← Book details Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 137

Sashe 80

Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

" Ki fad'i mata exactly as u said,in kikai man karya....." kafin ya ida maganar ta katseshi ta idasa mashi ".....in kika man k'arya ina zaune zan gani" tayi Maganar tana kwaikwayon yadda yake Magana harda wani d'age gira daga haka ta fuce da gudu Haisam bai san lokacin da kyalkyace da dariyar da bai tunanin ma ya ta6a yinta, arayuwarshi ba mai mashi irin abunda Fatuu ke mashi haka kuma bai ta6a sake ma wani mutum 6are kaman yadda yake mata ba ko k'annenshi bai sake masu kaman yadda yake ma Fatuu ayanzu,wato ashe ta ruke Maganar da yayi mata lokacin da tazo bashi hakuri ta dau alkawarin ta daina fada da kowa yace inma tayi yana zaune zai gani kar tayi tunanin zata mashi wayo,girgiza kai yayi a fili ya furta"ZARAH".

Tana komawa gida cike da farinciki ta sanarma gwaggo kaman yadda tace zata fad'i matan sai dai da farko nunawa tayi bata yarda ta bishi ba kawai salon taje ta takura mashi,magiya ta shiga yi mata tana rantsuwar bazata takura shi ba,da kyar gwaggon ta amince bayan taja kunnanta sosae,cike da zumud'i ta nufi bandaki don yin wanka tana cikin yi aka fara kiran sallar la'asar da sauri ta gama ta fito tayi walwala kafin ta nufi dakinta ta fiddo sabuwar maroon jallabiyarta mai ratsin brown ta zumbula bayan tasa undies sannan ta duddungura sallar shaf shaf tana gamawa ko addu'a bata yi ba ta mik'e ta nufi gaban mirror ta fara yin kwalliya dama ta jere kayan shafan da Haisam ya siya mata,kwalliya tayi simple ba mai hayaniya ba ga powder din ta kwanta mata sosae tayi wani fayau,dama yanzu fatarta ta k'ara yin smooth saboda mayukan da take amfani dasu,ta shafa maroon janbaki wow,jama'a kuzo kuga Fatuu yanmata,fita tayi taje wurin gwaggo tace ta bata takalmanta na sallar bara dama ita ta 6oye su don Fatuu in tana son abu bata san ta kyaleshi ya huta ba yanzu ya tsufa,ba don gwaggon na adanawa ba shima takalmin da tuni ya tsufa koma ya lalace,d'aukko mata tayi da yar jakarshi bak'a shima bak'i ne mai tudu nan da nan ta idasa fitowa a yar budurwa,sark'a da yan kunne harda d'an agogo golden gwaggo ta fiddo mata harma ta tayata sakawa,tana niyyar juyawa ta fita gwaggo tace"wannan kitson na gaba ki maida shi baya ki hade ki kulle kar ki fita haka dashi",amsa mata tayi da toh daga haka ta koma dakinta tayi yadda gwaggon tace ta feshe jikinta da turare harda bakinta ta fesa mouth freshner dama tayi brush da ta shiga wanka,tsayawa tayi tana kallon kanta a madubi,kayataccen Murmushi tayi a fili tace"Fatuu kinyi kyau kaman sarauniya" tuntsirewa tayi da dariya daga haka ta fita daga d'akin ta d'aga murya tana fad'in "Gwaggo sai na dawo" lek'owa gwaggon tayi tana kallon bayanta har ta fita bayan tace mata adawo lafiya,d'an girgiza kai tayi ganin yadda Fatunta ta fara zama Budurwa.

Tana niyyar shiga part d'inshi ya 6ullo daga corridor d'in da zai kai ka cikin harabar gidan,tana ganinshi ta tsaya,suna had'a ido ya d'an buda mata ido alamar mamaki hakan yasa tasa tafukan hannayenta ta rufe fuska alamar kunya,
"Nayi kyau?" ta tambayeshi bayan ta bud'e fuskar,kai ya d'aga mata alamar eh kafin yace taje parking space ta jira shi,amsa mashi tayi da toh tabi ta gefenshi ta shige cikin gidan shi kuma ya ida shigewa part din nashi,tana shiga ta nufi part d'in hajiya don ta gaidata Saude ta sanar da ita Hajiyar bata nan bayan ta gama yabon gayun nata hakan yasa ta juya ta fita,tana isa wurin aje motocin Haisam ya fito ya nufo parking space d'in yana sanye da Sportswear ya ratayo jakarshi a hannu guda,k'ura mashi ido Fatuu tayi tana kallonshi don shi komi yasa kyau yake k'arawa,ganin kallon da take mashin yasashi sadda kanshi k'asa har ya k'arasa cikin wurin,back door na mota ya bud'e ya saka jakar,yana k'okarin bud'e gaban motar Fatuu tace"Ya Handsome mu hau wanccan mashin din" juyawa yayi ya kalli bike d'in da take nunawa kafin ya juyo yana kallonta, imagining ya fara abunda zata iya yi mashi in ya hau bike d'in da ita hakan yasashi girgiza mata kai yace"zamu a Mota",turo baki tayi tana d'an yamutsa baki alamar ba haka taso ba,ganin hakan yasashi cewa"wani lokacin" ya jaddada mata da kanshi itama ta d'aga mashi alamar toh daga haka ya bud'e Motar ya shige yace mata ta zagaya ta shiga,bayan ta shiga ya fiddo motar cikin harabar daga haka yajata suka fuce.

