← Book details Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 137

Sashe 56

Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fitowa Saude tayi jikinta sanye da doguwar rigar shadda,ba karamin kyau tayi ba sai kace ba mai aiki ba,tsaf tsaf da ita tayi d'aurin kallabi mai kyau,tana karasowa Dining d'in tun kafin tayi magana hajiya tace"ki zuba ma fateema abinci"amsawa tayi da toh,ta kalli fatun"inyee wannan kyau haka fateema"Saude ta fad'a fusakarta da murmushi,itama fatun murmushin take,janyo katuwar Warmer d'in dake kan table din tayi ta bud'e,White rice ce tasha peas da green beans harda carrot gwanin ban sha'awa,Plate ta daukko ta zuba mata sai da ta tambayeta in ya isa Fatun ta ce eh,sannan ta rufe Warmer d'in ta bud'e ta biyu,jar miya ce taji uban nama kitif da ita ta zuba mata a saman shinkafar, sannan ta kuma janyo wata warmer d'in yar babba ta bude,farfesun kaza ne ciki sai uban k'amshi ke tashi,cikin wani d'an bowl ta zuba mata sannan ta rufe,nuna ma fatuu coleslow tayi"gashi nan kisa wanda zai ishe ki"fatuu ta amsa da toh,bayan ta gama zuba mata komae ta tsiyaya mata Ginger Drink a Cup daga haka tace"Aci lafiya"tana shirin juyawa Hajiya ta dakatar da ita"ki d'aukko ma haisam lemu wai ginger d'in tayi mashi yaji"kallon haisam din Saude tayi"Wanne iri za'a daukko?" batare daya d'ago ba ya bata amsa"Coke",amsawa tayi da toh,daga haka taje ta kawo masa,kallon hajiya tayi cikin girmamawa"akwae abunda za'ayi?"hannu ta d'aga mata alamar taje.

Sam fatuu ta kasa sakewa taci Abinci yadda ta saba ci,idonta na akan haisam tana kallon yadda yake tsakuran nashi,hakan yasa itama take ci a hankali,hajiya ta lura da bata sake ba kuma tasan saboda haisam d'inne don taga yadda take ta kallon abincin da yake d'ebowa,
Gyaran murya Hajiya tayi, hakan yasa duk suka d'ago suna kallonta,kallon fatuu tayi tace"muyi yar rigen cinyewa Fateema,wanda ya riga shi yayi nasara"aikam tana fad'in hakan fatuu ta fara yin loma da sauri,itama Hajiyar lomar take sai dai bata kai ta fatun ba,shi kam haisam zuba masu ido yayi cike da mamakin yadda suke tura abinci a baki,kan kace mi Fatuu ta cinye,kyalkyacewa tayi da Dariya tana fad'in ita tayi Nasara,d'an girgiza kai haisam yayi ya fara kokarin mik'ewa,kallon fatuu hajiya tayi"yi maza kisha ginger d'in,dashi wai zaku fita"da sauri ta kalli haisam don ta fahimci inda zasu,a tunaninta hajiyar bata san ina zasu ba,mikewa tayi bayan tasha ginger d'in ta bi bayan haisam da tuni ya bar wurin,

"Don Allah haisam kasa hulan ka an fi ganinka da kamala,akan kabar wannan gashin awaje kasa manyan kaya" d'aga mata kai yayi ba tare daya juyo ba,nufar kujerar da ya aje hulan shi lokacin da suka dawo masallaci yayi ya dauki hulan wadda ash colour ce itama,sawa yayi saman kan ya d'an dannata ta d'an shiga sai dae duk rabin sumar ta fito ta gefe gefe da bayan kan hakan kuma ba k'aramin kyau ya k'ara masa ba,daga haka ya nufi kopar fita daga falon fatuu dake tsaye tana jiransa ta rufa masa baya hajiya na masu adawo lpy.

