← Book details Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 137

Sashe 44

Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallonta haisam yai tayi ganin yadda take rawa daga zaune hankalinta a kwance,hakan yasashi cikin ranshi yin tunanin da suna da kayan kallon k'ilan da bata rinka fitowa tana yin rigima ba don zasu rinka dauke mata hankali,bayan wasu mintuna ya duba time a wayansa ukku saura kwata,hakan yasa ya mik'e ba tare da ya d'auki wayarshi ba ya nufi Bedroom dinsa,juyowa fatuu tayi ta bi shi da ido tana kallon yadda yake yin tafiyan a hankali har ya shige cikin corridor d'in sannan ta juya kan tv taci gaba da kallo.

Almost 40 minutes ya d'auka kafin ya fito,k'amshin turaren jikinshi ne ya bugamma fatuu hanci hakan yasa ta d'ago da sauri ta kalli bakin corridor din,baki bude take kallon haisam da ya fito cikin jeans bak'i da t-shirt fara ta mashi cif a jiki,k'irarsa ta kakkarfa ta bayyana,a gaban rigar anyi babban rubutu bak'i ansa XL,gashinshi a nad'e yasha gyara sai salki yake,ganin ta k'ura masa idanu yasa ya kauda nasa idon dama shi baison kallo,nufo inda fatuu take zaune yayi daga gefenta ya aje mata abubuwan da ya ruk'o a hannunsa kafin ya juya ya nufi inda desk yake,laptop d'in dake asamanshi ya d'aukko ya dawo cikin falon,inda ya tashi ya koma ya zauna ya jawo c-table ya d'aura computer d'in,budeta yayi ya fara kokarin kunnata,

K'ura ma abubuwan da ya aje mata ido tayi wanda Milk pop corn ne anyi sealing dinsa a leda da k'aton biscuit sai wasu manyan chocolate guda biyar wanda ko ledar da aka nade su abun kallo ce,cike da mamaki ta juya ta kalli haisam wanda keta operating laptop d'in gabanshi,
"Yaya Handsome" fatuu ta kira sunanshi,ba tare da ya kalleta ba ya d'age gira"yess"ya amsa, ta ci gaba"wannan abubuwan da aka ajiye a gabana fa,mi za'ai dasu?" still bai kalleta ba yace"kallonsu zaki yi" tace toh,

bayan wasu yan mintuna ya yi mata kallon k'asan ido yaga ko ta fara ci,don yaga jiya da yayi mata gatse ta gane har tace irin abun gwaggo,aikuwa cike da mamaki ya idasa d'ago kanshi yana kallon ikon Allah,ashe bata ma d'auki komae ba, yadda yace matan tayi,wato k'ura masu ido sai kallonsu take tana hadiye miyau,Murmushi Haisam yayi ya d'an girgiza kai"Zarah" ya kirata, juyowa tayi ta kalleshi ta gwalo ido,gently yace"u can eat" fuskarta d'auke da mamaki ta juya ta kalli abubuwan kafin ta sake juyowa ta kalli haisam "yanzu duka wannan ni ka ba in ci?" kai kawae ya d'aga mata,
d,aukar Pop corn din tayi ta fara kokarin budewa dama duk shi yafi tafiya da ita saboda madarar da ke cikinsa,

"Wllh Yaya handsome kai mutumin kirki ne,yanzu duk abunda nayi maka kuma ka bani wannan kayan dadin,harfa ciwo naja maka"

