Fatuu kuwa tunda sati na biyun ya kama ta kimtsa kayanta tsaf tana jiran ranar tafiya kullum in aka kwana sai tace saura kwana kaza yau da ya rage saura kwana d'aya su cika sati biyu sam ta kasa zaune ta kasa tsaye har bata iya 6oye farincikin da take ciki su kam su yadikko basu son ta tafi ba kamar kannenta tuni sun fara jin kewarta ba kamar Mino duk tafi kowa damuwa har cema Innarta tayi itama abarta ta koma can yadikkon tace a'a abun zaiyi yawa karma ta sake jin ta fadi haka, a ranar da daddare bayan Baffanta ya dawo ne yake sanar da ita tafiyarsu gobe Asabar bazata yuwuwa ba sai jibi in Allah ya kaimu don akwae siyayyar da yake son yi mata kuma sai goben ne Kasuwar da zaije ke ci cikin abunda zai siyo harda sak'on Fatun na tsarabar da zata kaima Haisam ba haka taso ba amman jin harda tsarabar Haisam za'a siyo yasa ta hak'ura hakan kuma ba k'aramin dad'i yayi ma Mino ba, a kwana a tashi ba wuya a wurin Allah duk abunda aka sama rana zai zo harma ya wuce a daren ranar Lahadi baccin Fatuu ragaggene saboda d'oki har k'agara tayi garin ya waye, Asubahin farko ta farka ko jiran yadikko batayi ba taje ta d'aura ruwan wankanta lokacin da yadikkon ta farka saidae ta ganta tana shiryawa da sabbin kayan Fulanin da Baffanta ya siyo mata Navy blue, Murmushi kawae tayi don ta gama fahimtar duk zumudin saboda taje taga Haisam ne, ana gama sallan Asuba suka fito don tafiya dama tun jiya da daddare tayi ma kowa sallama kuma ba laifi sun bata Abubuwa harda kudade haka Mahaifinta ma da Yadikko sun had'a mata sha tara ta arziki, har kopar gida suka rakota dama shi Amadu tuni sun fito shida Kamalu don zai rakasu ne, Mino nata matsar kwalla don itama sam batayi baccin kirki ba saboda tafiyar Fatun da ta saka a ranta gashi an hana tayi masu rakiya zuwa Jimeta inda zasu hau Mota, suna ta d'aga masu hannu bayan sun hau Mota Baffanta yaja suka tafi, Lokacin da suka isa jimeta basu samu Motar da zata kaisu direct Katsina ba hakan yasa suka hau ta Kano har saida suka ga tashinsu suna ta d'aga masu hannu cike da kewa suna masu Fatan Allah ya kiyaye hanya ya kaisu lafiya.
Sam bata jin tafiyar ko bacci ta kasa yi burinta kawai ta ganta a Katsina hakan yasa bata takura ma Amadu ba sosae, sai bayan Azahar suka iso Kano ba 6ata lokaci suka samu Kano line mai zuwa Katsina, tunda suka kamo Hanya take ta sakin Murmushi don har ta fara jiyo kamshin Katsina, akace wai karfen Nasara ba Tabbas kwatsam Mota ta lalace masu a hanya har sunyo nisa sun kusa garin Kankia ta jahar Katsina, tun ana ganin zata gyaru har aka fara fidda ran gyaruwarta duk Mutanen ciki sun fito waje sun zazzauna a gefen hanya ciki harda Fatuu tana a wurin da Mata suke fuskar nan sam ba annuri murna ta koma ciki sai tsoki take bugawa Matar dake kusa da ita tun a Mota mai kirki ko abu zata ci sai ta bata ita ke bata baki tana nuna mata tayi hakuri komi Allah yayi mai kyau ne k'ilan da akansu matsalan zata faru ta faru akan Motar, ita dae jinta kawae take can ta mik'e ta nufi wani gida dake can gefe inda taga ana zuwa yin fitsari taje tayo bayan ta dawo ne ta nufi inda Amadu yake tana ta tura baki tace mashi wai ba'a kusa Katsinar bane su k'arasa ko a k'afa ne, wani kallo yayi mata kafin yace "an kusa baifi awa guda da wani abu ba sai ki taka ki k'arasan" yay Maganar yana harararta tana tura baki tace "ai wllh don bansan hanya ba dana tafiyata",