Yana isa bakin parking spot ya juya yace ma fatuu ta jira,shiga yayi ciki ya nufi wata jeep ash colour sai d'aukar ido take,ba kowace mota bace fa ce Motar da ya za6ar ma Hajiya shekaranjiya har an kawota jiya da yamma yau da safe tahir d'in ya koma,budeta yayi ya shiga ya fara kokarin fiddota waje,fatuu dae sai bin motar take da kallo don sam bata ta6a ganinta ba,sai dae bata yi mamakin ganintan ba don gidan hajiya bai rabuwa da bak'in Motoci,bayan ya fito cikin harabar yasa hannu ya bud'e kopar dake gefenshi fatuu na ganin haka ta matsa gaban kopar tayi tsaye tana kallonshi,
"Sai nace ki shigo ne?" jin haka yasa da sauri ta haye ciki,bayan ta shiga tasa hannu ta jawo kopar a hankali,
"Bai rufu ba,ki bud'e ki sake rufewa da karfi",yin yadda yace tayi,sai dae har lokacin bata rufun ba,rankwafawa yayi don ya rufe da kanshi,da sauri fatuu ta kame jikinta ajikin seat ta runtse idanunta, don sai taga kaman zai had'a jikinshi da nata ne,dakatawa yayi cike da mamaki yake kallonta,a hankali ta fara bud'e idanun,lokaci guda ya fahimci dalilin da yasa tayi hakan,hannunshi ya d'aga yana nuna mata kopan idonshi a kanta yace"bai rufu bane shine zan gyara", jinjina mashi kai tayi,maimakon ya gyaran sai kawai ya juya ya fita daga cikin Motan ya zagaya side d'in da taken ya bud'e kopar ya sake rufewa sannan ya koma cikin motan daga haka ya tasheta,fuu ya tunkari gate din da tuni Officer ya zuge masu shi suka fuce.

G.R.A POLICE STATION

Slowly ya parker motar agaban Station din,hannu ya kai ya d'auki wayarsa dake aje a gefe yayi dialing number din Sp khamis,tana fara ringing yayi picking bayan yayi masa sallama ya sanar dashi yana a waje,
Ba'a dau wani lokaci ba Sp ya fito jikinshi na sanye da Uniform bai dad'e da ya zo station d'in ba,don yanzu a Police headquarter yake aiki, saboda case d'in haisam yazo,haisam na ganinshi ya bud'e motan ya fito,nufo shi yayi yana fad'in"H,zakee d big COE",hannu haisam ya mik'a masa suka gaisa fuskan kowannansu d'auke da murmushi,bayan sun gama gaisawa Sp khamis yabi motan da haisam yazo da ita da ido"H,zakee kune mota,duk wata hadaddar mota da ta amsa sunanta ku ake fara gani da ita,gaskia Motan nan ta tafi da ni Ma sha Allah",haisam dake d'an Murmushi yace"ka shiga kawae,bai da wani tsada..."wani kallo Sp ya bishi dashi"haba zakee ai koda ni makaho ne dana laluba jikin motan nan wllh zan gane mai kudi ce" kafin haisam yace wani abu Fatuu ta fito daga cikin motan ta zagayo inda suke atsaye idonta akan Sp,

"Wow,what a beautiful girl", gaidashi tayi ya amsa yace"ya sunanki?"tace"Zarah",
"Fatima zahrah,ya School kina zuwa ko?" kai ta d'aga mashi alamar eh,
Kallon haisam yayi"is she d girl?"kai haisam ya d'aga masa alamar eh,jinjina kai Sp yayi kafin yace"let's get in"jerawa suka yi da haisam,yayi ma fatuu alamar ta biyo su,bin bayansun tayi suka nufi cikin station din,Office d'in DPO ya nufa dasu,