"Gashi ma kinzo ko abun ciwo baki kawo man ba" haisam dake ta latsa computer ya fad'a,
"To ai mu fa bamu da irin wad'annan kayan dadin wllh,ko Kawu Amadu bai saida su,to ko inje in zubo maka abinci"?
Girgiza mata kai yayi alamar a'a,tace"shinkafa ce fa"sosae ta bashi dariya amman sai ya basar,ya lura tana son shinkafa don ko jiya ta ambace ta,
"Ko baka cin shinkafa ne?"ta tambaya,
"Ina ci,amman yanzu na koshi ne" gyad'a kai tayi daga haka ta fara tura Pop corn din a baki,wani kalan dadi ne ya ratsa cikin bakinta,lokaci guda ta fara k'okarin gyara zamanta gaba daya ta d'aura kafafunta asaman kujeran ta lankwashe su tayi zaman cin tuwo,mutsu mutsun da take yi ne yasa ya d'an yi mata kallon k'asan ido dai dai ta juyo da alama magana zatayi suna had'a idanu tace"don kar na 6ata maka k'asan parlon yasa nayi haka" jinjina kai yayi kawae.

"Wllh yan gayu sun ji dadinsu,Allah muma kasa mu a Aljanna muci kayan dad'i tunda nan mu ba masu kudi bane balle muci,komai na masu kudi na daban ne" tana maganar tana taunar Pop corn d'in har wani lumshe ido take da alama santi takeyi,haisam na jin duk abunda take fad'a bai dae tanka mata ba,
can ta juyo ta kalleshi"Amman dae Yaya handsome wannan guggurun na kasar yan turanci ne ko?" ya fahimci tana nufin yan kasan waje,girgiza mata kae yayi"na yan kasan hausa ne" ya bata amsa,
"To a ina ake yin shi Abuja ko lagos",

" ki duba jikin takardar ciki" da sauri ta ciro yar takardar tana dubawa,cike da mamaki tace"kai wai anan garinma ake yinshi,tabb lalle amman mu an raina mana wayo,kasan wanda ake kawo mana makaranta wllh duk tsakuyoyi gashi ba madara kuma duhu gare shi duk ya k'one,kasan mi?" girgiza mata kai yayi alamar a'a,
"Shi fa ko sugar babu sosae kuma da gishiri suke had'awa da sugan kana ci kana cin gishiri,kawae dai mu don anga talakawa ne ake mana irinshi mugaye kawae" daga haka ta ci gaba da taunar Pop corn d'in tana jujjuya kai,

"Ba kina zuwa Islamic school ba?"haisam da ya d'ago yana kallonta ya tambaya,
"Eh amman lokaci bai yi ba sai an kira sallah,sai inje in shirya" nodding kai yayi,sai kuma yace"dama kenan baki wanka",
Cakk ta tsaya da taunar pop corn d'in ta juyo baki cunkushe"wllh ina yin wanka,duk yanmatan unguwan nan nafi so yin gayu" jinjina kae kawae yayi da d'an murmushi ya maida kan aranshi yana fad'in wai duk yanmatan unguwannan ko ina abun yake,

K'okarin mikewa tayi ta kwashe su biskit d'in ta rungume ta nufi hanyar fita tana fad'in"bari inje inyi wankan to kafin a kira sallan" d'aga mata kae yayi ba tare da ya kalleta ba,ita kam tana nufar kopar fita amman idonta na akanshi ba k'aramin kyau yayi mata ba,yadda ya duk'ar da kanshi sumar kanshi mai matukar kyau da tsawo ga daukar ido a nad'e,ga ta gefen fuskan a kwance luf haka hannunshi da yake latsa computer dashi duk suma liya liya a kwance,
tana kaiwa bakin kopan ta tsaya"Yaya handsome"ta kira sunanshi,sai lokacin ya d'ago ya kalleta had'i da dage gira alamar amsa kiran nata,fuskarta d'auke da murmushi tace"thank u so much da abubuwan da ka bani"d'an murmushi yayi ya jinjina kanshi,daga haka ta juya ta kama handle d'in kopan ta bude,sake juyowa tayi ta k'ara kiran sunanshi,kallonta yayi "What" runtse idanunta tayi tace"A wodi masha Allah" tana fad'in hakan ta juya da gudu ta fita,shiru yayi yana tunanin ko mi take nufi da abunda ta fad'a don ya fahimci fullanci ne tayi,koma dae miye yasan ba rashin kunya tayi ba don ta had'a da masha Allah,dan ta6e baki yayi yana k'okarin juyawa aka turo kopan,itace ta lek'o da kanta tanata dariya duk dimples dinta sun lotsa sosae"yaya handsome kasan mi nace?" d'an girgiza mata kai yayi alamar a'a,
"Cewa nayi kana da kyau masha Allah" rasa abunda zaice mata yayi kawae yaci gaba da kallonta,hakan yasa ta kyalkyace da dariya ta janye kanta ta turo mashi kopan,haisam dake kallon side d'in kopar d'an murmushi hadi da girgiza kai yayi daga haka ya juya ya ci gaba da abunda yake.

