← Book details Yar Aikin Karuwai Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 93

Sashe 91

Yar Aikin Karuwai Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tayi sauri ta soye,kamar zasu kashe yarinya da gashi suna ta abu daya,Salma tace shi yasa nace a siyo gawayi kaga yayi amfani mun tanadi abun mu,Auta yace yaushe za a fara mata kwalliya,tun yanzu Kuma a barta ta kwana biyu tayi Kwari yace haka ne ya matsar da wutar gefe yace ko Zaki gasa local government dinne again? Salma tace ta gasu ai dazu sai dare Kuma,Abu kadan sai budewa yarinya cibi a gasa a gasa a ajiye ta,cikin kaskon wuta Kuma na kasa a ciki suka zuba gawayinsu sai da suka Nemo abinsu tun cikin Bai girma ba,Auta ya zauna a gadon yace kamar kar a Kira kowa muyi ta kallon Yar mu,Salma tace ae wlh a bari sai dare a fada musu,Suka zauna suna ta kallon yarinya ba ji ba gani. Auta yace wannan hancin nawa ne,Salma tace wlh nawa ne kana gani gashi nan daga karshe yayi tsini,yace bari dai a Kira Mami Dan darajar jaririyata suzo su tayamu murna,Auta ya Kira Mami yace Mami tace Naam,Yace albishirinki,tace goro Auta,yace to kinyi jika yarki Salma ta haihu,Mami harda guda tace Auta yaushe me aka Haifa? Yace Mace Mami tun 12pm ta haihu muna gida fa muna ta kallon Yar mu shi yasa santin Baby ya kwashe mu muka ce baza mu fada da wuri ba,Mami tace gani nan amma kuruciyarku tayi yawa Auta,ta zaci ma ba a yiwa yarinyar wanka ba,su Wise ta fadawa ta fadawa Iyamami,Ina jikin Nawwar a kwance Auta ya Kira Nawwar ya daga,yace Yaya ku taho na haihu dazu tun 12pm,Nawwar yayi dariya yace Allah kace kaji jiki me ka Haifa? Yace wata zukekiyar mace ce da gani wannan sai Dan sarki Amma dai zan hakura ta auri Abdullah muyi manage,Nawwar yayi dariya kamar me,yace to gamu nan,Auta yace kuyi sauri kar ta huce ku kalleta da duminta,Ina jinsa Ina ta dariya nace to fa Auta yayi Baby mun shiga uku Kuma yanzu,da Kansa duk ya Kira su Star ya fada musu,Ya kira su Umman mu ya fada musu,Baso ya Kira yace ta wajenka ta haihu,Baso yace akwai burar....a gidan nan sai munzo zan Kira Salma,Omaira tana ji tace Salma ce ta haihu? Baso yace ae fa ki shirya akwai suna ba yawaa,Omaira tace saura namu yace ba Yawaa zai zo inshallah, Allah yasa kar Nakuda ta miki ae yane kin gane,Auta Baffa ya sanarwa da Papa. Mami ce ta fara zuwa ta shigo har bedroom din Salma ta iske Auta a zaune a tsakiyar gadon shi da Salma da Baby dinsu sun sata a tsakiya,Mami tace yayi masu 'ya haka ake haihuwar ta ganganci baku San komai ba kuka ki fadawa mutane,Auta yace ga waya me takeyi a Nan muke browsing mu gani yanda ake yi,zo ki ganta Mami,Mami ta leka tace to a bani ita mana,yace bacci take yi ya daukota cikin kaya pink masu kyau ya mikawa Mami a cikin showel,Mami tace Masha Allah,Me jego boyon ciki Kuma ya kare yau gashi abinda ke ciki ya fito,Salma harda jawo mayafi ta rufe fuskarta,Iyamami,Sabreen,Wise sune suka zo suma ana ta yiwa Salma tsiyar boye ciki,tayi shuru ko Allah ya raya bata iya amsawa wai ita kunya,Auta ne ya mata rada yace Idan ance Allah ya raya ki amsa a zuci,tace ai Ina amsawa a hankali