A zaune suka iske dpo d'in bayan sun shiga yana cikin duba wasu files,nuna masu kujerun dake agaban table sp yayi alamar su zauna,hannu dpo ya mik'o ma haisam bayan ya d'ago suka gaisa,gaishe da shi Fatuu tayi,fuska a sake ya amsa mata kafin yace"Fine girl,what's ur name?"fuskarta da Murmushi tace"Zarah"jinjina kai yayi,ya maida idonsa kan Sp,bayaninsu yayi mashi nan take ya gane case d'in,hannu ya kai ya jawo wani file gabanshi,bude ciki yayi yana sake duba statement d'in haisam kafin ya dago ya bada Umarnin a kawo mashi su gaye,lekawa cikin corridor din Sp yayi yace "Sergeant" da hanzari Sergeant d'in yazo gabanshi hadi da sara mashi,umarnin kawo su gaye ya bashi daga haka ya dawo cikin Office din,

After few minutes sai ga su gaye an shigo dasu da ganinsu sunji jiki sosae,don farko da aka kamosu aka fadi masu laifin da ake tuhumarsu dashi sai suka karyata don basu san waye ya kawo kararsun ba,shi kuma Sp yasan haisam bai ta6a yi masu karya,ko ba haka ba gama shaidar raunin da haisam d'in yaji,sai da suka ci na jaki sannan sukai confessing,tun lokacin suke cikin mawuyacin hali don ba wanda yayi yunkurin zuwa belinsu jin babban laifin da sukae yunkurin aikatawa,a k'asa suka zube kan gwuiwoyinsu,

Kallon Fatuu Dpo yayi"kinsan wad'annan"kai ta daga mashi alamar eh,
"Mi sukai maki?"gyara zama tayi ta fara kora mashi bayanin yadda sukai yunkurin yi mata fyade a kango" jinjina kai dpo yayi"tun farko ya akai kika san su"shiru tayi ta d'an saci kallon haisam dake opposite da ita,alamar ta fad'i masa yayi mata da kai,nan take ta juya ta fara kora mashi bayani tun daga kan glass da ta fasa ma haisam har zuwanta kangon,ta k'arasa sai faman nishi take,

Kallon su gaye dpo yayi fuska a murtuke yace"gaskiya ne abunda ta fad'a" inda inda suka fara Sp ya kwatsa masu tsawa nan take goga ya fara magana don Gaye gaba d'aya ya firgice,tsoronshi kar ace za'a kaisu kotu don yasan daga can sai gidan yari,tsananin tashin hankali ne akan fuskarshi,

"Yalla6ai hakane,duk abunda
ta fad'a gaskiya ne,amman wllh sharrin shaidan ne bada niyya ba...."da sauri Fatuu ta katseshi"Wllh karyane,kar ka yadda yalla6ai so yake ya maida kai sakarai baka san aikin ka ba,Allah da niyya sukae kokarin yi man fyaden,shi wanccan gayen shine baiso ayi mun ba,yace a kyaleni don Allah don babban laifi ne hukuncinshi daurin rai ne,amman wannan katoton banzan gogo ne ko miye sunanshi ma yace sai yayi",ta k'arasa tana ta nishi ta kumburo baki,gyalenta gaba d'aya ma ya dawo hannunta don da tana bayanin har d'an yunkurawa take kaman zata mik'e daga kan kujeran,Sp khamis sai faman Murmushi yake don confidence din yarinyar ya burge shi,irinsu zai yi matukar wuya a cucesu suyi shiru,

A kausashe Dpo ya fara magana idonshi akan su goga"akwae wani shaidan da ya wuce ku masu lalata yaran mutane,duk irin yadda aketa fadakarwa da gargad'i amma abanza bakwa ji ko,kun lalata rayuwarku da shaye shaye hakan bai ishe ku ba sai kunbi yaran mutane kuna lalatawa,to tunda bazaku daina ba mukuma bazamu yi kasa a gwiwa ba wurin ganin an yanke ma duk wanda yake aikata irin wannan laifin hukunci,Don ubanku duk sai kunje gidan yari",a fusace ya kai maganar,gaba dayansu suka rud'e,gaye har ya fara kuka,kwalla nata zubowa daga idanunshi,magiya suka shiga yi ma dpo suna sun tuba bazasu kara ba,
Chapter 56 · 0% Book details