Sashe 50
Yar Aikin Karuwai Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read
ato,Kaka yace kwarai kuwa,Hammad yace sabo da Allah nayi suka masa godiya. Washe Gari Ahsan shopping yayi na suturu masu tsada da kyau harda agogo Rolex ya bawa Hammad yace gashi ka kaiwa Cele a matsayin Kaine,Hammad ya tafi gidan su Cele suna ta kallonn film da Kaka,Kaka ga lemo a gabansa yana korawa yace Ina goge duniya Alqur'an bana son barin garin nan,kinji Ko ciwon Kai banyi ba har yanzu,Cele tace to komai me kyau ake ci ba cuta,Kaka yace da a Nigeria ne da yanzu na shanye paracetamol yafi carton guda,maganin ma baya aiki duk kamfanunuwan mu sun gurbata maganin basa aiki Idan cuta ta kamaka ayi ta gabza maka kwaya da Allurai basa aiki,komai namu Babu me kyau,asibiti ma abinda aka ga dama akeyi,sai ayi ta shirme ga inda ya dace a gyara baza ayi ba Kai muna Shan wahala a Nigeria kawai rayuwa muke,muma da halinmu muyi ta sabon Allah ana jika kasa da jinin bayin Allah Wanda jinin mutum Daya mumuni ya Isa ya haifar da masifa a kasa yau mutane million nawa aka kashe,a kama wasu a gana musu azaba,a kama wasu masu aure mata a auri matan wasu aure kan aure su haihu da wasu,cin Amana,yaron me gida ya kashe me gidansa,a danne hakkin marayu,zinace zinace,luwadi ga lasbiyalizim wai yan Lesbian inji Kaka alkalai zalunci kowa zalunci,masu siyar da kayan masarufi zalunci awo ma baza a baka dai dai ba,Yan kasuwa su boye kaya su tashi abinsu kullum sai an Kara kudin kaya,daga an fitar da doka kafin ta fara aiki mutanen kasar sun karawa kayan Abinci tsada, awannan zunubin da zalunci Ina zamu kaishi,Cele tace kyale su Kaka Allah zaiyi hukunci ga shugabanni sabo da suna da ikon su sa baki a gyara baza su ce komai ba su suna da kudinsu ba abinda ya dame su komai tsadar Abu zasu iya siya ba ruwansu,mutane Yan kadan sun jefa milliyoyin mutane a mafisa. Hammad ne ya shigo yayi knocking Cele ta Bude masa ta gaida shi ya amsa yace gashi ya Mika mata,tace Kuma ma dai? gaskiya kana kashe mana kudi mun gode fatan dai nan gaba Idan banji sonka ba baza aji haushina ba? yace ba damuwa tace to na gode Allah ya Kara maka so na ya links shi sai dari indai hakane ni kuwa na sha kyauta,dariya Hammad yayi yace kefa baza kice Allah ya sa Miki so na ba,tace wayyo bana mararin samunka yayi dariya ya juya yace na tafi tunda babu Kara abin,tace yo ai gaskiya na fada. Salma tana ta aikinta kullum bata hutawa,Mami ce ta shigo kitchen ta iske ta tana girki tace sannu Mami,Mami tace yawwa kawai ta shareta,kamar tayi kuka tunda Auta ya fara ciwo basa zuwa school dukkansu,jinyar Auta take fama. Washe gari da sassafe ta tashi ta tafi barruwan flowers tana sanye da Doguwar Riga yar fitted me siririn hannu dark blue me layin layin fari tana aikinta Auta yana zaune a garden din yana latsa waya yana kallonta tana rike tiyo tana fesawa flowers ruwa tana bi layi layi ta bata rai kamar zata yi kuka,ta Kalli Auta ya dago ya kalleta ta dauke kanta yaci gaba da kallonta ta sake kallonsa ta gasa masa harara,tana gamawa ta wuce gate ta budewa Baffa zai fita ta yafa Dan karamin mayafinta,tana rufewa na shugo da motata ta Bude min gate ta kalleni na kalleta nace Masha Allah gaskiya Allah yayi halitta itama,Ina fitowa ta karaso da gudu tace Aunty Ina kwana,nace lafiya Alhmdllh nayi wucewata,Salma ta tsaya tace kowa ya tsaneni ta fashe da kuka ta koma kujerar me gadi ta zauna,dakin Auta ta shiga yace ki kaini Palo,ta rikeshi tana dafa bayansa yana dogarawa da sandunansa suka fito Palo,ta karbi sandunan ta jingine gefe,Mami tana kallo tace Auta bai karya ba,Salma ta fada kitchen da gudu ta fara girki,tana jin Karar mota ta fito da gudu ta fice ta bude gate aka fita ta rufe ta dawo kitchen da gudu ta iske Auta yana kwance a cinyar Mami sai shagwaba yake,Ina wajen Wise sai daga baya na shigo bangaren Mami na samu Salma ta fito daga kitchen da tire ta jerawa Auta komai a dining tazo tace ka taso,Mami tace jeka ka karya, tace ke a baki Zaki bashi sometimes baya ci da Kansa,Salma kamar ta fashe tace to ta koma dining tayi serving nasa ta hada masa tea tace Bude bakin ko Shima sai an bude maka? yace ae,Hannu tasa a kumatun Auta ta matse masa baki ya saki Kara tace to ka bude ance,ya Bude kadan tana bashi a baki,yana ci yace nifa Idan Ina cin abinci ana shafa min gashi fa inji Auta,Salma tace nidai mutuwa zanyi kowa ya huta kawai ta saci kallon Mami taga tana kallonsa hannunta ta sa a cikin gashinsa tace ko kunyar Iyaye Babu a gabansu za ayi wannan aikin ni wlh Ina da kunya ba a nan na taso ba, Auta yace ko a Kira Baso ne? tayi shuru taci gaba da bashi a baki tana shafa masa gashi,Mami ce tace dani Rabi Idan cikin ya cika watan haihuwa ki dawo nan sabo da gudun matsala,nace ae haka yace me gidan can Shima nan zamu dawo,Mami tayi murmushi tace so kike ta rainaki ko kina tsokanarta kema.