← Book details Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 96 OF 137

Sashe 96

Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Girgiza kai Zee tayi ta maidashi kafin tace to ta za6i wani, tambayarta tayi wanda basu kaishi kud'i ba ta nuna mata gabansu, wani Golden yellow mai sak'a Coffee brown ta nuna shima yay kyau sosae amman tun kafin aciro ta tambayi nawa yake, saida Zee ta d'anyi jimm kafin tace dubu 42, shima sai cewa tai yay kudi a nuna wadanda basu kaishi ba Zee ta nuna mata, wani blue mai kwalliya golden brown ta nuna tana washe baki alamar yayi mata don dama tana son blue har saida Zee ta sauke yar ajiyar zuciya don duk atunaninta shi zata d'auka amman koda ta ciro mata taga kudinshi dubu 34 sai tace shima bata so yayi tsada, lallashinta ta fara yi tace ta daukeshi kawae tunda tana sonshi kuma shi ai baiyi kudi sosae ba tunda kudinshi ma rabin na farkonne amman ta kafe akan yayi tsada shima, jagub zee tayi tana kallonta tana ta tura mata baki can ta tambayeta kaman na nawa take so ne tace kaman na dubu goma irin wanda gwaggonta ta siya mata waccan sallar, jinjina kai tayi tace to bata da irinshi gaskiya don ita laces d'inta masu kananun kudi duk sun kai 20k, tana jin hakan ta juya tana fad'in "bari in ma Ya Handsome Magana babu wanda nike so sai mu tafi wani wuri",
Zee na jin tana niyyar yi mata asarar ciniki ta d'aga murya tana fad'in ya zatace ba wanda take so bacin duk gasu nan ta nuna, aikuwa tana yin Maganar sai a kunnan Haisam d'in dama hakan take so, tsam ya mik'e ya nufo su ya tambayi abunda ya faru Zee tayi mashi bayani, wani kallo yay ma Fatuu data tamke fuska, kallon Zee yay ya tambayi wanne ta nuna da farko aikuwa tana jin hakan tasa mashi kuka tana fad'in "Ni wllh bazansa wannan leshin ba don Almubazzaranci ne an fad'a mana a islamiyya, kudinshi fa sun kai na d'an shanu kuma ko gwaggo taji kudinshi wllh sai tayi fad'a, nidae banson shi don Allah Ya Handsome kar ka siya man shi" still sukai suna kallonta har fuskarta tayi sharkaf da hawaye gaba daya gyalenta ya zamo tana goge fuskarta yayinda Zee ke fad'in Masha Allah acikin zuciyarta ganin gashin kan Fatun, Sigh Haisam yay yasan halinta sarae tunda ta nuna bata so to fa yasan bata so d'in, umarnin suje su zauna ya basu ya fara duba kayan da kanshi, lace d'in data nuna tana so blue d'an dubu 34 shima shi ya d'aukko, sai atampa Chiganvy Gold mai shegen kyau, kiran Zee yay ta taso ya nuna mata kayan yace suje ta samo mata takalmi da veil da duk abunda yakamata kar ta k'ara tambayarta ta amsa mashi da toh, umarnin biyota taba Fatuu suka shiga kopar nan da wadda ta kira da Esther ta fito, suna shiga nan ma Fatuu sakin baki tayi tana kallo wurin don wani katon shagonne shake da takalma, jakuna, gyaluluwa, sarka da yan kunnaye, Undies Cosmetics harda English wears, akwae babbar kopar glass ta shigowa daga waje banda ta cikin d'ayan shagon, takalma golden da gyale guda biyu da jaka daya da zasu shiga da kayan ta d'aukko mata ta bata takalmin ta gwada wanda mai tsini ne amman heel d'in nada kauri kuma takalmin nada mad'auri, Jama'a kuzo kuga Fatuu cikin takalman sun mugun yi mata kyau ita kanta sai Murna take sai kace ba wadda ta gama kuka ba dama kuma tana son takalmi mai tsini amman gwaggo bata so shiyasa bata siya mata su sai mai tudu, sam bata ma tambayi su nawa suke ba saboda d'oki, sark'a da yan kunne da yan hannu gold plated ta daukko mata sai agogo, juyowa tayi don ta tambayeta ko akwae abunda take so kuma sai taga ta k'ura ido tanata kallon d'an mutum mutumin da aka sanya ma wasu had'addun wando jeans da riga sai kyalli suke ,

"Ko kina son su?" Zee ta tambayeta, maido idonta tai akanta tace "inaso amman fa ni ina jin tausayinshi ne banson sashi kashe kudi sosae saboda sai yayi wahala yake samunsu" ta k'arasa a marairaice, jinjina kai Zee tay da mamaki tace "ke waye ya fad'a maki sai yayi wahala yake samun kudi?"
"Eh mana, ai ya fad'i man shi engineer ne rannan dana tambayeshi kuma yace man a filin jirgi yake aiki kinga kenan suke gyara jirgi in ya lalace in ma yak'i tashi su suke tura shi har ya tashi",
bud'a ido Zee tayi sosae alamar mamaki sai kuma tasa Dariya tace "Yaushe H,zakee ya zama injiniyan jirgi kuma?" wuri wuri tayi da ido sai kuma tace "ko bashi bane?",
girgiza mata kai tayi "yea bashi bane, shi Kwararran Computer engineer ne, he knows both the hardware and software da duk abunda ya danganci computer dae sosae, kuma yana samun kud'i sosae don yanzu we're in a Digital world so kullum cikin samun kud'i yake gashi Dad nashi ma mai kud'i ne sosae ke baki san Babanshi bane, ba yar'uwarsu bace?" da sauri Fatuu ta girgiza mata kai "a'a ni ba yar'uwarsu bace bafa makwabciyarsu ce",

" No wonder dat's why kike cewa kina jin tausayinshi, to bari kiji in zai siye maki kayan shagonnan duka ba abunda zaiji kuma dukiyarshi bazatai ko gezau ba, a Abuja fa baki ga tangamemen gidansu ba gari guda in kika shiga zaki manta kina a Nigeria ne kuma bashi ne kadai gidansu ba don ko anan garin a GRA suna da wani katon gidan hadadden gaske..."