cikin rada ganewa ne ba a yi,Mami tace ai kunyi kokari Auta wlh da kuka iya aikin nan,yace Yar tawa na kasa gyarata Ina bazan iya ba ai zagewa nayi Mami Ina kallon kan Yar ya fito daga local government,Kai Mami kunyi kokari ku duba Yar wannan kafar yaro guda ya taho,Mami ta Kalli Auta tace wannan rashin kunya haka Auta wlh zaka bar dakin nan, Iyamami tace Dan bantan Uba marar kunya ka tashi ka fita Kaki fita yau naga jaraba,Baffa kuwa Auta ya ishe su da Kira wai ya akayi yaga shuru ne Basu zo ba,Baffa suka zo da Papa suka ga Baby suka tafi. Mami tace to yanzu dai ai dole na zauna a gidan nan tunda ba Babba ko Iyamami ta zauna,Iyamami tace rabani da fitsararre amma tunda ke da Mijinki ki je gida na zauna haka Kuma wlh yaro ya min rashin kunya ubansa zan ci,Mami tace me za a kawo Salma na ci? tace wlh yunwa nake ji dama a kawo min tuwo ,Ina Shirin zuwa nida Nawwar na gama shirya girke girke na, Auta ya sake Kirana wai me kuke yi ne a gida ni ba'a son jinina Anki kulamin Yata,Nawwar yace gamu nan fa a hanya tunda Yar har an bawa Abdullah ai munyi suruka,Auta yace kar kuce Ina Neman Kai da Yata Idan bata sonsa bazan mata auren dole ba,haka muka tafi da Abdallah Wanda har tsaiwa yana yi. Su Star dukkansu suna ciki Cele kuwa sai waya suke da Auta tayi nauyi,tace Auta Yaya Baby din? Shike nan ku Kun huta Inama nice Auta yace saura ke Kam munyi gaba mu,tace Allah sa na haifo Mace muyi takara da Kai wajen Neman auren Abdallah,Auta yayi dariya yace ai mu sai dai azo ace ana so,Muna shiga Auta ya dauki Abdallah yace Dan banza inye yaro yayi goshi tun yanzu sai farin jini yake ana ta son aurensa Allah yasa baka gaji babanka ba wajen Kaunar local government ka cuci Yata a banza,Star dariya harda bugar kafa tace Amma Auta anyi Dan Iskan yaro,Iyamami tace yaron nan ba ya jin kunyar kowa,Nawwar yayi dariya ya dauki Yar Auta ya mata Addua yace gata kuwa so cute,Auta yace mu ai ba na wasa bane kalleni Kalli uwarta,Salma ta gyara hancinta da hannu tace wallahi,Aka kwashe da dariya. Muka zauna muka kafa dabar hirar Antena,Star tace ai ni sati biyu da haihuwa Ina samun lafiya da nayi wanka Abhulkhairi ya fara buga harka,Wise tace ni kuwa ai ni na Kai kaina Kun San ni ba hakuri, Seraline tace ni kuwa har yanzu,Mandula tace an barki a kwana yarinya,Yar Zabil tace bare ni ai tuni na Mika Kai,Iyamami sai Yar ta dauka ta bar dakin,Salma kuwa sai labarin haihuwa take bamu muna Shan dariya tace ai na zaci mutuwa zanyi yau Auta yasha zagi ban San ma Ina zaginsa ba,sai dare sosai muka tafi abincin da na Kai shi Salma taci Auta ma haka da Iyamami tuwon shinkafa na mata miyar danyar kubewa sai farfesun naman kaza. Da sassafe ma lafiyayyen Kari Wise ta kawo gidan,Iyamami ta Hana Auta kwana a dakin Salma itace take Hawa bed din dole bedroom dinsa ya koma amma kullum da shi ake yini ana karbar barka yana cikin mata. Santana ma Yazo da Jamcy dinsa itama tana ja cikin ya tsufa. Ana gobe suna Auta ya dauki Salma da Baby da Iyamami ya kaisu can gidan Baffa wai kar a bata musu gida, Baso Yazo tare da Omaira da Dan cikinta Kato,Baso ya ga jaririya yayi