*💖A SANADIN MAKWABTAKA💖*

_A heart touching story of Love and Destiny_ 💔

*Mallakin*
⬇️
*🌹ZAINAB LALUH*📲✍
_~(Oummu imam)~_

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

5️⃣3️⃣

Wani Babban Bookshop ya nufa dasu, a gefen wurin ya parker motar, da har zaice mata ta jirashi sai kuma yace ta fito sakamakon tunawa da Maganar data yi na cewa ita kifin rijiya ce duk bata san wurare ba, suna shiga ciki Fatuu tabi wurin da kallo don an tsarashi sosae gashi k'ato ne akwae duk wani abu da Mutum zai iya bukata a Bookshop, wani k'aton Alhaji ne zaune saman kujera acan ciki yana ba yaran shagon umarnin d'aukko ma Mutane abubuwa hannunshi ruke da calculator da littafi da alama lissafi yake, yana hango Haisam ya fara washe baki yana mashi dariya,
"Barka da zuwa yalla6ai" Alhajin ya fad'a lokacin da suka k'arasa,
"Yauwa Alhaji,ya kasuwa" ya fad'a cikin cool voice dinsa,
"Kasuwa Alhamdulillah gamu cikinta" Alhajin yayi maganar still da fara'a a fuskarsa, maida kallonshi yayi kan Fatuu data k'ura mashi ido tanata kallon tumbinshi cikin ranta kuwa tunani take wai ko dai ciki gareshi ne,
"Sannu yanmata"Alhajin yace mata, saidai sam hankalinta na kan tumbinshi har saida Haisam ya kira sunanta sannan ta maido idonta kanshi yay mata nuni da ana mata Magana, kallon Alhajin tayi dake mata Murmushin yake don ya fahimci abunda take kallo ya sake ce mata sannu sai lokacin ta gaidashi ya amsa mata, d'aura takardar yayi saman wurin dama ya fiddota daga cikin pocket d'in wandonsa yace ma Alhajin wannan yake so, da sauri ya kira wani matashin saurayi acikin yaran shagon yace ya mik'o masa takardar, bayan ya duba ya d'ago yace ma Haisam duk akwaesu nan take ya nuna ma saurayin inda zai d'add'auko su, bayan an fiddo mashi su duka Alhajin ya tambayi shikenan, Haisam yace a d'aukko mashi Calculator guda biyu da Math Sets, da sauri Fatuu ta kalleshi tace" Ya Handsome guda biyu biyu ai sunyi yawa kuma ma ina dasu don dai sun tsufa ne wasu abubuwan maths set d'in duk sun 6ace, amman dai guda d'aya ya isa" shiru yayi mata duk idanun mutane suka dawo kanta dama kuma tunda suka zo wurin tun a waje aketa faman kallonsu,(dama abu mai kyau badai jan hankali ba), jin baice mata komae ba yasa ta sake maimaita mashi cewa guda daya fa ya isa,

"Ba kinada Friend ba,ki bata" taji yace ba tare daya kalleta ba, shiru tayi sai yanzu ta gane ashe harda Haulat ya siya, da itama ance ta siyo littattafan harda ita zai saimawa kenan ta ayyana aranta, bayan an d'aukko su yace a bashi bandir d'in littafin rubutu,kwalin biro dana pencil da eraser da sharpener, wata zabura tayi ta zaro ido tana kallonshi shikam baima san tana yi ba, ganin duk an d'aukko mashi yasa a rud'e tace"Ya Handsome wannan ai sunyi yawa sosae duk ina zan kaisu?" banza ya mata ganin hakan yasata ta d'an buga k'afa tana jujjuya kai irin na shagwababbun yara hakan yasa Mutane yin Murmushi harda Alhajin yace "ai abun amfani bai yin yawa, in aka siya da yawa kinga zaki dade baki nema ba, ko baki son ayi mana ciniki ne" tura mashi baki tayi batace komae ba,

bayan duk an d'aukko komae aka zuba masu acikin katuwar leda mai tambarin shagon ya basu card suka cire kudinsu daga haka suka yi sallama da Alhajin har sun juya zasu tafi ya kira Fatuu ya bata kyautar jotter mai cover din frozen had'e da dan bironta in ana rubutu dashi da daddare yana sakin haske kala kala, fuska a tur6une tace ta gode ta nufi hanyar fita ita ala dole anyi mata laifi gashi ma Ya Handsome d'in yaki tanka mata hakan ya kara fusata ta,

Har suka hau hanya tana ta tura baki tana d'an satar kallonshi, duk yana kallonta ta cikin mirror can ya d'an juyo suka had'a ido tayi narai narai da idanu kaman zatai kuka,
Chapter 80 · 0% Book details