Sai da ta koma gidan sannan ta tuna da gwaggo tace ta share kitchen da tsakar gidan,da sauri shaf shaf ta share su kafin ta zuba ruwa ta shige band'aki don yin wanka,bayan ta fito tasa Uniform tayi sallah sai lokacin ta dan zubo abinci ta ci kafin ta d'auki jakarta ta fito don tafiya islamiyya lokacin kusan karfe hudu da rabi.

Da sauri take tafiya bayan ta fito ta hau hanya tana gab da shan kwanar gidan hajiya taji an kwala mata kira"Fatuu" da sauri ta juyo ganin haulat ce yasa ta tsaya har ta k'araso wurinta"ya akai kika makara yau keda baki makara?"haulat ta tambayeta,
"Gwaggo tasa in yi mata wani aiki" fatuu ta bata amsa bayan sunci gaba da tafiya,jinjina kai haulat tayi kafin tace"in muka dawo sai muje in raka kin abashi hakurin" kallonta fatuu tayi ta d'age gira"wa kenan"ta tambaya cike da rainin wayo,

"D'an gidan Hajiya mana da kika fasa ma glass ko" wata yar iskar dariya tayi tace"sai dae ko ni in rakaki ki bashi hakurin"da sauri Haulat ta kalleta" yo ni hakurin mi zan bashi kamar dae ni na fasa masa glass din...." fatuu ta katseta"to wadda ta fasan taje ta bashi hakuri kuma ya hakura" zaro ido haulat tayi cike da zumudi tace"don Allah da gaske kinje fatuu,kuma ya hakuran?"
"Bari kiga dil" fatuu ta fad'a tana kokarin bud'e cikin jakarta,biscuit da chocolate din da haisam ya bata ta fiddo harda ledan d'an sauran Pop corn da bata k'arasa cinyewa ba,ta mik'a ma haulat,

Cike da mamaki baki bude haulat ta kar6a"wai don Allah da gaske kike shi ya baki wadannan abubuwan?" fatuu tace"eh mana shi ya bani,kuma yace ya hakuri amman fa sai da yasa nayi masa alkawarin na daina rashin ji ko fad'a yace kar ya sake ganina ina yi"ta k'arasa tana yar dariya,
cike da farinciki haulat tace"kai amman wllh naji dadi da ya hakura,daman nayi tunanin zai hakuran don ni banma yarda da maganganun gaye ba,amma fa nayi mamakin saukin kanshi keda kika yi masa laifi wai kuma har ya baki wadannan kayan dadin",

"kinsan ni d'in jinin sa'a ce" fatuu ta fad'a tana murmura idanu ",
"Ah lallai ni ce sheda,jinin sa'a mai kukan za'a kaita gidan yari ta rink'a cin gabza kwarkwata ta gwaigwaye mata kai ba,yar rainin wayo zaki wani gaya man jinin sa'a bayan kin gama 6are ma mutane baki"haulat ta fad'a tana dariya itama fatun dariyar take,ta bude chocolate guda ta tura baki,kallon haulat tayi "ke ba zaki sha ba",
Chapter 44 · 0% Book details