d'an girgiza kai yay yace" indai hanya ce wannan ba matsala bace mik'ewa zaki sambal kita tafiya ba sai kin sha wata kwana ba zaki ganki har Katsinar" maimakon ta tafin sai ta tsaya tana tura mashi baki yace ta tafi ta bashi wuri ta juya Mutanen dake kusa dashi na mata dariya ganin tak'i ta tafi a k'afan ta koma ta zauna. Da kyar aka samu ta gyaru don da har direban ya fara tunanin buga waya a turo masu wata duk da hakan ba k'aramin dare zaisa suyi a hanya ba tunda yaushe Motar tazo har suka tafi, Hamdala Mutane suka shiga yi suna Addu'ar Allah ya kaisu lpy yasa kada ta k'ara lalacewa, ba tare da 6ata lokaci ba suka ci gaba da tafiya saidai direban bai yin gudu kaman da lalla6awa yake su samu su isa Lafiya, Allah sarki gwaggo tana can hankalinta duk ya tashi jin abunda ya faru da ta kira Amadun ya sanar da ita dama akai akai take kira tana jin sun iso ina haka ma can inda suka baro Mahaifin Fatuu da yaya Kamalu suma duk bayan d'an lokaci suke kira suyi masu ya Hanya, Alhamdulillah sai ana sallar isha suka k'araso duk sun gaji likis Fatuu kallabinta a hannu ta fito daga Motar kitson fulanin da yadikko tayi mata nata reto, suna sauka gwaggo ta kira lokacin Amadun na niyyar kiranta ya sanar mata ai koda taji sun sauka nan take ta hau yin hamdala harda yin sujjadar godiya ga Allah, ce ma Amadun tayi bari tazo ta taho dasu yace ta barshi kawae tunda sun shigo gari zasu k'araso lafiya lou, within some minutes suka iso gidan lokacin gwaggo na tsaye jikinta sanye da Hijab tana dakon isowarsu Keke Napep d'in na tsayawa ta nufeta tana masu Oyoyo, saida ta taimaka ma Fatuu ta fito cike da tsantsar farinciki ta rungumeta don tayi missing d'insu sosae duk sai gidan yayi mata ba dad'i saukinta ma tana zuwa aiki, bayan an sallami mai adaidaita sahun tare da gwaggo da Bello daya dawo daga Masallaci ya taimaka masu suka shiga da kayayyakin yay masu sannu da zuwa kafin ya fito lokacin tuni Fatuu ta baje a d'akin gwaggo don akwae wutan nepa atare suka shigo ita da Amadu ya zauna kan kujera ita kuma ta nufi gefen gadonta tana yi ma fatun sannu sam fuskarta ta kasa 6oye farincikinta sai faman tatta6a Fatun take tana yi mata sannu ita dae kai kawae take d'aga mata, mik'ewa tayi ta tafi kitchen ta fara kawo kayan abinci Amadu nayi mata sannu tace ai su keda sannu bayan ta gama kawo komae tace to su saukko suci Abinci, mik'ewa Amadu yay yace shi yafi bukatar yayi wanka kafin Abincin tana jin haka tace to bari ta had'a mashi ruwan wanka yana ta barshi zai had'a tace yay zamanshi, Allah sarki uwa mai dad'i ya ayyana a ranshi kafin ya koma ya zauna, bada jimawa ba ta had'a mashi ruwan dama akwae ruwan zafi a electric kettle data jona saboda su don garin a d'an kwai sanyin damuna, bayan ta dawo d'akin tace gashi can a bandaki yaje yayi yace to, kallon Fatuu tayi tace "to taso auta kici Abinci ko sai nazo na daukeki ne?" girgiza mata kai tayi alamar a'a tace "to daure ki tashi in kika ci abincin zaki ji karfin jikinki" tana jin haka ta yunkura ta fara kokarin saukkowa don tana bukatar karfin jikin saboda taje gidan Hajiya, zuba mata Abincin tayi ta zauna kan darduma ta fara ci ita kuma gwaggo ta hau kan kujera tana kallonta da Murmushi tana k'ara yi mata sannu, ta d'an ci ba laifi ta mik'e gwaggo na har ya isheta tace gidan Hajiya zata je ta fad'i mata sun dawo,
"Ki bari ki huta gajiyar mana zuwa da safe ba sai kije ba" tura baki tayi tace ita dae yanzu zata je ba dad'ewa zata yi ba, d'aga mata kai tayi alamar taje da sauri ta nufi kayansu ta bud'e jakar kayanta ta d'aukko wata bak'ar leda dake k'ulle sai kuma ta bud'e ta tsarabar da suka yo ta kalli gwaggo tace "don Allah gwaggo kina da bak'ar leda yar babba?" tambayarta tayi mi zata yi da ita tace "zan d'ibar ma Hajiya tsaraba ne" gwaggon tace "to ki bari da safe ba sai akai mata ba ko",
"To ai tsarabar Ya Handsome zan kai mashi tana iya cewa ita ina tata shiyasa zan fara kai mata wannan goben sai akai mata sauran" jinjina kai gwaggo tayi alamar gamsuwa ta mik'e ta samo mata ledan ta bata dama tasan duk zumudin na son ganin Haisam ne, bayan ta zuba abubuwan da zata d'iban tace ma gwaggo sai ta dawo ganin tana niyyar fita ko kallabi babu ta mik'e ta d'aukko mata kallabin ta bata tace ta yafa akanta tunda babba ne daga haka ta fuce.