← Book details Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 137

Sashe 84

Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washe gari Friday bayan ya ajesu a Makaranta ya bata wata envelope yace in ta kaima malamin nasu littattafan ta bashi, lokacin da ta kaima Auncle Bash sak'on Haisam d'in da mamaki ya bude, kudi ne ya gani a ciki yan dubu duba har saida gabanshi ya fad'i, kallon fatuu yayi ya tambayeta ta tabbatar shi akace taba tace mashi eh, sosae ya jinjina abun kafin yace in tasan lambar wayarshi ta bashi tace batasani ba, ba haka yaso ba eson gobe ba makaranta balle yayi mashi godiya, mik'a mashi littattafan da aka siyo Fatuu tayi ya amsa yace sai zuwa Monday za'a fara mata amfani dasu amman duk da haka saida ya bata wani English Grammar ya nuna mata inda yake so ta duba cikin weekend, kamar yadda Haisam yace mata tayi da abubuwan da ya siya mata da yawa hakan tayi, ta babba wasu wanda basu dashi harda ma wad'anda suna dasu ta k'ara masu hakan ba k'aramin mutunci da girma ya siya mata ba, Haulat ma ta d'ibar mata duk abubuwan dasu Calculator d'in da yace ta bata sosae tai farinciki tanata gode masu su duka har Fatuu nace mata ai itace silar komae da ta bata shawarar zuwa bashi hakuri, ita dai Haulat d'in d'an Murmushi kawai tayi tace dama Allah ya rubuta hakan.

A cikin wani satin daya kama Haisam ya siya ma Tk sabon mashin d'in daya tura mashi sakon yana so kaman yadda sukai dashi duk da dak'yar yayi k'arfin hali ya tura mashi Message d'in don bukatar tashi yana ganin babba ce don mashin din yayi wurin dubu dari biyar, sosae Tk yay farinciki har ya kasa 6oyewa ba kamar da ya kasance shima zai biya ma kaninshi bukatarshi na mashin d'inshi da yaketa so ya bashi, sam Haisam bai bashi damar yi mashi wata doguwar godiya ba, bai 6oye ma Hajiya komae ba yay mata bayanin yadda akai Haisam ya siya mashi mashin din, batace komai ba sai murna ma da ta tayashi don tasan halin tk yana da kawaici kan abu irin hakan sam baida zari, tambayarshi ma tayi yadda zai aika ma kaninshi da nashin yace mata akwae wasu yan garinsu dake zuwa cin kasuwa nan to da babbar mota mai bud'addan baya suke zuwa su zai ba su kai mashi tace hakan yayi.