"Ke kin ta6a zuwa gidansun ne?" Fatuu da tayi kasak'e tana sauraronta ta tambaya,
" Yea sosae, don nasan yan gidansu suna siyan kaya awurina kuma wani lokacin ni ke kai masu in naje Abujar, yanzu haka akwae Sisters dinshi a Whatsapp group dina kuma suna fallowing handle ena na instagram da sunga kaya suna so zasu siya ne, akwae ma Stepmom dinshi da suke ce ma Aunty ita bata dad'e da auran dad dinshi ba, ita dama to tun kafin ta auri Senator d'in nasanta don yar Daura ce yar'uwarsu ce itama sosae take siyan kayana kuma wasu kyauta kawae take dasu, so su haka suke, yin babban Alheri ba wani abu bane a wurinsu, in ke kin k'i suna yi ma dubban Mutane gara ma kiyi amfani da damanki ki d'auki duk abunda ranki ke so" sauke ajiyar zuciya Fatuu tayi tace to ta bata kayan, juyawa zee tayi tana d'an girgiza kai ganin yadda tasata uban bayani kafin ta amince, wasu riga da skirt na jeans masu kyau ta daukko mata, rigar fara ce tana da ta sama kalar skirt d'in ta nuna mata wata kopa tace ta shiga change room ne ta sanya sai aga in sunyi mata, ba wani 6ata lokaci ta sanyo kayan don dama doguwar riga ce ajikinta,sosae kayan sukai mata kyau kuma sunyi mata daidai dama skirt din irin wanda bai kaiwa can k'asa ne, wasu riga da wando ta sake daukko mata har sunfi na jikin mutum mutumin kyau tace ta gwado su suma, cike da zumudi ta amshi kayan ta nufi dakin, suma bata dau wani dogon lokaci ba wurin sa su, lokacin data fito cikin jeans da shirt d'in har saida Zee ta furta Tubarkallah a fili ba tare da shiri ba don ba k'aramin amsar jikinta kayan sukai ba, babban abunda yaba Zee mamaki shine ganin yadda k'ugun Fatun ya fito sosae cikin wandon duk da kananun shekarunta amman hips ne da ita sosae, da alama dae Maganar gwaggo ta tabbata da tace da alama irin jikin mahaifiyarta gareta,

Cike da Murna Fatuu ta nufi hanyar fita d'ayan shagon tana fad'in bari ta nuno ma Ya Handsome ba tare data jira mi Zee zata ce ba ta fice saidae tabi bayanta, tunda ta fita ta kwala mashi kira ya d'ago daga kan wayar da yake latsawa ya kalleta, tana ta washe baki ta nuna mashi kayan jikintan da hannu, bud'a ido yay ya d'age gira alamar mamaki,
"Nayi kyau ko?" ta tambaya cike da zumud'i, jinjina mata kai yay alamar eh ai sai ta fara d'an tsalle gashinta dake zube a bayanta yana d'an watsowa har ta gefen fuskarta ita dae Zee na atsaye gefe tanata Murmushi, can tace mata tazo suje su ko sa gama don an bar Haisam d'in nata zaman jira, bin ta Fatuu tayi suka koma ciki suna shiga taci gaba da Murna tana ta ta6a jikinta,

" I think u also need dis" Zee ta fad'a yayin da takai hannu ta ciro wata yar k'aramar bireziya ta mik'o ma Fatuu, ai koda idanunta sukai arba da ita da sauri kamar wadda shock ya ja ta matsa baya tana zare ido,
"Kina bukatarta itama" Zee ta fad'a, da sauri ta girgiza mata kai "a'a ni bani sa ta, kawae so kike ace man yar iska",
yar dariya tayi "to mu da muke sawa duk yan iska ne kenan?" turo baki tay "ai ku abunku manya manya ne"
"To ai muma da kaman nakin ya fara mana kuma tun lokacin ake fara wearing nata",

" to ai dana isa sawa gwaggota zata siya man ne",
"Inaga ita gwaggon naki bata san yakamata ki fara sawa bane tunda baki sa irin wannan dress din ba agabanta, look at ur nipples yadda suke showing fa, haka kika je gaban Ya Handsome din naki da naji kina fad'a har kina tsalle" shiru tayi tana ta turo baki ita ala dole bata son sa bra d'in hakan yasa Zee ta kama hannunta ta kaita gaban katon mirror dake a shagon,
"Look at ur chest very well, ko da breasts d'in basu da girma kiga yadda nipples dinki suka bayyana sosae" tayi Maganar tana nuna mata abunda take magana akai ta cikin Mirror d'in, aikuwa da sauri tasa hannu guda ta rufe bakinta alamar al'ajabi d'ayan hannun kuma ta kare kirjinta dashi alamar kunya,
Chapter 96 · 0% Book details