murna siyayyar da yayi me yawan gaske ya hadowa Salma kaya da nata dana Baby,ranar Suna Baby taci Sunan Mami Salamatu wato Salma Kuma sunan matar Auta uwar yarinya,Auta yace Baby za a dinga ce mata Babyna ce,,da yamma Auta hole ya kama me kyau muka dauki wankan Anko kamar ana party na biki haka Auta da Salma suka hade a high table ana cashewa anci an sha an cashe. Bayan kwana uku da suna Ahsan Yazo yaga Babyn Auta ranar Kuma Auta ya dauke matarsa da Iyamami suka koma gidansa. Bayan sati daya da Suna Kaka da Mama suna gidan Cele da Zama ta fara nakuda,Cele ce ta fito kamar an jefota tace Kaka ka taimakeni Kaka,bazan sake Shan maganin mata ba,har Umma na sawa a lemo na bawa Auta ya sha,Cele tana ta tonawa kanta Asiri Kaka yace ni maganin nan yayi min kici gaba da bani wlh ko ya kika ce Zuwaira? Zuwaira tace wlh wannan ai abin a siya ne, sun Saba Cele tana yawan siya musu kala kala suna shoshalewarsu,Mama Basu san Nakuda take ba sai da suka ji tana ta maganganu ita kadai kamar me Aljanu,tace Sanda na hadawa Salma mugunta na sawa Salma maganin sai muguntar ta dawo kaina ranar Ahsan yayi min ciki Allah Kaka, Mama tace Kai ba lafiya ba ta Kira Ahsan yana daki ma yana bacci tace tashi Cele nakuda,bai gane da Hausa ba sai da zancen kurame Mama ta nuna masa yayi zumbur ya mike ya fito ya dauketa da gudu,Mama ta dakko kayan haihuwar,suka tafi driver ke Jan motar kaka yana gida shi Kam,Ahsan sai kuka yake ya rike Cele ,dama su akwai saurin kuka sai kuka yake yana Kiran Allah,ya Allah,yana yiwa Cele kiss a goshi Cele ta dirka masa duka a kirji Dan iska ka barni naji da kaina aikin banza kayi min ciki ka hanani sakewa ko wani zaka sake yi min yanzu to sake yi min na gani,kawai ba tausayi ba Imani kawai ka dawo kana min kiss Ina wani halin, kiss din banza,Ahsan yace kiyi hakuri ciwo ne,tace bazan hakura ba wlh bazan hakura ba Mugu kawai,wayyo zan mutu Zuwaira zuwairaaaaaaaaa....uwarku gaba daya, Ahsan dan iska.....Koda suka je asibiti ma Cele cewa take likita uwarki,Likitar burar....ashar dazagi ba Wanda basu sha ba,wata nurse tace Kai wannan da bala'i take haba Babu Wanda bata zaga ba,a lokacin Kuma Santana an kawo Jamcy ta haihu harda dafe Kai yana ihun murna ,ya Kalli Ahsan yace sorry woo ta kaina nake yi nima, ya shige ciki abinsa. Basu dade ba Cele ta haifo yarta mace kuwa,tana samun kanta tace a Kira Miracle,aka kirani na tafi asibitin duk muka Kira Yan uwa da abokan arziki sannan tace Kira min Auta ki fada masa kice tawa Abdullah zai aura jinin larabawa kalleta gaba daya Ahsan tayi wlh,Nace au ku yanzu akan Abdullah kuke takara da Auta nace Antenar yarona lafiya ku jawo min masifa ya girma da wuri wlh ku Daina wannan iskanci ke da Auta,Cele tace to shi a dangin Uba ni a dangin Uwa naga Dan Iskan da zata auri Abdallah din,na dinga dariya nace Dan Allah ki koma ta auri dan gidan Wise wlh bazan hana Yar Auta Dana ba,Muna ta dariya akan Yara kanana muke wahalar da kanmu, da wuri aka sallamomu Ahsan ya ishishire Shima ba kunya ba komai kamar Auta yarinya tana hannunsa,gashi da taurin Kai, Mama tayi
Chapter 91 · 0% Book details