A cikin satin kuma aka sako su Gaye bayan anyi tsatstsauran rubutun cewa za'a saka masu idanu in aka k'ara kama kowannansu ya aikata ko k'ara yunkurin aikata laifi makamancin wannan to za'a tado wannan ahad'a ayi masa hukunci, daka kallesu zaka fahimci sunji jiki ba laifi duk sun k'ara yin bak'i sun jeme ga wata uwar rama (ba tuwon gyatuma), gaye har wasu kuraje suka fito mashi banda uban cizon sauron dake kan fatarshi, A daren ranar da aka sakosu mahaifinsa Malam tanimu ya tasa shi gaba suka je gidan Hajiya don yi mata godiya, sosae ya shiga yi mata godiya hajiya tace ba wani abu ai d'a na kowa ne, yace in ba damuwa yana son ganin Haisam, Hajiyar na niyyar kiransa awaya sai gashi ya shigo cikin parlon don lokacin ba'a dad'e da gama sallar isha ba, sosae malam tanimu yayi mashi godiya shima had'i da sama rayuwarshi da iyayenshi Albarka, yayi masa Addu'oi sosae kafin yace ma Gaye dake ta faman sussunar da kai tunda Haisam d'in ya shigo yayi mashi godiya, kallonshi ya d'anyi cike da jin kunya yay mashi godiya, sai lokacin ya bud'e baki yay Magana dama shi baison ayi tayi mashi godiya shiyasa koda Malam tanimu nayi saidae ya jinjina mashi kai in kuma Addu'a ce can kasan makoshi yake amsawa da Amin, yar nasiha yayi ma gaye ya nuna mashi yana da damar da zai gyara rayuwarshi a yanzu tun kafin lokaci ya k'ure mashi don a rayuwa komae yana da limit idan lokaci ya k'ure mashi koda ya gyara hakan bazai amfaneshi da komae ba, bayan ya gama ya kalli Mahaifinshi yace idan ya gyara halinshi ya natsu zai d'auki nauyin karatunshi in yana son yi, in kuma kasuwanci yake so to zai bashi isasshen jari, sosae Malam tanimu yaji dadin wannan Maganar don harda yar kwalla yayi ya kalli gaye yace mashi yaji dai da kunnanshi wannan dama ce agare shi, bayan ya gama yi mashi magana Hajiya ta tambayeshi yanzu Jos d'in zai kaishi yace ehh, duk da Ashirun yace mashi wai ya bari amman yasan in ya kyaleshi ruwa zai koma saboda gurbatattun abokai don haka gobe in Allah ya kaimu zasu tafi zuwa wani lokaci in yaga ya gyara halin da gaske sai ya maido shi nan, Hajiya tace hakan yayi, da zasu tafi ta basu kud'i masu yawa tace su sha ruwa a hanya Allah ya kiyaye bayan itama tayi ma gayen nasiha, Bawan Allah harda yar kwallarshi yace in sha Allahu zai yi amfani da nasihar da suka mashi zai dage don ganin ya gyara rayuwarshi daga haka suka yi masu sallama suka tafi,

(Allah sarki Gaye inayi maka fatan Alkhairi, Allah ya baka ikon gyara rayuwarka ya shiryi duk masu irin halinka ya shirya Al'ummar Annabi(SAw) gaba d'aya Amin, nasan masu karatu ma nayi maka fatan Alkhairi don ka taka muhimmiyar rawa a labarinnan muna godiya)

Kwanaki sun shud'e sun bada satittika haka suma sun shud'e sun bada wasu yan watanni har gashi yau Asabar saura sati biyu cub a fara azumin watan Ramadan, da yammacin ranar Misalin k'arfe shidda saura Tk ya parker hilux ta wurin aikinsu Hajiya a kopar gidansu Fatuu, fitowa yayi ya zagayo d'ayan 6arin ya tsaya yana yin yar mik'a, kallon Amadu dake cikin shago yana ta faman binshi da ido tunda ya tsaya yay yace "ka fito ka d'auki Amaryarka" cikin rashin fahimtar zancenshi Amadun yace "Amarya kuma,wace amarya" da alamun mamaki akan fuskarshi yay Maganar, Tk yace ya fito mana ya gani, lokacin daya fito yaje bayan motar turuss yay yana kallon katon kwalin da ke nuni da freezer ce acikinshi, cikin rashin fahimta ya kalli Tk daketa murmushi tun kafin yace wani abu ya rigashi cewa tashi ce Yaya Haisam yace ya kawo mashi, zaro ido Amadu yayi a rude ya maimaita tashi ce! Tk ya bashi amsa da eh kafin yace yazo su sauke, da taimakon wasu mutane aka sauke freezer d'in suka nufi cikin gida da ita, Gwaggo na zaune asaman tabarma a inda ta saba zama in ba wuta taji anata kiciniyar shigo da abu, sakin baki tayi tanata kallon ikon Allah har suka samu shigowa da ita suka nufo cikin gidan a gaban gwaggon suka ajeta, tun kafin tayi magana Amadu dake ta faman washe baki yayi mata bayani, abun bana zama ne, mik'ewa tayi ba shiri tana kallon kwalin freezer d'in cike da mamaki, maida idonta tayi kan Tk dake tsaye gefe tace ya tabbatar nan akace ya kawo, tambayar tata har saida ta bashi dariya kafin yace mata eh, ita mamakinta yadda yasan da Maganar zata siya freezer d'in har ya aiko, wanda yau bai wuce saura yan kwanaki bama ta siyo ma Amadun ba donma kud'in sun samu gi6i ba da tuni ta siya mashi, suna cikin tsayuwar Fatuu ta rafko sallama ta shigo jikinta sanye da uniform d'in islamiyya, baki bud'e tabi kwalin itama da kallo cike da mamaki ta furta "kai,wai Gwaggo harkin siyo ma kawu Amadu freezer d'in?"
Wannan Maganar yasa gwaggon tunanin ko ita tayi ma Haisam zancen hakan yasa ta tambayeta ko tayi mashi zancen siyan freezer d'in, da farko cewa tayi ita batayi mashi Maganar ba gwaggon tace ta dai tuna, don ita abun yasata al'ajabi indae ba wani ya gaya mashi ba taya zai sani tunda gashi ance Amadu aka siya mawa, can Fatun tace ta tuna lokacin da Uncle Bash yayi mashi maganar littattafan nan daya ta6a siya mata, to lokacin ne ta gaya mashi gwaggo ma tace zata siya littattafan amman bata da kud'i sai ta kwashi kudin adashen da take wanda zata saima kawu freezer, jin hakan yasa gwaggo sauke nannauyar ajiyar zuciya tama kasa cewa komai don Al'amarin Haisam akwae d'aure kai, ko acikin mutane masu yin Alkhairi shi na dabanne, tambayar Tk tayi ko Haisam d'in na gida yace mata a'a yana can wurin exercise shima kiranshi yay awaya yace ya d'aukko mota ya iskeshi a wurin, jinjina kai gwaggo tayi kawae tk d'in yayi mata sallama zai tafi ta shiga yi mashi godiya harda cewa don Allah ya tsaya abashi tukuici, wata yar iskar dariya yayi yace "haba dae Kakus" dayake shima d'an barkwanci ne, bayan ya tafi tsaye sukai su duka farinciki duk ya cikasu sai fara'a suke Fatuu kam harda rawa tayi,

Da daddare bayan sallar isha suka d'unguma zuwa yin godiya lokacin Haisam na a part d'insa hakan yasa suka je can, karo na farko kenan Gwaggo da Amadu suka shiga sashen nashi, ba k'aramin burgesu wurin yayi ba suna ta yabawa acikin ransu, lokacin da suka shiga falon bai ciki yana can cikin bedroom d'inshi saida kawu Amadu ya kirashi a waya ya sanar dashi zuwansu sannan ya fito, fuskarshi a sake ya gaida gwaggo shikuma Amadu ya gaida shi ya amsa, wuri ya nuna masu yace su zauna kowa ya zauna saman armchair d'aya, bayan sun zaunan gwaggo ta fara mashi godiya tana cewa anga abun arziki angode Allah ya saka da mafificin Alkhairi ya albarkaci rayuwa yasa agama da duniya lafiya, sosae take mashi godiya had'i da Addu'a har saida sautin muryarta ya d'an karye kaman zatayi kuka, shidae abu d'aya yace shine ba wani abu, sai kuma Addu'ar daya rink'a amsawa jefi jefi, tana tsagaitawa kawu Amadu ma ya shiga yin godiya, kallon Fatuu yay data zauna akan carpet gefenshi yay mata alama da kanshi nan take ta gane abunda yake nufi don yanzu da yayi mata alama da kai ko da ido take ganewa, mik'ewa tayi ta kalleshi k'asa k'asa tace "Lemu ko ruwa?" wani kallo yayi mata kafin ya k'ara mata alama da kai ta juya ta nufi Fridge d'in, lemu da ruwa ta d'aukko ta kawo ma gwaggo kafin ta juya ta kalleshi ya lumshe idanunshi hakan yasa ta juya ta k'ara d'aukko wasu ta kawo ma kawo Amadu,
Chapter 84 · 0% Book details